12

120 6 0
                                    

_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA SHA BIYU_
     _(KARSHE/FINALE)_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

*WASHE-GARI*

      Bayan Marwaa tayi sallar asubahi gari ya fara haske. Ta bi lafiyar gado ta sake nannadewa bacci mai nauyi ya dauke ta..

Sai da ta dau lokaci sosai tana ramuwar baccin da batayi a baya ba saboda hayaniyar unguwar su ma kadai ya tasheta a baya... Nan kuwa shiru kake ji sai karar kanaru da hazbiya.

Da addua ta tashi tana mai yin miqa hadi da tayar da hannuwan ta sama.. Ta rufe bakin ta da hannun ta saboda hammar data taho maata.

Ta saka hannuwanta tana shafa lallausan zanin gadon da aka shimfide shi akan katuwar katitar 8by6..

Ta runtse idanu tana tuno yar katitar su dake gidah a baya... Ta tuno su lokacin da suna cin danwake itada Safaa a wata shekara a sallar bara. Suna cewa idan suka girma sukai kudi zasu sayawa ummy gidah katoto ko'ina zasu zuba mata gadaje da katifu luntsuma luntsuma da talabijin da firji da sauran kayan da suke gani a gidajen yan gayu...

Wasu zafafan siraren hawaye suka shigaa ziraro mata... Ta sanya hannun ta tana goge su. Cikin dakushasshiyar murya mai dauke da damuwa tace,

"Allah ya jikan ki da rahama Safaa... Nayi kewar ki sosai wallahi. Allahu ya gafarta Miki ya raya Safaa Amin. Allah kuma ya bamu ikon kula da ita Amin"

Mikewa tayi ta nufi kofar da ta gani take kuma tabbatar da bandaki ne. Da addua dauke a bakin ta ta shigaa..

Sabon brush ta gani da toothpaste ta matsa ta wanke bakin ta. Ta tara ruwa tayo wanka. Bayan ta futo ta tsane jikin ta ta shafa mai da deodarant a hammata. Ta shafa turaruka ta zura kayan ta. Riga ce doguwa ta lace kalar royal blue. Batayi kwalliya ba tadai shafa man baki na lipgloss data gani an jera akan dressing mirror.

Ta na zaune akan kujerar gaban mudubi.... Cikin ta sai qugin yunwa yake. Ta wawwaiga cikin dakin babu alamar akwai abun da Zata saka acikin ta. Don haka ta mike da sauri ta bude kofar ta fita..

A gyare ko'ina yake. Tsaf tsaf da alama an sake gyara wajen ne..  Domin har kamshin tiraren wuta ne ke tashi a parllorn na khajinguru din kamfanin tiraren yerwa incense and more.,

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now