*💔MAFARKINA💔*
*(MY DREAM )**BY*
*🤍THE DMK's🤍*
(MissDmk✍🏻)ELEGANT ONLINE WRITERS ✊🏻
Page 13
Sai ganni wannan Alhajee nayi wanda ya taba siyan kindirmo a guna a Rijana amma hankali sa gabadaya nakan system dake gabansa harna Gama arranging table bai dago ya Kalle ni ba Komawa kitchen nayi Ina sanar ma anty Godiya cewa nasan Alhajee... "
Alama tayi min da ido da inyi shuru kafin ta jani daki Aidah dagaske kin sanshi...?
Eh shine haryayi min kyautar kudi ya ma so ya dauke ni hoto alokacin amma yace sai ya sake dawowa garin mu.. "
Toh kinsa mai inda kin koma kai sauran abinci ki gaishe shi sannan ki nuna mai sanni watakila ya taimake ki.. "
Toh nagodai Sosai anty Godiya jin madam nakira Godiya yasa nima na fito... "
"Kuskus Mai kk yi ana bakin aiki, ke kiyi maza ki kwashe akai mai zai wuce ne godiya ta amsa da toh.. "
"Inata Kai kawo har aka gama packaging abinci nazo zan dauka kenan Munirat tace ita zata kai wai haka madam tace tafada tana watsa min mugun kallo ta amshe ta wuce.."
"Karki damu Aidah indai yana gari yana zuwa nan sau biyu a wata maybe ya sake dawowa..."
Toh shikenan... "
*New York City*
AMEEN AHMAD ARDO ne kwance a bed rike da wayar sa yana jin duk abinda Barrister ke gaya masa abinda suka shirya na shiga kotu..."Wani murmushi gefen baki yayi kafin yace Barrister Kai a tunanin ka zuwa na ne zai sa a Kama masu laifin..? Nigeria fa ake magana ba wata kasa ba sune rike da Nigeria suke sa ayi kuma suke sa a hana zuwana kotun bashine zai dawo da mahyfiyata ba,sun kashe ta sun kasheta yafada jiyoyi kansa na fifitowa ga kuma launi idonsa da ya canza sabida tsananin bacin rai.. "
Yes na sanni Al'ameen wanda ya mutu bazai dawo ba but shi Wanda aka daura wa laifin kisan Hajiya Fatima fa baiji ba bai gani ba duk sabida politics Shekara kusan Ashirin yana rike a gidan yari Ka duba ka gani yana da family da loved ones please Ameen yakamata kaji shawarar da Nabaka in shaa ALLAH you're safe.."
Shuru yayi for seconds without saying anything kafin yace I'd think about Barrister bye!
*KD*
Ba karamin walima akayi ba sabida har kasan waje suka so kaisa akace duk abu dayane saide a hadasa da helping machine sai Gashi dare daya ALLAH yaye masa kamar yadda adare daya suka samai sa da ciwon...Haryanzu dai baida wata walwala tunda Yar fillo ta gindiya mai sharadi cewa sai ya gaya sannan kuma ya nimo ta aduk inda take duk shi ke cin mai tuwo a kwarya..."
"Yanzu ta ina zai fara? Mai zai ce ma iyayensa..? zaice shine sanadiyar bacewar Aidah? Koko mai zaice?
Yana tare da family shi amma Sam hankalin sa baya gun.. "
Bayan angama sauke alkur'ani aka ci aka sha kowa ya watse ya rage isu isu... "Mummy, daddy ina da magana daku.. "
Shuru sukayi suna kallon sa cike da mamaki wannan maganar yake son suyi..?
Toh Muje part dinna daddy ya fada yana mikewa duk suka bi bayansa... "
Come sit here son daddy ya fada yana nuna mai kusa dashi..."
Maraice fuskarsa yayi kafin yace Mummy , Daddy Inason nayi tafiya
Cike da mamaki suke kafin sukace tafiya...?
Eh tafiya zanyi Zanje na nimo Ma'idah..!
Son a ina zaka ganta? Bayan anime ta sama koh kasa bata, amma mai ya kawo maganar batan ma'idah koh daman kasan inda take ne...?"
Mikewa Hajiya juwairiya tayi Tana mai alama da ido da yayi shuru kar yasake cewa komai.. "
Alhaji ina tunanin ciwon da yayi ne yasa shi haka amma karka damu zanyi magana dashi Sagir zo muje dakin ka ka kwanta kayi barci anjuma sai muyi magana amsawa yayi da toh ya Mike suna fita Alhajee Omar ya shiga tunani maiyasa Sagir ya kawo maganar Ma'idah Yanzu? Kohde da hadin bakinsa ta bar gidan shiyasa yake cewa zai je nimo ta yana cikin Haka wayar sa tafara ringing dubawa yayi yaga Alhajee Ahmad ke kiransa cikin girmamawa Ya amsa Kiran da Sir.Ina bukatar ka a gidana gobe by 11am akan wannan coming election din.. "
Amsawa yayi da toh Sir in shaa ALLAH zanzo da wuri kit Alhajee Ahmad ya yanke Kiran.. "
Hajiya Juwairiya ne zaune kusa da Sagir duk tabashi dukkan hankalin ta Tana sauraran abinda yake fada mata wanni dogon ajiyan zuciya ta sauke kafin tace Sagir are you for real..?
Share gutun kwallasa yayi yana kallon ta yace Gaskiyar kenan mom my life is at stake mom please help me..!
First of all I want this to be between us koh da wasa karka sake ka gayawa koh wa kohda mahyfin Ka ne sannan batun aljanar ai bata fi karfin ALLAH ba dama nasha fada Ma'idah tana da hadi dasu sabida yanayi ta da komai ya nuna tana mu'amala dasu aiga irinta nan ga inda son kanka ya jefa ka nayi ma katanga Karfe da ita amma kaqi ji har bude baki kayi kace wai ai bani na hyfeta ba koh bani na hyfeta ba ai kasan Uban ku daya ina kataba jin ayi hakan..?
Walhy mom bazan iya fadin abinda nake ji game da ita ba kowai inason ta kuma so na kauna bana yan uwantaka ba..
Baka da hankali Sagir Nace you're insane tayaya zaka dinga having wannan feelings for your own blood..? Does that sounds normal to you...?
Mom walhy that's what I feel..."
Bata Bari yakarasa ba tayi sauri cewa you better stop saying that nonsense Yanzu dole a nima kariya daga sharrin su, Yanzu nan kuwa Zanje koh nawa ne zan kashe a kanka amma midin kayi taurin Kai Ka gayawa wanni wannan batun kashin mu ya bushe Don nasan your Dad won't take it likely with us.
Mom I'm scared I don't want to die now please mom lemme go find her.. "
Karka kuskura, nace ma Ma'idah is gone and she's gone forever bazata sake dawowa ba in shaa ALLAH, so put your trust in me son you know I love you so much..!"*LAGOS*
Nice tsugune gaban madam bola Ina rokanta alfarma shiga school din yamma amma Sam tace bata yarda ba tana tsoron Karna gudu bayan tafara samu alheri Dani.. "
Kinga Aidah ban hanaki yin adininki ba sannan biyan ki nake yi Don haka ban yarda da Zuwanki school ba.."Toh nagodai madam na Mike na cigaba da aiki dake gabana, can aka kirani nakai ma oga Tunde abinci small parlor natsana Tunde yazo cin abinci sabida zaita kallon ka kamar ya hadiye ka daka duka sai ya nima cabko ka, Ganin banso zuwa madam ta dakamin tsawa da naje and make him feel comfortable da yasha kawomin karanki wai baki da manners.."
Turo da baki nayi kafin na amsa abinci koh knocking banyi ba Nafada ciki inda naga grace nagyara buttons riganta shikuma yayi saurin gyara zaman sa.."
Sannu yarinya Maicho, I ordered for two Amala with ewedu and kpomo you're giving me Jellof rice.. "
Sorry Sir..! Na kwashe abinci na mayar madam tace lafiya? Nagayamata abinda yace shuru tayi kafin tace a canza ana canzawa na kaime natarar dashi a tsaye bakin kofar zan wuce.. " sya matsa yabani gu ina kokarin arranging table naji yana wasa da hanun sa abaya na bansa sanda zuciya ta dibe ni ba na juyo rike da kwalban coke na rusa mai akai nan take ya rike goshi sa kafin ya fadi ya suma ga jini nata zuba ganin haka yasa na fito aguje na nufe inda Godiya take ina bata labarin... "
Cikin tsoro Godiya tace shikenan kinsa kanki a matsala DPO ne fa na police Yanzu inda baki gudu ba toh tabbas a cell zaki kwana za ace kin nime kashe shi..."
Cikin kuka Nace ya zanyi Yanzu? Jana tayi ciki daki ta bani kudi da address din wanni mai tsire Gashi kije gunsa ki buya
Anty Godiya ya zanyi nabar nan bayan madam ta nan nafada ina kuka...?
Kice mata zaki je Wanca chemist siyo Magani daga nan sai ki gudu.. "
Toh nagodai kamar yadda tace hakanan fada ma madam saide ban Ida fita daga shagon ba naji...
Thanks
MissDmk✍🏻
