7

62 4 0
                                    

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍

    _SHAFI NA BAKWAI_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

   *Hijabi* ne dogo har kasa ajikin ta mai hannu ta kuma saka takunkumi baki (face mask) a bakin layin su ya tsaya da mota, tayi saurin shigewa ciki ya tashi motar suka bar unguwar....

Akan hanyar ta tafiya ne ya juya ta dube shi sai murmushi yake yi.. Jin kamar tana kallon sa ne ya sashi juyawa idanun su sukaa hadu.

Ya mika hannun sa daya ya riko hannun ta. Yayinda dayan hannun yake tuqi dashi..

"Yammata na....." Yace da ita yana murmushi.

"Uhum"

"Menene ? Uhmmm? Meya faru?" Ya tambayeta cikin muryar roko yana mai rage gudun da yake akan titi

"Ba komai..."

"Ki kwantar da hankalin ki zulfa babe .."

"Rayyan kasan na gaya maka duk yan uwa sai magana suke anata gulma akan rashin aure na. Ga su Safaa fa dik an kusa bikin su... Kuma ni wannan maganar daka kawo gaskia tsoro nake rayyan.... "

"Shhhhh haba zulfa'u. Wai meyasa har yanzu kin ki ki yadda ki amince da ni ne? Shekarun mu nawa tare na taba neman ki ne banda yanzu? Na gaya miki matar nan kwarata take bama ta gidah na yanzu . A matse nake ne. Auren kuma babu bashi ki rubuta ki ajiye. Zulfa'u idan ban aure ki ba ai mutuwa zanyi."

Kalaman sa yasa tayi murmushi. Rayyan ya dube ta tana murmushin shima yayi yana lakuce mata kumatu yace,

"Yauwa yammata na... Kar ki wani damu. "

"To shikenan.."

Wani hotel suka nufa already dama ya rigada yayi komai mukullin kawai aka basu sika hau saman wani daki kawatacce.

"Ki cire hijabin ki sha iska..."

"Zan cire..." Ta fada tana zare din facemask dake fuskar ta

Rayyan ya zaro bandir din yan dubu daya guda daya ya dora akan cinyar ta,

"Ki fara da wannan"

Zulfa'u ta rike bandir din kudin tana murmushi.. ta zuge yar jakarta ta zura su aciki.

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now