1

242 9 0
                                    

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍

_Wannan LITTAFIN kirkirarre ne, Ta iya yiwuwa rayuwar ciki, Tazo iri daya data zahirin wani… Idan har hakan ta faru to akasi aka samu don ba labarin gaskiya bane…._

©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

    بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ
_(Da sunan Allah mai rahama mai jin kai📌)_

           _SHAFI NA: 1_

___*Kasancewar* yanayin zafi ne, lokaci ya canza... Kamar ko da yaushe sun yiyyi shimfida a tsakar gidan na su... Wasu da gidajen sauro na net wasu kuma babu sai dan maganin sauro dake ci akan kwalbar fiya-fiya.

Wani yaro ne ya kusa kai cikin gidan bako sallama yana mayar da numfarfashi ya dafe gefen bango da hannun sa daya,

"Wane marar hankalin ne wannan?" Cewar Adabiyya mahaifiyar zulfa'u.

"Gallau ne ga kunnuwan nan, ai su zuri'ar gidan su bata buya"  cewar hamdiyya

"Wai ana sallama da zulfa'u.." yaron ya sake fada

"Wai inji uban wa?" Adabiyya ta tambaye shi tana yamutsa fuska

Zulfa'u na daga gefe ta sakala yar rediyon ta agefen kunne tana jin shirin wakokin mukoma Bollywood.

Yaran ya saka kai zai fita zulfa'u ta dan daga murya tana ce da shi,

"A kasa yazo ko a mashin vespa ko a mota?"

Yaran ya daga kai yana tunani can ya grigiza kan sa yace,

"Ban lura ba ni dai nagan shi a tsaye"

"Jeka tambayo waye"

"Toh"

Yaran ya fita da sauri yana kallon saurayin yace,

"Wai waye?"

"Kache Abbas ne"

"Tohm"

Ya koma da sauri yace,

"Abbas ne"

"Dan anache... Kai wannan yaro gaba daya bashi da zuciya,  Jeka ce tayi bacci"

Yaron ya koma yace,

"Ance tayi bacci"

Abbas ya grigiza kai hadi da zaro alawa yar hudu biyar ya mikawa yaron,

"Nagode aboki na"

Yana dai tsaye ya tokare bai tafi ba. Har ga Allah so yake yaga fuskar sahibar tasa, Amman yasan dama dakyar idan zai samu ganin ta.

     Cikin haka sai ga dawowar Safaa da Marwaa daga makarantar dare.

Abbas ya dubu agogon dake cikin yar karamar wayar cocilan din dake hannun sa... Sai yanzu ma aka taso daga makarantar dare? To lallai zulfa'u ba zata futo bane kawai akace tayi bacci.

Ya janyo katuwar bahaguwar ajiyar zuciya ya sauke yana grigiza Kai... Zasu shige cikin gidan saafa tace dashi,

"Ina wuni?"

"Lafiya kalau kanwar mu... Kun dawo lafiya ya karatu?"

Marwa dake bayan ta ta tabe baki ta shige cikin gidan abun ta tana yamutsa fuska.

Saafa zata shige cikin kenan itama wani mai mota ya dallarasu da hasken fitilar motar sa

Yayi saurin fitowa daga cikin motar tasa kirar panadol extra..

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now