19

38 1 0
                                    

MissDmk

Bansa lokacin da Zuciya ta dibe ni ba, nace "Mujaheed do as you wish. " ina fadin haka na yanke kiran, kafin na fashe da matsananci kuka mai cin rai,  sabida ya ga ina sonshi kulum sai yay ta min barazana da saki?

Mujaheed was memontarily dumbstruck, that's his jaw almost dropped out of shock, sake kiran wayar ta yayi coz be yarda cewa ita ta bashi wannan amsar ba, amma ya tarar da wayar a kashe, nan ne ya kara tabbatar da cewa ita ta ba shi amsa.

He rose to his feet and started wandering in the office with alot running through his mind.

Can kuma yayi undid necktie sabida zafi da yake ji duk da sanyi AC.

Zuwa Gombe ya kamani, yayi maganar kamar akwai wanni agun.

Innaro da ta shigo dakin ta same ni sai kuka na keyi.. Tace

Lahaula, ya tabbata dai wannan mutane ke jikin ki? Ashiya zo ki ganne min ikon Allah, Aseeya dake parlour Yawuro da Ummah suka karaso da sauri, jin yadda Yawuro take rafka salalami.

Innaro mai ya faru kike kwala min kira haka?

Innaro pointing masu ni tayi, hade da cewa ashe ba a banza ta koma Dodi minal Dodi ba? Ashe arnan ne a jikinta, ah ban ga ta zama bara naje na kira malaman gida kafin a farfasa min samirun da Hajiya Gudai ta lale Murtala har hudu tayimin, tana fadin haka ta rike sandar ta, ta kara gaba.

Aseeya dauki Abbah ku fita, Ummah tayi maganar tana karasowa inda nake..

Dafani tayi alamar miye yasa nake kuka? Kawai na fado jikin ta, ina kuka mai cin rai, saida nayi kukata mai isata kafin, ta dago da fuskar ta, tana kallona

Aisha duk duniya baki da wacce ta fini, idan kina cikin wani halin na damuwa I think I should be the first to know, gaya min miya saka ki kuka?

Kallon Ummah nayi, naga tausayawa da jinkai na uwa a idonta.

Ummah Allah ya bani damada ikon faranta maku kamar yadda kuke  min, tabbas ba wani da yafi min ku a duniya nan, I wish never to repeat the same mistake I did last year.

Goge min hawaye na tayi kafin tace komai ki ga ya samai Dan Adam to a rubuce yake, kuma bawa baya wuce kaddaran sa Aisha, saide wasu malamai sunce kyakkyawar adu'a da niyya kan iya canza mumunar kaddara zuwa kyakkyawar kaddara.

Ummah na, tabbas duk wanda ya rasa iyayensa, yayi babbar rashi, da ace na rasa Abbah bansa a wannan irin halin zan tsince kaina ba? Kuma ace wai ta sanadiya ta? The thought of Abba almost lost his life for me, is devastating Ummah.

Aisha abinda ya wuce ya wuce, Alhamdulillah tunda ga shi duk muna tare?  Shin kina fuskanta barazana a gidan auren ki? Ki gayamin Aisha dan ni kadai ya kamata ace na san damuwar ki?

Zanyi magana kenan Innaro suka shigo tare da baba liman da kanne Abba,
Yawwa kun ganta nan, hamsheken ke a jikinta, Kuyi ku fitar dasu Karta rusa min da gadon ta alfarma. Ga kuma samirun da Hajiya Gudai tayi min lokacin da na haifo magajin Dan ta, wato Aminu, tsabar murnan haihuwar da namiji mai kama da danta yasa ta Lale naira yana gugan naira har mutala hudu ta siye min su, to gaskiya ina ji dasu kamar yadda nake ji da wannan sandar.

Ummah tace haba Yawuro? Miye yayi zafi haka?

Maryama ba wani pikipki da ido, ko wanni zance abu ne na taimako ki bari kawai... Bata karasa magana ba na mike tana ganin haka ta rusa kururuwa tana kuka, jama'a akawo agaji kaina suka yo, aradu ni suke kallo .

Ummah mu koma part naki, ina fadin haka muka fara takowa, Innaro na ganni haka ta damke daya daga cikin yaranta,  kawu Jamilu da Innaro ta damka, yace haba Hajiya mai haka kuma?

A DAREN AURENA(SABON SALO)Where stories live. Discover now