4

75 4 0
                                    

*_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
        

    _SHAFI NA HUDU_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

*Ya fito* yana ta sauri ya cinma su yana doka sallama....

Aisha ta daga kai ta dube shi alokacin da ya karasa kusa da su din. Don ita azaton ta ma ko dan sahun lefi ya masa yadda ya tuko motar gadan gadan ya tunkare su ya faka motar..

"Idan kun amince zaku biya hakan yadda na fada ku hau muje idan baku yarda ba gaskia ba zanje a dari hudu ba Allah ya sa ni"

"Haba yayana Allah a haka muke zuwa ko ina fa ana ragi" Marwa ta ce da dan sahun cikin muryar roko..

"Gaskia idan ba zaku biya hakan ba sai dai ku nemi wani"

"Aboki na jeka kawai, Zan karasar da su... Assalamu alaikum sannun ku." Cewar saurayin daya fito daga mota

Duk suka tsaya suna binsa da kallo... Musamman Marwaa dake binsa da kallon ka renawa kanka hankali, Ta kasa hakuri tace,

"Akan wane dalilin zaka karasar damu gidah? Munsan ka ne? Bawan Allah mu ba irin yammatan nan bane masu shiga motar maza suna rage musu hanya. Da mu hau motar ka gwara mun karasa gidah a kafa wallahi. Ku shiga muje dan Allah."

Ta chusa Saafa aciki, Ta sake janyo hannun Aisha ta shiga, daga karshe ita kuma bayan ta tsaya ta watsawa saurayin dankareriyar lafiyayyiyar harara ta shiga ciki mai adaidaita sahun yaja suka tafi...

"Gaskia wanan gayen anyi dan renin hankali, Ni fa at first na dauka mai adaidaita ne ya masa ba daidai ba yasin.." cewar Aisha

"Nima dai yaban mamaki audacity din nasa yayi yawa" saafa ta fada..

"Bar dan renin hankali ... Irin samarin nanne masu rawar kai. Irin shi ga mai kudi dinnan cikin izza yana magana, ya dauka muma irin matannan ne ballagazazzu marasa kaman kai, Bamu sanshi ba haka kawai sai mu shiga motar sa. Mtscew dan renin hankali kawai" Marwaa tafada cikin hasalewa... Ta karasashe zancen da jan tsaki...

Mai adaidaita sahun ya na jan babur yana jinsu ya kyalkyale da dariya yace,

"Nafu tunanin wata yake so acikin ku gaskia"

"Allah ya kiyashe mu ya kuma tsare mu da kula irin wancen..."

Dan adaidaita ya juya ya kallo marwa data gama magana taja tsaki yace,

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now