Chapter -6

159 25 4
                                    

Duka sosai Mama tayi min tun tana dukana tana zagina har ta kai tana dukana tana kuka kamar yadda nake kuka. Hana ma kuka take saboda ta ga ina kuka daman haka take duk fitinarmu da ita idan wani abu ya bata min rai ko ya saka ni kuka ita tana shiga damuwa sosai, wani lokacin har ta kan fi ni ma saboda Mama tana cewa ni ban san ciwon kaina ba, sai dai wani ya sanin min. Na rarrafa na tashi zaune ina jin tsiyayar ruwan da na tabbatar na jini ne a kaina.

“Mama yanzu me ye amfanin haka? Gashi yanzu kin ji mata rauni a raunin da ta ji, yanzu kuma a koma jinya ana neman na magani Baba kuma ba badawa zai yi ba kin san tun da kudin nan suka kai hannunsa ba zai bada su ba, kuma halin nan ba dainawa zata yi miye amfanin dukan?”

Bana ganin fuskar kowa saboda kuka, sai dai zan iya shaidar muryar Yaya Nabil ne mai maganar cikin yanayin damuwa.

“Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un”

Shi ne abun da nake ta jin Mama na maimaita cikin kuka, na dai na samu na isa bakin kofar dakinmu da rarrafe, na shige ciki na kwanta. Daga lokacin da na kwanta sai kukan ya tsaya min daman can Allah be yi da son kuka ba, ba komai ke saka ni kuka na dade ba, sai dai na bar abu a cikin zuciyata idan na tuna ya kuna min rai, shi ma kuma da zarar na samu wani abu da zai dauke min hankali a take zan manta sai idan an bude sabon shafi kuma.

“Jinin ya tsaya?”

Na ji muryar Yaya Nabil sai na tashi zaune na kai hannu na taba gurin har lokacin zafi yake min sosai, kuma jinin yana zuba sai dai ba kamar dazun ba.

“Rashin jin magana ke ja miki shiga matsala Noor, ke babu ranar da zaki yi hankali? Kuma kin san idan kika aikata wani abu laifin a gurin Mama yake komawa, fitar nan da kika yi babu kalar fadan da Baba be yi ma Mama ba saboda ta barki kin fita, na dawo gida na tarar baki gidan sai wani sabon fada ya tashi”

“Ka ce Mama ta yi hakuri ba zan sake ba”

Shi ne akwai abun da na ji zan iya fada, domin ni na janyowa kaina matsala da kaina, kuma Mama ta yi gaskiya kwadayina ne sila. Yaya Nabil ya fita daga dakin be jimawa ya dawo rike da maganin ciwon kai ya mika min.

“Ki Sha biyu idan jinin be tsaya ba anjima sai mu tafi gurin Saminu ya sake gyara miki gurin, ni ma gashi kina son ki zama silar korata daga aiki, Allah kadai ya san me kika masa da yace na zauna gida na kwana biyu”

Na san fadar gaskiyar zai sake jefani a matsala ne, dan haka na zabi shiru daman hausawa sun ce shiru ya fi yawan magana alheri. Ina cikin dakin ban fito ba sai da aka yi sallah magariba, a lokacin jinin ya daina min zuba, dan haka na nemi tsumma na gyara gaban kaina na goge jinin na saka wani kyalle na daure gurin sannan na fito na nufi gurin da buta take na dauka na zuba ruwa na yi alwala. Ina ganin ledodin Kareem Restaurant a tsakar gidan na san Mama sun cinye komai, hakan kuma ba karamin koma min rai yayi ba, ashe wahalar banza na sha ba zan ci komai a ciki ba. Da hawaye na gama alwala na mike tsaye kenan Hana ta fito daga bandaki rike da buta, Mama kuma tana dakinta tana sallah.

“Mama ta rantse ba zaki ci ba, shiyasa ban shiga da shi dakinmu na ci a dakin Mama”

Na kalleta cikin yanayi na rashin jindadi dake bayyana har a muryata na ce.

“Kun cinye duka kuma?”

Ta daga min kai.

“Mama ta miki haka ne saboda karki sake aikatawa gobe, dan Allah ki daina abun da kike Noor, dan Allah ki daina”

“Ba roka na yi ba, shi ya ba ni ku tambayi Yaya idan ba ku yarda ba, Hana har da yar tsutsar kun cinye?”

“Aa zubarwa aka yi, waye zai ci tsutsa idan ba ke da abinki ba Noor, abun kyama”

Ban sake ce mata komai ba na nufi dakinmu na shimfida dankwalina na saka hijab na fara sallah idan na yi sujuda sai na kai gefen goshina a kasa saboda rabin ciwon yake min. Ina gama sallah yaro ya shigo yana sallama, ina jin Mama ta amsa masa.

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now