8

75 5 0
                                    

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA TAKWAS_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

      °°°°°Akwatuna ne saiti kala kala... Designers da na gidah masu dauke da kaloli gwanin ban sha'awa..

"Habibty pick your favorites..... Ki zaba mana masu kyau. Saboda zan dinga anfani da wasu idan ni kadai zanyi tafiya. Idan mu biyu me Kuma sai muyi twinning .."

Safaa tayi murmushi kawai kunya duk ta dibibiyeta. Ahsan ya dan matsa kusa da ita yana rage sautin muryar sa kasa kasa kamar rada yace,

"Babes.... Ki zaba mana... Kinji?"

Safaa ta kamo hannun Marwaa dake danna yar wayar ta mai Torchlight tache da ita,

"Twinny dauka mun kalar da kike so... Please"

Marwaa ta zare idanu cike da dinbim mamaki tace,

"Haba twinny... Ai wadanda kikeso zaki zaba. Idan kika biye tani zance duk wadannan kalolin basu mun ba"

Ahsan yayi dariya yana nunata da yatsa yace,

"Kiji tsoran Allah... Kai bari na Kira Faysal yazo ya tafi da ke ma"

"Ai ba Kai na biyo ba twin dina na rako"

"Yo daman idan ba dan itan ba kin Isa ki shiga motata?" Ya karashe fada yana dariya sosai don yasan tabbas ya shaka mata

Marwa ta mayar masa da hararar ta karasa gaban akwatunan tana dubawa bata tankawa Ahsan ba.

Safaa dai tana gefe sai dariya take musu. Marwa ta nuna wani set kalar purple tana murmushi tana mai duban tagwanta tace,

"Wannan yayi kyau"

"Yayi sosai ma shaa Allah. Habibi na dauke su?" Safaa tace da Ahsan

"Sunyi kyau kam. Amma a hadamana da wancen set din blue din yayi unisex ko?"

"Eh.. sosai ma "

"Yauwa habibty.."

Maaikatan suka daddauka sets din akwatunan biyu. Ahsan ya Isa wajen biya ya biya kudaden su. Yasa suyi delivering to gidan sister dinsa inda ake hada lefen..

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ