20

49 2 0
                                    

MissDmk

Idan naga ya rubuta "Aisha na sake sabuwar rayuwa. "

Na karanta wannan note yafi karfin sau goma, ni haryanzu I'm lost, ko mai yake nufi da sake sabuwar rayuwa? Jina shuru a toilet, Addah Aseeya tace lafiya? Tayi maganar tana knocking kofar..

Waken fuskata nayi kafin nayi alwala na fito jiki a sanyayye,

Lafiya kike Aisha? Ya naga kina tafiya kamar wata gilliu?

Ban tanka ta ba, na dauki khimar na shimfida dan yin nafillah, ficewa tayi daga dakin.

A Raka'a ta karshe, kuma a sujud na dukfafa wajen kai wa Allah kuka na, ina yi ina kuka, sabida ni kaina ina tausayin kaina idan Mujaheed ya rabu dani, dan ina son sa sosai fiye da yanda nake son kaina.
Na shafi hour daya ina kai roko na da kuka na gun Ubangiji na, dan shi kadai zai iya cire ni aciki wannan halin da na tsince kaina.

Ina sallamewa, Ummah ta shigo dakin, bayan nayi tasbh na kara daga hannun na sama ina rokan Allah, bayan na gama addua Ummah tace Allah ya amsa kuma ya biya miki bukatun na alkhair ya'ta.

Amin Ummah ta, nayi maganar kwala cike a idannuwa ta..

Aisha? Aisha yanzu so kike ki kashe kanki a dalilin wani  Aisha?

Girgiza kai na, nayi alamar A'ah.

Ummah tace Aisha ko baki fada ba, nasan akan wa kike cikin wannan damuwa, amma Aisha ki sanni cewa shi namiji kamar yaro karami yake, duk yadda kika yi training insa, a wannan hanyar zai taso, kamar misali nida Abbanku tun farkon auren mu ni ban yarda a girka yaci ba, saide ni na girka ya ci, shiyasa komin dare idan yaji yunwa yake sa nayi masa girki, sabida ban yarda da je ka saya ba, shiyasa kika ko tafiya zeyi yafi so yayi dani ko da ba dadewa zeyi ba? Na kwadaita masa cin abinci na ne don ya taso da ra'ayin kansa wajan cin abinci, kamar dai yadda in bani ba ka Yawuro ko ke baya iya cin abinci,

Sannan na koya masa barci waje daya, tunda nake ban taba raba wajen kwana da Abban ku ba, koda kuwa tafiya mu kayi waje daya muke kwana, kuma hakan ya saba da shi, wannan kana nan misalai na baki akan rayuwa da Miji.

To Aisha misali ace yanzu kome Abba yayi daide ne a wajena?ko da na san hakan laifi ne? Sannan kuma ban taba ganin laifin sa, kuma a haka na saba masa, to yanzu kina tunanin idan yayi min laifi zai san yayi min?

Girgiza kai nayi alamar A'ah.

Good Aisha, sabida na nuna masa cewa, kome yayi shine daide kuma bai taba yin laifi aguna, kuma ko da conscience insa na gaya masa cewa abinda ya keyi lefine, mindset insa ya riga da ya ginu akan cewa bai taba miki laifi, shiyasa zai yi yadda yaso kai tsaye ba tare da jin wani dar ba ko danasani yin haka, sabida haka kika koya masa, Allah ya sa wannan misalan da na baki zaki iya samo mafita kuma ki gyara rayuwan auren ki Aisha, dan yanzu ko mutuwa kika yi shi beyi asara ba, mu muka yi, kuma ko baki mutu ba zai iya kawo wata wacce zata koya masa sabon rayuwa da kuma sabon ra'ayi.

Jin Ummah tace sabon rayuwa yasa nace Sabon Rayuwa kuma Ummah?

Ehman, sabida ya samu mace mai daide da ra'ayin sa, wacce suke sharing kome nasu tare, dama a tsari na aure, mijin bawai a matsayin companion ya tsaya ba, miji yakan playing roles daban daban acikin rayuwar matarsa, kamar zame mata uba, aboki, Wa, da sauran su.

Shiru nayi ina nazarin abinda Ummah take nufi kenan, Mujaheed ya samu wacce ra'ayin su yazo daide da ita?
Dago da idona nayi na daura a fuskar Ummah nace, shin namiji zai iya auren wacce yake so amma kuma wajen ra'ayin su ya babanta?

Eh. Shiyasa da kin aure ki karance shi, wata kila shi mijin baya son mace mara ra'ayin kanta, sai kuma ya gane cewa matar da ya aura bata da ra'ayin kanta, to koda yana son Matar, kadan daga cikin kason son da yake mata zai ragu, sabida aure ba wai so ke gina aure ba, love can only lead to marriage but never tighten up the marriage.

A DAREN AURENA(SABON SALO)Where stories live. Discover now