Chapter -5

111 16 0
                                    

KAREEM POV.

After ya mika masa tsarabar Noor ya bude motar ya shiga sai Nabil ya rage tsawonsa yana bashi hakuri.

“Ranka ya dade dan Allah ka yi hakuri, Wallahi ba zan sake bijirewa umarninka ba, kuma idan wani abun marar dadi Noor ta yi maka da ya saka ya kanye wannan hukuncin dan Allah ka yi hakuri”

Kareem ya kirga 10k ya mike masa.

“Noor bata min komai ba, kuma a yanzu ina jin hakan da na yi yayi daidai domin be kamata na baka umarni ka saba ba, ba wai na koreka ba ne noo zaka zauna ne a gida har Monday”

“Toh ranka ya dade”

Har Kareem yaja gambo zai rufe motar sai kuma ya kalli Nabil

“Shekarar kanwarka nawa?”

“Wannan watan zata yi 15”

‘Fresh one, shiyasa kanta be tsaya ba, tashen balaga take’

Ya fada a ransa a zahiri kuma sai ya sake tambayar Nabil.

“Kai kuma fa?”

“19 ranka ya dade”

“Okay, amman tana karatu?”

“Bata karatu gaskiya, bata son makaranta”

“Why?”

“Haka nan kawai bata son karatun, kanwarta da kusan suke tawaye tana karatu sosai amman ita bata son makaranta”

“Kuma aka zuba mata ido? Baku tsoron future dinta ya lalace?”

“Toh ya za'ayi ranka ya dade ai ka ga yadda take, Baba ne kawai zai iya da ita shi kuma karatun ba damuwarsa yayi ba”

“Allah ya kyauta”

“Ameen mun gode”

Ya rufe motar ya juya, ya fice daga unguwar. Ba gida ya nufa kai tsaye ba restaurant dinsa ya sake komawa a gurin yayi sallah La'asar yana fitowa Masallacin abokinsa Hafiz na fakawa kusa da motarsa, Kareem ya karasa gurinsa ya mika masa hannu suka gaisa.

“Dazun na ga motarka, na so mu yi magana amman ban san fitarka ba”

Kareem yayi murmushi tunawa da Noor.

“Wata bakuwa na yi mai kiriniya ita ta saka ni zuwa nan kuma na kaita gida”

“Bakuwa?”

Hafiz ya tambaya domin be taba jin abokinsa yayi zancen wata mace ba bayan Safeena da matarsa, ko siblings dinsa iyakarsa da su gaisuwa, sai kuma fada idan sun yi ba daidai ba.

“Yeah wani yaro na ne, da yake aiki nan ya zo duba ni sai ya zo da kanwarsa to kanwarsa ce rikitacciya”

Yana maganar yana murmushi maganarsa da ita yake tunawa a lokacin da take fada masa abincin restaurant dinsa yayi tsada.

“Kuma ka kawo ta nan ka kaita gida? Ko dai...”

Kareem yayi hanzarin katse shi yana girgiza kai

“Noo kai yarinya ce irin fresh yaran nan yanzu take girma, kuma ni bayan Safeena babu kowa a raina”

Hafiz yaja tsaki jin ya ambaci sunan matar da ya fi tsana a duniya fiye da kowa, matar da ta sauya dabi'u da mu'amalar amininsa zuwa wani dabam da ba shi ba.

“Ya jikinka?”

“Alhamdullahi na ji sauki sosai”

“Amman baka shiga aiki ba yau, domin na shiga ban same ka ba, na tambaya aka ce baka shigo ba”

“Na shiga da yamman nan na kai Noor na mata treatment”

“Wace Noor me ya faru?”

“Yarinyar da nake baka labari yanzu ita ce Noor, Yusura ce ta buga mata abu akai kan ya fashe jini ya zuba shi ne a kaita asibiti”

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now