3

81 6 0
                                    

       *_KADDARA!!!💔_*
     _KOWA DA IRIN TASA_
              👭👩‍❤️‍👨💍


©️®️ _NANA HAFSATU_
          _(MSS XOXO)_

    _SHAFI NA HUDU_

_Arewabooks:mssxoxo_
_Wattpad:missxoxo00_

_ADVERT👇_
_YERWA INCENSE AND MORE : (MASARAUTAR KAYAYYAKIN KAMSHI)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

___________

  *Ranar* laraba Saafa da Marwaa suka zana jarabawar zangon karatun su na karshe na matakin babbar sakandire.. paper chemistry da ita suka karashe. Fuskokin daliban baki daya kumshe suke da farin ciki marar misaltuwa na yau suma burikan su sun cika sunyi candy..

Sukai ta ife ife bayan sun gama zana jarabawar. cike da maduakakin farin ciki kuma suka shiga musayar sunayen su suna rubutawa da marker ajikin hijaban su.. wato signout..

Su dai malaman sai bin su kawai sike da kallo, suna masu taya su murna.

Headmaster ta tsawatar musu ganin sun dauki tiyo suna jika jikin su da ruwa . Ta dauki lasifika ta shedawa kowannen su ya saurara...

Ta shiga yi musu nasihar ban kwana mai ratsa jiki da yadda kowannen su zai cigaba da rayuwa bayan makaranta. Kowanne ya karbi rayuwar da Allah ya dora masà ita ya yita cikin lumana bisa tafarkin tsira.

Bayan ta gama jawabi, daya bayan daya malaman kowanne ya shiga tofa albarkacin bakin sa. An kuma yaba sosai kan kwazo da hadin kai da yan ajin suke da shi.

Daga karshe aka kira headgirl tazo tayi bayanin sallama ta kuma bawa dalibai yan uwanta shawara.

Malama Batula, malamar physics dinsu itace ta sake Kiran sunan Saafa a Karo na biyu Kan tazo tayi jawabin bankwana a matsayin ta na headgirl din makarantar Kuma ta ajin karshe da suka kammala.

"Ina headgirl dinne? Saafa Muhammad  Alhassan.... "

"Malama! Ga Ni"

"Yauwa karaso ki karba"

Saafa ta sauke zuciya. Gabanta na tsananta bugawa. Marwaa ta daga mata Kai da mata jinjina da hannu alaman karfafa mata gwiwar zata iya..

Saafa ta karasa kan tudun da malaman sike a tsattsaye yayinda daliban ke tsaye daga kasa suna kallon su. Ta karbi lasufikar tana gyaran murya tace,

"Assalamu alaikum wa rahamatu Allah... Ya Yan uwana"

Suka amsa sallamar tata da karfi. Ta cigaba da cewa,

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now