14

45 0 0
                                    

*A DAREN AURENA*
  _SABON SALO_

Page 14

Doctor yace Abba ya na bukatar gannin Aisha, ina jin haka na shiga da sauri, hawaye na zuba daga idanuwa na, na durkusa a gabansa,ina mai nema gaffarah

My Doctor ? Abba yayi magana cikin taushin murya, kasa amsawa nayi sai embracing insa da nayi, ina kuka mai tsuma zuciya,  Abba am so sorry for the pain I caused you, please Abba forgive me..

I've already forgiven you but please come back home, yayi maganar yana kallona...

Inajin haka na tsaya cak da kuka na, ina kallon sa, haryanzu dai Abba baya son aurena da Mujaheed? Jin nayi shuru yace My Doctor?

Abba... Ban karasa magana ba aka shigo da small Abbah dake famar kuka, cike da mamaki Abba ke kallon yaron, maimakon na amsa yaron na mika wa Abba, ga takwaran ka Abba. Nayi maganar ina kallon expression insa..

He was memontarily dumbfounded and loss for words...can yace

Aisha kece da yaro? Yayi maganar cike da mamaki..

I reluctantly smile and tilts my head up, alamar Eh.

Kasa cewa kome Abba yayi sai kallon Al'ameen  dake famar kuka,
Can yace Allah mai iko, Allah ya raya mana shi, yayi maku albarka ya na fadin haka, ya mikamin yaron, amsa Abbah nayi ina lalashin sa, Ummah tace sai kije kiji dashi ai...

Mikewa nayi nabar dakin na samu wuri na zauna..

Abbah kallon Ummah yake cike da mamaki, can yace shikenan a haka kaddaran Aisha yazo? Aisha ne haka Maryam? Dan Allah ki duba yadda Aisha ta koma? Sai kace ba ita ba? Abba yayi maganar cikin damuwa da daci.

Honourable to ya zamu yi? Tunda ita ta zabar wa kanta? Dan Allah Hon ka kwantar da hankalin ka, tunda tana tunanin farinciki na tare da wannan yaron.sai mun bita da adu'a kawai..

Ai na hakura da tsamani cewa Aisha za ta dawomin kamar yadda nake zato Maryam? He smiled in grief, sai kawai gannin ta nayi da yaro?yanzu na hakura da saka burina akanta Maryam.

Gara haka Hon. Shekara kusan biyu kenan kake dauke da fushin ta, gara ka hakura kawai mu bita da adu'a, Ummah tayi magana cikin taushin murya..

8pm

Duk muna dakin da Abba yake, Addah  Aseeya na ba su labarin abinda Ya Fahad yayi. Da kuma yanayin da ya tsince ni kafin har akasamu damar ceto rayuwana dana da'na..

Ya Nura yace ai ban taba ganin mara zuciya irin Fahad ba, in banda rashin zuciya irin tasa Walhi ni ko kara waiwayar ta ba zanyi balle har na taimaka masu..

Innaro tace A'ah Nura wannan hali ba halin Krista na gari bane, karka kuma, idan kana so maganar nan taka tayi armashi ga wacce za kayi wa, tunda yarinya ta koma Dodi minal Dodi ba taji maganar manya saide na mijinta, oh oh ni naga jaraba, Innaro tayi magana tana rike da haba, to ke Shatu na tambayeki yanzu da kika  auri wannan fakirin riban nawa kika samu?

Shiru nayi kamar ba dani take yi ba.. Coz duk maganar da su keyi bai dame ni ba, tunda yanzu Abba ya yafemin.

Ke dake na keyi kike wanni mirsisi da ido kamar a murje gyada, Innaro tayi maganar tana nunani da sanda ta, can kuma tace dan Allah Nura ka dube ni ka dube ta, ko ni da nike tsohuwa nafi ta ganuwa, kalle ni shadaudau dani gwani sha'awa amma kalle ta kamar an murje taliyar hausa, Sam ba fasali..

Addah Aseeya tace ai Innaro ko miye zaki fadi ba zata saurare ki ba, zuciyar a toshe yake..

Ashiya to ai Dodi ce shiyasa ba zata fahimce yaren ba, in baki labari lokacin ina yammata da naso nima na zama Dodi minal Dodi kamar yadda kika ga wannan kanwar taki, amma Allah ya kareni ban shiga figar kazar wahala ba,tuni nabi biyayar iyaye na auri Alhaji Gidado, to ba gashi ba sai gannin albarka na keyi ko ta ina ba? Hajj da Umrah duk shekara, kaji sai naci na ture amma Walhi ko kaffara ba zanyi ba, rabon ta da nama tun tana gidan Aminu,

A DAREN AURENA(SABON SALO)Where stories live. Discover now