15

34 0 0
                                    

*A DAREN AURENA*
  _SABON SALO_

Page 15

LAST FREE PAGE☺️

Cike da mamaki nake kallon sa, na kasa yarda da abinda kunne na suka jiyomin..

JayD? Yanzu.. Bai bari na karasa ba ya dakka min tsawa da yasa na hadiye tambaya ta, da cewa just do as you wish Aisha...!

Kallon Ummah dake tsaye nayi, muna hada ido ta shige dakinta, shima barin wajan yayi, kallon Mimi nayi ina kuka..

Kiyi hakuri Aunty ki...Mimi bata karasa maganar Ummah ta kira ta da ta je..

Zuciyar ta acushe take na rasa ina zan sa kaina, kaina ya kulle tsabar rashin sannin mafita, ina cikin haka waya ta tafara ringing..

Fito da wayar nayi ina kallon mai kiran, tsabar bakin ciki na amsa ina kuka..

Hello My doctor kuka kike yi? Abba yayi magana a sanyayye..

Hadiye sauran kukan nayi kafin na ce "Noi Chomri Abba am"

My Doctor why are you crying? Is everything okay? Abba yayi maganar cikin damuwa..

A'ah Abba cikina ne ke min ciwo nayi maganar ina zubar da hawaye mai zafi da cin rai...

Shine kike zaune a gida? Ki taho asibiti  ina jiran ki, Idan kuma na turo da driver ne sai na aiko miki dashi...

Shiru nayi not knowing what to say, can nace Abba Nurse dake dubani tana kan hanya zuwa, Abba ya jikin naka idan na samu sauki zanzo..

Abba ya dauki time kafin yace My  Doctor you know in this world loyalty pays alot..?

Kasa cewa kome nayi sai kuka..

And you know trust and loyalty move hand in hand? Do you feel secure and safe with Mujaheed? Creating a sense of belonging where you feel safe knowing that your confidence is protected, that's how a good marriage should be Aisha, I pray one day you'll finally get off this predicament. Yana fadin haka ya yanke kiran,

Zubewa kasa nayi ina kuka mai cin rai, zuciya ta kuna yake tsabar bakin ciki, I subconsciously stood up and headed to my room..

A zaune na same sa yana latsa wayar sa..

Durkusawa nayi a gabansa nace Dan Allah Mujaheed ban dani ba ko dan Abba ka bari naje na gansa kuma nayi masu salama tafiya...

Ko kallona beyi ba, balle kuma ya bani amsa, Mujaheed Dan Allah ka barni naje muyi bankwana da Abba sabida ni yake cikin wannan halin..

Mujaheed furiously said  Aisha don't make me to lose my mind..

Tsawar da yayi saida ya farkar da Abbah dake barci a bayana, ba shiri na mike daga durkushe da nake..
Kuka nake yi ina lalashin da'na, daga karshe fita daga dakin JayD yayi..

@ Asibiti

Kowa cike da mamaki yake kallon Abba bayan gama waya da yayi da Aisha,

Innaro tace Yo hauka ma akeyi da za ace haka yabar ta? Kai ni tunda nake bantaba gannin Dodi minal Dodi irin yarka ba Aminu? Ko wa yace ka saka mata suna Aisha ne Oho? Dan masu suna Aisha ba Dodi minal Dodi.. Oh oh ni Indodo nabi ina naga haske?

Ummah tace saide abita da adu'a dan wannan yafi karfin a zuba ido kawai..

Shiru Abba yayi ba tare da yace kome ba, amma kowa ya gansa yasan he's unhappy..

Innaro tace Uhm Uhm Kaji tsoran Allah kaji tsoran tallaka, tallaka bakin rai ne dashi, shiyasa ni duk inda tallauci yake bana raba sa, to in ma raba mana? bani zan shige su ba? Ganni Asiya na kallon ta, Innaro tace aradu Ashiya ban kaunar tallauci...
Abinda za ayi yanzu kawai Nura ya kira Hamza yake kowa? Wannan sojan dai, muje muci masa uwa, nima kaina sai na nuna masa ba a zaune muke ba, da kafar mu..

Abba yace mu wuce gida kawai, yayi maganar a sanyayye..

Cike da tausayawa Asiya ta rike hannu Abba, saura suka bi bayan su...

Some Weeks Later
Abuja, Nigeria
4pm

Na dawo gidana dake "Dutsen Alaji"
I was super exhausted and peckish, I hastily went straight to the bedroom to freshen up, 
Ina ajiye Abbah ya saka kuka, ba shiri naji da dashi, nayi masa wanka na shirya shi tsab kafin nayi wanka agurguje na fito,

Na zira jallabiya na nufa kitchen, na daura noodles tunda shi zai fi sauri, bayan dan mintina yayi na sauke na zubo a plate na fito living area na zauna ina ci...

Ina cikin cin abinci kiran JayD ya shigo, nayi sauri nayi picking kafin ya yanke, dan idan ya yanke ko na kira shi bazai picking ba...

Amsa nayi da Hello JayD?

Mai kike shirin girkikawa yau? Yayi maganar ba yabo ba fallasa...

Tuwo miyan kuka, nayi maganar ina jiran mai zace...

Kiyi Jellof Rice Sadeeq zasu zo anjima, ai akwai abubuwan girki dai ko?

Amsawa nayi da Eh. Ina fadin haka ya yanke kiran..

9pm

I really work myself out today, ga Abbah ba daman na ajiye shi kuka ya keyi.

Ina canza mai diaper ya shigo dakin, Sannu da zuwa nayi masa ya amsa kafin yace suna living room suna jiranki,

Bayan na gama shirya Abbah ya amsa she shi suka fice daga dakin.
Bayan some minutes na fito sanye da hijab..

Ganin yadda Ashiya ta mulka kiba na saki baki nayi, kafin nace Hajiya kece haka?

Dariya tayi kafin tace k'anwata ya kike ya Abbah?

Gaida Sadiq nayi kafin na koma kusa da ita na zauna, nace nikam maine ne kike ci haka da kika wannan mulka kiba..

Kiwo na ne Sadiq yayi maganar yana dariya, da ya firit da ita amma kalle ta yanzu har rokanta nake ta rage kiba..

Hmmmmm! Sauke ajiyan zuciya Mujaheed yayi.

Bara akawo abinci nayi maganar kafin na mike na nufi kitchen, arranging abinci nayi a kasar parlour, duk suka sauko aka fara cin abinci, sai santi abinci su keyi ana raha har aka gama cin abinci...

Nikam anya ba za abani Abbah yayi min kwana biyu ba kuwa? Ashiya tayi magana tana ma Abbah wasa..

Hmmmmm wannan Sarkin Kuka, inajin ko hour daya baza ayi ba zaku dawo da shi..

Dariya tayi kafin tace wai nikam tunda kika dawo Abuja Kinje gida kuwa?

Kallon JayD nayi, ya wanni hade rai, murmushi nayi kafin nace ai duk suna Gombe,  Abba ko ya shigo bai jimawa yake komawa.

Banya dan wanni lokaci suka ce zasu wuce, rakasu mu kayi har waje kafin na dawo ciki, ina shiga na tarar da wayar JayD na kara kira, bayan Kiran ya yanke message ya shigo, kamar ance na duba kawai naga notification from Feenah
"Am at Transcorp now and have booked a room waiting for Ya! "

Bansa lokacin da na zube a kasa tsabar shock da na shiga, kaina a cushe yake na ganni text din Feenah

©️MissDmk

*Littafin na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya kafin ya karanta domin hakkina ne. Biya ta wannan account din: FATIMA DAHIRU  UBA 2291620442 sai ku nuna shaidar biya ta number 07065957874 Dan Allah banda vtu.*

A DAREN AURENA(SABON SALO)Where stories live. Discover now