21

103 8 0
                                    

MissDmk

_NA BADA WANNAN PAGE A MATSAYIN BONUS PAGE SABIDA WANNAN PAGE NA DAUKE DA AINIHIN LABARIN IRIN BUTULCIN DA MUJAHEED YAYI MATA, MU HADU A COMMENT SECTION DAN JIN RA' AYOYIN KU_

'''AND THE REASON WHY I CHOSE THIS NOVEL TO BE PAID NOVEL, SABIDA BANSO ABINDA ZAI JE YA DAWO, I BELIEVE WANDA SUKE BIYA SUNSA DALILIN SU NA BIYA, ESPECIALLY MY SPECIAL ☺️'''

Cike da mamaki nake kallon yarinyar, wacce akala baza ta wuce age mate ina ba?

Dan Allah Aisha in banda na miji mai ya ganni a jikin wannan matar maza? Kyau ne ko-ko fari ne ko kuma sumar kai ne zata nuna miki? Yanzu Sadiq ke gayamin cewa saida yasa sisin gwal goma, kinsa haka Al'ada shuwah suke.

I was completely stunned into silence, yanzu har Mujaheed zai iya saka miliyan ya saya gwal ya saka ma wata? Lalle na yarda cewa yana son wannan yarinyar, dan ni tunda nake ko kyautar kudi be taba min balle kuma har akai ga bani kyautar wani abu ba.

Ya naga kinyi shiru ne Aisha? Ashiya tayi magana tana kallona kafin ta kara da cewa shifa kishi yanzu dana da akwai babbanci, besides apart from her social stand she has nothing to offer, kin fita kome ta ko ina, Aisha ki dage wajen gina kanki da ya'yan ki, karki bar kishi wacce bata isa kiyi kishi da ita ya kaiki ya baro, bara kiyi arba'in zan daura ki kan network, ba boka ba malam, iya kissa da kisisina. So ki kwantar da hankalin ki.

Murmushi mai daci da ciwo nayi, dan Ashiya bata san irin zamar da mu keyi da shiyasa take fadin haka..

An soye kayan ciki sai kanshi ke tashi amma ni ko dilis ban haba a baki ba, oh ni Indo wannan bakin rowa da yayi kama? Innaro tayi maganar a ya da ta shigo dakin.

Kai Hajjah Innaro? Duk wannan dandano da kika dinga yi a gabar murhu kice wai ba abaki ba? Ashiya tayi magana tana kallon Innaro

Sannu Ta la'asar sarakan hana ruwa gudu, yo ni naga abu? Kece maijegon ko-ko kece maigidan ? Ina magana da masu gida ki wanni sako min burmemen bakin ki kamar an saka ma yaro lemun tsami a baki? sai ki bari idan kin hayhu sai ki fada haka, to wama ya sanni ma ko bakar rowa ce ta hana ki haihuwa? Dan kar azo aci nama suna?

Ganin Innaro na nema kara min ciwon kai nace, ai ba akawo kome nan ba, duk yana wajen suya amma bara na kira Mimi ta zubo maki.

Ka ga yar arziki ba a banza ba aka baki suna na ba, To mai za'ayi da marowaci Allah na tuba? Ai shiyasa da kika ce wai balarabe ya kaini gidan Ashiya nace maki A'ah bazani ba, sabida ba kama kuma ba laba.

Hararanta Ashiya ta keyi tsabar takaici, Innaro tace kin zagi uwarki Amina, ni duk cikin ya'ya na da jikoki na banga mai bakin hali irin Amina da ya'ya ta ba, aradu sai kace nono wata Dodi minal Dodi ta sha ba nawa ba..

Innaro kije parlor yanzu zata zubo maki nayi maganar trying to divert her attention, amsawa tayi da toh kafin tace Ashiya dake da wannan likita Kudinga kyauta ko kwa samu rabo Atoh. tana fadin haka ta fice daga dakin.

Innaro rikicin tsufa kenan, nayi maganar ina dariya, Ashiya tace Walhi ba wanni rikicin tsufa duk tana sane da abinda ta keyi, muna zaune kiran Ummah ya shigo, nayi saurin picking da salama, magana ta ke min akan kara aure da mijina zeyi,  mun dade muna magana da ita wayar tana kwantar min da hankali hade da nasiha akan zaman aure.  Godiya nayi mata kafin ta yanke kiran.

Some Months Later.

Yau ake daura auren Mujaheed da Farida, tun safe Ashiya ke gidan wai tazo danna kirji,
Nayi kuka na harna godewa Allah, dan ace banyi kuka nan ba Allah zuciya ta zata iya bugawa,

Coz kwata kwata Mujaheed ba tani yake ba ta amarya da za akawo masa yake, mun koma Sabon Gida wanda kowa da part insa amma kuma muna sharing the   big living room and dining room, bamu dauko kome daga tsohon gidan ba, kome shi ya zuba acikin gida,  ko wanne part akwai parlor kuma anzuba kayan alatu aciki, ba zaka iya babbanta na amarya da nawa ba..

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 11, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

A DAREN AURENA(SABON SALO)Where stories live. Discover now