2

91 6 0
                                    

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA BIYU_

_ADVERT👇_

_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

   :::::::::::::::

*** *Zulfa'u* ta shige daki zuruf... Adabiyya mahaifiyar ta ta bi bayanta da sauri ita da Hamdiyya.

Malama zuwaira kamar ko da yaushe ganin hakan yasa ta dan daga murya daga cikin daki da take tana kiran yaranta

"Safaa ku shigo da tabarmar nan dare yaja dama"

"Tohm Ummy.."

"Maman Safaa ba dai har kwanciya ba?"

"Dare yayi aunty amarya shi yasa"

"Toh shikenan Allah ya tashe mu lafiya nima bari na tafi"

Wadda malama zuwaira ta kira da aunty amaria itama ta nannade yar tabarmar ta tayi cikin dakin ta.

"Rage hasken fitilar nan Safaa"

"Tohm Ummy..."

Marwa ta sake makalewa a yar katitar su zatayi bacci. Malama zuwaira ta dubi saafa dake dauke da littafan su su biyu kamar ko da yaushe zata musu aikin gidan da aka basu a makarantar boko.

Ta daga hannu ta dada mata duka a dundu marwa ta mike da sauri tana shafa wajen,

"Wayyo Allah na ummy menayi?"

"Haba marwa ke kullum ba zaki wa kanki fada ba! Ki dinga tausayin yar uwar ki Mana, kullum itace ke muku duk ayyukanda ake baku a makarantar haba marwa."

"Ummy dan Allah kiyi hakuri.. itama tana tayani a makarantar a aji. " Saafa ta fada tana murmushi

Marwa sai kunkuni take tana cuno baki gaba,

"Zaki saki bakin ki ko sai na taso na hambare ki?"

"Yi hakuri ummy"

   Adabiyya ta fito daga daki tana ta tauna kashin kaza. Hannun ta rike da fika fiki biyu na gas meat tayi dakin su Saafa,

"Salamu alaikum ko kunyi bacci ne?"

"Waalykm Salam a muna shirin yi dai"

"Gashi ba yawa kamar ko yaushe saurayin zulfa'u ne ya kawo"

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now