9

62 5 0
                                    

_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA TARA_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

****Ji da ganin Marwaa ne ya dauke gaba daya... Yayinda kunnuwan ta ke futar mata da sautin wata kara quuuu..

Ta yanke jiki ta fadi awajen. Kawu Adamu da malama zuwaira sukayi kanta.

Ahsan kamar wani matashin zaki haka yayi kukan kura ya cakumi wuyan likitan ya takwaikwaye masa wuyan rigar tamkaar zai yage masa fatar jikin sa.

"Karya kake yi.. Safaa na nan da ranta makaryacin banza da wofi. Safaa bata mutu ba. Safaa ba zata mutu ba. Mun gama shirya yadda zamuyi rayuwar mu da 'yar mu.. Makaryacin banza futo mun da ita..

Malama zuwaira dake tallafe da Marwaa a hannu ta dubi adamu kaninta dake katse hawaye tace dashi,

"Adamu yi masa magana kache yayi hakuri. Ya karbi KADDARA. " Bata yi kuka ba saboda batasan ta zubar nata da hawaye. Sai dai idanun ta sun kada sunyi jazir. Wata jijiya katuwa ta futo mata tundaga tsakiyar kanta zuwa saman fuskar ta.

Aka dauki Marwaa aka dora akan wani gado sukayi cikin emergency unit da ita.

"Cika shi Ahsan... Safaa yanzu addu'oin mu take bukata ba zubar hawayen mu ba. kayi hakuri Ahsan.. mahaifiyar ta gata nan catai a baka hakuri. " Kawu Adamu ya fada yana kokarin raba tukwikwiyewar da Ahsan yayiwa wuyan likitan.

"Kai ma ka amince Safaa ta mutu? Yanzu kun yarda Safaa ta mutu? Yanzu yanzu fa kai innnalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Ya karasa fada yana zare hannuwan sa daga wuyan likitan

Likitan ya sauke ajiyar zuciya yana girgiza kansa domin sun bashi tausayi matuka musamman Ahsan ma kasancewar miji ne agareta kuma sabon aure ana dokin ganin abunda aka haifa tare da kwadayin kasancewar rayuwa atare zuri'a daya.. Gashi shine dai likitan dake ganin su tun farkon gwajin shigar cikin ya zuwa daukar cikin na watanni har ila yau da Allah ya sauketa lafiya ya kuma dauke abarsa

"Kuyi hakuri.., Allah daya fi mu kaunar ta ya karbi abar sa. Allah ya sa ta cika da Imani Kuma Allah yasa aljanna makoma ce agareta.. " Yana gama fada ya bar wajen da sauri.

Malama zuwaira ta goye jarirya Safaa a bayanta tana ta zagaye da ita. Kukan zuci takeyi. Domin duk dakiyar da take da ita. Kafafuwanta gaza daukar nauyinta sukayi sai kujera ta samu agefen su Ahsan ta zauna.

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now