chapter 9

160 18 2
                                    

KAREEM POV.

8:19am ya nade sallayar da yayi sallah ya aje, sannan ya dauki wayarsa dake ringing ya duba. Ganin number mahaifiyarsa ya saka shi farinciki.

“Hello Momy”

“Ashe zaka dauka, ai na dauka idan an kira ka ma ba zaka dauka ba”

“Haba Hajiya me ya kawo wannan maganar kuma?”

“Yaushe rabon da ka kira ni?”

Ya sauke ajiyar zuciya ya zauna gefen gadonsa.

“Na kira sai Baba Karami ya dauka ya ce min kina bachi kuma likitocin sun ce a barki ki huta na kwana biyu kar a takura miki, ana son ki samu bachi”

“Wannan ba hujja bace, hakan ai be hana matarka kirana safe da rana da dare ba, kullum sai ta kira ni sau uku ko da ban amsa wayar ba zata ce idan na farka a sanar min ta kira waya, haka ma mahaifinku kullum sai ya kira ta gaishe shi”

Yayi shiru for few seconds sannan ya ce.

“Yi hakuri Momy, Wallahi saboda likita yace a barki ki huta ne yasa ban takura da kira ba, Daddy kuma ina son na shiga this Saturday na gaishe shi”

“To ya dai kamata dai, ina yaran?”

“Suna lafiya Momy, ya karfin jiki”

“Alhamdullahi ina samun sauki, yanzu dai suna gasa min kafafuwan ne, sun ce jinin ya sauka”

“Maa Shaa Allah haka nake son ji, Allah kara sauki ya dawo mana dake lafiya”

“Ameen, Allah ya muku albarka kai da yaranka, Yusura ma Allah ya mata albarka mace ce mai mutumci samun mace irinta akwai wahala yanzu, yarinya ce mai kirki da biyayya duk da kasancewar ta yar'uwa ta kara karfafa zumuncin, bata taba nuna min cewar ba ni na haifeta ba, shiyasa ko da yaushe nake jan kunnenka akan riketa amana, duk da na san kai ma yaro ne mai biyayya da kulawa, Allah dai ya muku albarka”

Sai da Kareem ya hade wani abu da ya tsaya masa a wuya sannan ya amsa da Ameen yayi mata sallama ya sauke wayar. Sannan ya mike tsaye ya aje wayar ya nufi kofar dakin ya bude ya fita, sai da ya fara leka dakin Tine ya duba bata cikin sannan ya rufe kofar ya sauko kasa.

“Ina kwana?q”

Ya gaishe da Yusura dake jera kuloli a dinning. A madadin ta amsa sai ta tambaye shi domin shi da ita ba al'adarsu ba ce gaisawa da juna da safe, kara ma shi ya kan fada mata wani sa'in idan zai fita, ko kuma gaisheta musamman idan yaransa suna nan.

“Wani abu kake bukata ne”

Ya kalli tv domin shi ma ba son kallonta yake ba, yana daga cikin dalilin da ya saka duk yadda yake son tsara gidansa ko tsara zama fa matarsa wannan rashin son, da kuma rashin ba shi hadin kai sai ya wargaza tsarinsa. Ya dauke ba tare da ya kalleta ba ya ce.

“Momy ta fada min kina kiranta kullum ki ji ya jikinta”

“Ba saboda kai nake yi ba, bana bukatar godiyarka, ina yi ne saboda kulawa da ita da girmamata wani abu ne da na saba da shi tun kamin na aureta, aurenka ba shi da tasiri a gurina baka da kimar da zan maka alfarma”

Ya zuba hannayensa a jallabiyarsa ya daga kai ya kalli yadda Allah ya wadata da mazaunai da shape kamar wadda ta yi surgery.

“Me yasa tun farko baki fada mata baki son danta ba, wannan soyayyar karya kike nuna mata”

Ya juyo ta kalleshi.

“Danta ya kasa fuskarta ya fada mata be son matar da ta zaba masa sai ni? Dukan abun da na ke yi ma Momy ina yi saboda Allah kuma saboda ita din uwace a gareni, ta rike ni a lokacin da uwata ta tafi ta bar ni, ta rike ni a lokacin da yan'uwan mahaifina suna wofintar da ni, ta rike ni a lokacin da ban san komai ba, tun bana iya cin komai sai madara har na mallaki hankalin kaina, a hannunta na yi ilmi a hannunta na girma ita nake kallo a matsayin uwa, da Momy zata ce Yusura dauki wuka ki dabawa kanki Wallahi zan daba. Na fada maka duk wannan ne saboda ka san ba saboda kai nake yi ba”

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now