17

32 0 0
                                    

MissDmk

Jin alamun tafiya mutum, yasa nayi saurin mikewa nabar gun, kitchen na nufa daide direction da zan iya hango shi,

Bayan shigowar sa, yayi picking wayar hade da dannan wayar daga ganni dai reply yayi mata, can kuma ya nufa bedroom, ina tsaye a kitchen din banda kuka ba abinda da ni keyi, I just can't believe what my eyes saw..?

After kamar 10mins ya fito with a different dress, kiran sunana ya fara yi, tuni na wanke fuskar ta water-based na fito goye da Abbah..

Aisha yanzu nan aka kirani agun aiki akan new currency so zanyi dan dare kafin na dawo, yayi maganar ba yabo ba fallasa.

Wait JayD did you check the time? Yanzu is to 11 fa?

Are you questioning me Aisha? He sneered and paused for a while.

No, kawai naga it late ne, ban karasa magana ba yaja tsuka yace ba laifin ki bane, laifi nane da na gaya miki yana fadin haka ya fice daga gidan.. Fashewa nayi da kuka without knowing what to do, yanzu gun Feenah zaije? Inna lillahi wa ina ilaihi rajiun Allahuma arjuni fi musibati waaklufli khairan Hasbunallah wani'imal wakyl, I just can't believe that Mujaheed would ever do something like this to me?ko da yake bansa dalilin da yasa zasu hadu ba? Haka na dinga magana ni daya kamar wacce depression ke damu..

I cried my heart really out tonight, ganni yanzu almost to 1 baidawo ba yake sanni losing mind ina, tsabar kuka har wanni dishi dishi nake ganni, ina cikin kuka kiran wayar sa ya shigo, saida ya kusa katsewa nayi picking,

Am at the door. Abinda ya fadi kenan kafin ya yanke kiran

Jiki ba kwari na nufa kofar na bude hade da me Sannu da zuwa, kamar mara gaskiya haka ya shige ciki ba tare da ya amsa ba..

Girgiza kai nayi kafin na rufo kofar, nabi bayansa, inda na same sa yana cire kaya, zama nayi samar bed and loss for words, jin hannunsa a fuskarta yasa nayi saurin dawowa daga duniyar tunani na..

Have you been crying? Yayi maganar a kausashe.

When you're away I used to find this house eeriely quiet sai inga kamar mutane zasu... Ban karasa magana ba naji bakin sa cikin nawa, abinda ban taba tsamani ba, sai ma nace rabon da ya taba jikin na tun cikin Abbah na karami, bansa dagaske yake ba, saida naga gaba daya baya hayacin sa, anya ba wanni abu yasha yau ba kuwa? Dan haka muke kwana mu tashi ba tare da wanni abu ya shiga, sai gashi yau kuma daga dawowa?

Washe Gari Da safe

Abbah ya farka dani da kukar da ya keyi, zama nayi kafin na dauke sa daga kan gadon sa, na fara shayar dashi, ashe JayD har ya farka yana wanka ban sanni ba, notification na text yayi popping up a wayar sa, da yake iPhone yake using zaka iya karanta sms ba tare da ka bude ba..

"You choose to hurt my feelings for her happiness why Jeed? " abinda ke cikin sms kenan.

Wanni farinciki da anashuwa ne suka lulube ni, coz nasan JayD na so na, kuma baze taba cin amana ta ba, shiyasa hadisi yace zato zunubi ne, ko da ya kasance gaskiya, da yanzu shikenan ina ta fushi da JayD akan laifin da be aikata ba, ina cikin wannan tunanin ya fito wanka daure da white robe

Good morning JayD. Nayi gaisuwar cikin girmamawa...

Morning JayBee! How was your sleep? Hope it was splendid? coz I enjoyed it, it's one of the best night ever..!

Cike da jin kunya nace Ya! I really love it,cos I love you JayD, murmushi yayi da har ina hango hakoran sa, kafin yace zanyi tafiya for two days zuwa Lagos, so zamu fita tare zan kai ku gidan Sadiq, ki deba kayan afanin ku...

To, Allah ya kaika lafiya ya kuma kare min Kai a duk inda zaka saka kafa, amsawa yayi da Amin..

Bayan mun gama shiryawa muka nufa living room, mu ka yi breakfast kafin yayi bolting cikin kankani lokaci bolt driver ya kira da cewa yana waje, cikin sauri muka fita gidan hade da rufe kofar, key na saka a jaka, kafin muka shiga motar muka nufi hanyar Gwarimpa 1st Avenue inda Sadiq yake zaune, muna issa Ashiya ta fito cike da murnan ganni mu, gaida Mujaheed tayi kafin ta kwasa kaya na, ta nufa ciki dashi, saida yayi pecking Abbah kafin ya mikamin shi, yace sai mun dawo, Allah kiyaye hanya nayi masa kafin nabi bayan Ashiya, gidan nasu ya hadu iya haduwa, I just can't believe Ashiya da ko secondary bata kammala zata iya dacen rayuwa haka? destiny is unpredictable! Rawan jiki ta dingayi dani irin taga yar uwa..

Ƙanwata mai zaki ci? Yanzu after 9,nasan ko breakfast ba kiyi ba ga kuma shayarwa da kike yi...? Tayi magana tana ma Abbah wasa

Wai yaushe na zama kanwar ki Ashiya? A iya sanni na dai wata biyu kacal ke tskanin mu dake...

Koma wata nawa ne dai na girme ki, tayi maganar tana dariya..

Wai nikam na tambaye ki, a ina kuka hadu da Sadeeq?

Murmushi tayi kafin tace, bayan da Ummah na, ta karbo ni daga gun Abba, shine na cigaba da tallan Nono, inda muka hadu kuma naje kai ma Innaro madaran shikuma ya fito masalaci shikenan Allah ya hada mu, har ya kai ga aure, kamar yadda dai kuka hadu da Mujaheed lokaci daya..

Da rabon zan hadu da better half naje bikin ki? gashi har ina da ɗa, Allah mai iko nayi maganar ina jajjada maganar..

Ashiya tace hakan yake, bacin kaddara ba wanda ya taba kawo cewa za kiyi aure da wuri, kamar yadda Ummah ta damu akan cewa na tsufa banyi aure ba..

Dariya nayi nace shekara 18 ne tsufa? Lalle kam, dan de can rugan basa karatu ne shiyasa...

Ashiya tace nide ba wannan ba, na hada miki sandwich ko-ko pasta kike so?

Walhi nayi breakfast kafin muka fito..

To shikenan Badamuw, daman by 4pm neighbor na zamu fita dasu, yau birthday ta, zamu je cin abinci a City View kinga sai muje tare ko?

A'ah ba zanni ba, sabida ban fada ma JayD ba.. Nayi maganar irin bana so naje..

In banda abinki mai zaice? Kuma ai yasan daman dole mu fita ko dan sabida Abbah, Allah nima dai ya kawo rabo ko zan samu abokin hira, tayi maganar cikin damuwa..

In shaa Allah, Ashiya Allah ya na sanne daku zai baku haihuwa, kiyi ta adu'a nayi maganar cikin lalashi.

Murmushi tayi kafin tace in shaa Allah Aisha.

4pm

Dole ta saka na shiriya cikin black Abaya da ya kara fito da haske na, kallon na Ashiya ta tsaya yi can tace wai nikam haihuwar ne yasa kika zube haka? Kamar ba Aisha mai jikin mata ba?

Murmushi kawai nayi without saying anything,

Ashiya tace ko da yake ga me tsose ki nan, kina rama shi yana kiba tayi, maganar tana jan kumatun sa, kamar jira yake ya bare baki...

10mins
Ya kaimu Wuse, City View, da yake motar gida ne, VIP ta yi reserving, zamu shiga kenan na hango...

*Littafin nan kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya kafin ya karanta domin hakkina ne. Biya ta wannan account din: FATIMA DAHIRU  UBA 2291620442 sai ku nuna shaidar biya ta number 09074267236. Dan Allah banda vtu.*

A DAREN AURENA(SABON SALO)Where stories live. Discover now