5

75 3 0
                                    

   *_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
         

    _SHAFI NA BIYAR_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

   Adamu ya riga su fita, Sannan su kuma suka zura hijaban su iri daya suka bi bayan sa...

Ahsan na dora idanun sa akan su gaban sa ya tsananta bugawa... Duba da yadda tsananin kamar tasu tayi yawa...

Adamu ya yafuto su da hannu suka karasa inda suke a tsaye. Marwaa ji take kamar ta saka hannu ta mangare kan Saafa . Da Saafa ta fadi gaskiyar itace wadda Ahsan yake nufi da tuni ba ita zaa fito.

"Acikin ku wacece ta shiga gidah a karshe?" Cewar kawu Adamu.

Marwa ta daga hannu zata nuna Saafa itama ta daga sukayiwa junan su nuni a atare.

Kawu Adamu ya girgzia kai cike da takaici yace,

"Banason wannan wasan na ku... "

"Marwa cee" Saafa ta fada tana murmushi

Marwaa ta daga kai ta sauke mata lafiyayyiyar harara. Ta hada da Ahsan daya ke binsu da wani kallo duka shima ta galla mai harara tace,

"Wallahi Safaa ce kawu. Ni ce na shiga a farko... Idan karya nake ta rantse yadda na rantse"

Ahsan ya sauke nannauyar ajiyar zuciyar dake tattare da farin cikin da ya mamayeshi. Daman tun daga hararar da Marwaa ta daka masa ya gano ba itace mutuniyar da zuciyar sa ta kamu da kaunar ta ta ba.

"Safaa wai haka? Kinsan dai bakyau rantsuwa akan karya ko?"

Safaa badan ta so ba ta daga kai ta murgudawa marwa baki kasa kasa tace,

"Eh.. Ni ce na shiga a karshe"

"Alhamdulillah....." Ahsan ya furta a fili. Murmushin fuskar sa na dada faadaduwa.

"Kawu na tafi ?" Cewar Marwaa.

"Toh wannan itace Marwaa tagwan Safaa." Cewar kawu adamu yana mai yiwa Ahsan nuni da su.

"Mashaa Allahu... Safaa da Marwaa Allah ya raya su Amin"

Marwa ta juya ta shige ciki. Yayi nda kawu adamu ya basu waje. Ahsan ya dan sake matsawa wajen Safaa taja baya tana lankwasa yatsunta yayi murmushi sannan yace

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now