Chapter - 2

186 25 0
                                    

Daga bakin zaure na tsaya ina leka ciki sai na hango Hana tana daka a turmi Mama kuma tana zaune gaban murhu tana aikin hura wuta. Yaya Nabil kuma yana daga gafe yana wanke wandonsa da talkami.

“Ina kika je?”

Na kalli Yaya sai na jingina da kofar bana son amsa masa tambayar domin na san fada zai min ni kuma ban iya karya ba komai za ayi min sai na fadi gaskiya.

“Ba magana nake miki ba”

Ya daka min tsawa, na dan matsa baya na saka hannu a baki ina cin akaifata.

“Yaya Mama fa ta cinye abincin da ka kawo kuma tace zata min duka shi ne na bar gidan na tafi gidansu Zee mamanta ta ba ni abinci bayan na ci ta zuba min wani a kula na kaiwa Zafeer”

Yaya ya girgiza kai yana murmushi.

“Yanzu ke gidan ku ana kokuwar yadda za a cefane a girka masara amman kin samu abinci sai ki kaiwa saurayinki? Noor Allah ya shirya ki”

Mama ta tabe baki

“Ai wannan yarinyar abu ne mai wahala ta yi jinkaina, duk abun da ta samu a duniyar nan sai dai ta kai ma saurayi babu ruwanta da ni”

“Toh ni Mama me nake samu? Kullum fa babu ne a gidan, kuma ai kece kika ce dukana zaki yi shiyasa na kai masa”

“Kya ji da shi dai, wuce ki daki kasan gadona ki dauki kudin adashe ki kai ma Assabe ki ce ga zubi na biyar nan”

“Mama yanzu kina da kudin adashe kika hana ni na babur din da zan tafi bikinsu Salwa?”

“Kudin adashen zan baki ki tafi biki? Wa nake ma dashen ba ku ba? Kudin kayan aure nake tara muku ai”

Ina jin haka na san Mama ta sauko kenan dan haka na wuce cikin gidan na shiga dakinta na dauko kudin a gurin da ta saba ajewa na fito ina kallon Yaya Nabil da zai zubar da ruwan kumfa.

“Yaya na kawo kala ɗaya ka wanke min dan Allah?”

Wata uwar harara ya watso min sai na yi saurin barin jikin kofar dakin na nufi hanyar waje.

“Kawo kala daya amman”

Ban yi mamakin jin haka daga gareshi ba, daman Yaya Nabil mutum ne mai sauki kai a gareni. Na juyo cike da kuzari da jindadi na nufi dakinmu na dauko tufafina na sallah babba da mayafin sai kuma na tuna ba lallai ne Hana ta yarda ta min kwaliya ba dan haka na dauko abayata na mika masa ta.

“Gashi Yayana na gode”

Na mika masa cike da ladabi.

“Kuma na fada miki ki daina zuwa gurin aikin Zafeer ko? Ba yau na sha miki magana amman baki ji”

“Abinci kawai na kai mishi idan ba yace na kai mishi abinci ba ko kuma na zo na karbi abu Wallahi bana zuwa, Yaya ni ma fa ina da hankalina”

Be sake ce min komai ba ya jefa abayar a ruwa ya fara wankewa ni kuma na nufi kofar fita ina yi ma Hana gwalo. Domin na san idan ita ce ba zata wanke min ba ko da kuwa zan yi hauka.

“Dan Allah can mai kayan aro”

“Na ji dai na ji dai ba zan cire ba”

Na fice abuna ina tafiya a natse, daman can bana kama da marasa tarbiya ko natsuwa zakewar da nake abu ma idan na san mutum ne ne nake yi, idan ban sake jiki a guri ba ko uffan bana cewa. Cikin natsuwa na isa gidansu Talatu mai adashe na bata kudin kuma na fada mata zubi na shida ne kamar yadda Mama tace ma fada, sannan na juyo na fito, a kokarina na takaitawa kaina wahala na biyo ta kwararo kwararo domin ya fi sauki sama da mike hanya sambal.

Wani abun da ban saka rai da tsammani ba ashe rabon ganin wani abun ne ya biyo da ni ta hanyar, Abbah na gani tsaye kofar gidansu Gambo mai furar yan gayu rike da yar ledarsa baka sai gyaran riga yake. Ban yo mamaki ba domin akwai zaurawa a gidan har biyu da kuma yan matan da ba a taba yi ma aure ba. Rage tafiya na yi saboda na samu damar ganin wadda Abbanmu yake so cikin ƴaƴan gidan, amman hakata bata cin ma ruwa ba, domin har na kawo kusa da Abbah yarinyar bata fito ba.

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now