6

90 3 0
                                    

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍

    _SHAFI NA SHIDA_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

**** *Allah* ya azurta Malam Muhammad Alhassan da yara guda shida.

Iya Adabiyya mai dakin sa ta fari tanada yara guda hudu, zulfa'u itace ta farko sai Hamdiyya mai bi mata, Sai Salmanu da autar ta farila.

Sai matar sa ta biyu malama zuwaira, yara biyu kawai Allah ya albarkace ta da su yan biyu, Safaa da Marwaa.

Sai ta ukun wadda itace ta karshe kuma amarya.  Asma'u suna kiran ta da amarya.

   Malam muhammd Alhassan yana cikin jerin irin mazan nan masu nakasasshiyar zuciya, Yan zaman majalisar zagi da cin dunduniyar mutane tas.

Sam hakkokin iyalan sa dake kansa bayayin su. Hasalima suna zaune ne agidan tamkar ba mata da yaran cikin sa ba.

Asma'u amaryar sa ce kawai yake damawa da ita tamkar ita kadai ce mai dakin sa. Itama don tana da rufin asiri ne . Mijin ta daya rasu yana da dan hali tasamu tuminin takaba mai tsoka. Don haka malam muhammd ya like mata har dai ya aureta yake cin arzikin ta.

Ita kuma ta aure shi ne don kyawun sa. Domin malam Muhammad yanada kyawu sosai duk kuwa da shekarun sa sunja da wahala da tayi masa yawa.

Amman shidin usulin da dan yankin fulanin bazne ne fulanin usuli da ke ji da kyawu.

Shi yasa duk yaran na sa suna da nasu kyawun musamman Safaa da Marwaa yaran malama zuwaira. Kasancewar itama bafulatanar ce ba surke. Kyau ya hadu da kyawu shtsa yaran nasu Allah ya azurta su da maduakakin kyawu mai wuyar fassarwa sai dai kawai ace tubarkallah Allah yayi halitta..

Su addabiyya da malama zuwaira kansu a hade yake tumma kafin malam Muhammad ya Karo auren amaria asma'u. Domin baa dau shekaru da auro ta ba.

Idan sunyi maganar ya Kanata ya tashi ya Nemo yayi wa iyalan sa yakance ai bashi kadai Allah ya dorawa hakkin su ba suma ai iyayen su ne shi yayi iya yinsa tunda dai gidah nasa ne bana haya ba su zauna su da yaran su su ciyar da Kan su ai ba zaman haya suke ba.

Ya warewa kowacce dakinta daya sai bandaki a tsakar gida. Dayan dakin Kuma ya shafe shi ya Karo aure amaria asma'u ta tare aciki.

Wajen gidan akwai shago karami Nan Salmanu yake kwana Kasancewar da namiji tilo agidan kuma ba wajen kwana acikin gidan. Da shi da Adamu kanin malama zuwaira da yake wajenta..

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now