11

86 2 0
                                    

_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA SHA 'DAYA_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

     °°°°Haajaraan maajaaran suka furfuto daga cikin dan sahun da ya faka a kofar gidan na Malam Muhammad Alhassan.

Dawowar su kenan dagaa asibiti. An sallamo Zulfa'u da aka curo 'da babu rai...

Duk sun fita hayyacin su... Musamman zulfa'u da tayi shakarere baki daya kamar ba zulfa'un da ba matashiya mai tarin samari. Kyakkyawa sarkin ado. Yanzun kuwa rayuwa ta sauya. Samarin duk sun gudu da jin tayi cikin shege. Don haka ba dan kayan dadin da kudaden da samarin kan bata a baya. Tuni ta koma ta jeme gwanin ban tausayi.

Suka shiga cikin gidan bakunan su dauke da sallama. Yan tsakar gidah suka amsa musu.

"Kun dawo? Sannu zulfa'u"

"Yauwa sannun mu"

Daki zulfa'u ta shige ta zube akan shamilalliyar katitar tah.  Sai haki take yi. Sanye take cikin wata kodaddiyar rigar shadda koriya tun ta sallar baara. Ta yage hijabin jikin ta shima . Hadi da daukar mahuci ta fara fiffita tana mai sauke numfarfashin ciwo...

Kawujo... Yaya ga malam Muhammad  kuma kawu ga su zulfa'u da su Marwaa ne yayi sallama tun daga kofar gidah kamar ko da yaushe yana mai neman abashi iso ya shigo

Duk suka kikkintsa kansu. Yayi sallama ya shigaa ciki.. Bakinsa na motsin taunar namijin goron da yake ci.

Daya bayan daya suka shigaa gayshe da shi. Zulfa'u ma ta leko ta kofar dakin su tana gayda shi . Duk ya amsa musu cikin sakin fuska...

"Yauwa ina neman ki..."

"Ni kawu?"

"Eh ke dai zulfa'u... Sai kuma ina Marwaa yanzu na ganta anan."

"Tana gayshe ka ta shigaa bandaki."

"Toh Alhamdulillahi an daura mata aure yau. Allah ya basu zaman lafiya da kaunar juna. Da yalwar arziki. Ya kuma raya wannan jinjinniya ya jikan mahaifiyar ta. Allah ya bamu ikon kula da ita dukkanin mu."

Dai dai da fitowar Marwaa daga bandaki. Ta saki butar a kasa ji kake fasssssss.

"Kawu an dauramun aure kuma?"Ta tambaya shi cikin tsananin mamaki. Domin zuwan Faysal na karshe da yazo zance bai yi mata maganar daurin auren su nan kusa ne ba.

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now