Chapter 16

38 2 0
                                    

Barka da Sallah Allah ya maimaita mana.

6-Month Later...
@8:11am.

Yana tsaye rike da mug yana kallon harabar gidan aka wuce da motar yaransa zuwa makaranta. Sai da aka rufe gate din sannan ya juyo zai dawo wayarsa ta yi kara alamar shigowar sako. Hannunsa na hagu ya saka ya ciro wayar ya duba, sako ne aka turo da bakuwar number.

“I Love You
I love You Kareem Ina sonka sosai”

Haka ya bi sakon yana karanta kalma bayan kalma sai kuma yayi saurin kiran number da sakon ya shigo masa ya kara a kunnensa ya juyo ya sauko daga entrance din...

“Hello... Kareem...”

Dakika biyu ce tsakanin amsawa da Hello da kuma kiran sunansa, sai ya lumshe ido ya matse bakinsa domin be ji muryar da yake zaton sakon ya zo daga gurinta ba.

“Safeena What Now?”

“Na yi marmarinka Kareem, na san idan na kira da line na zaka iya kin dagawa, ina cikin damuwa rashin saka a ido da na yi, ina sonka Kareem ka sani ina sonka sosai”

Ya katse Kiran ya sauke wayar tare da ajiyar zuciya, sannan ya busar da iskar bakinsa. What he got himself into? Matar aure matar sunna ta tsaya tana fada masa yadda take kaunarsa, ya san ya cutar da Safeena na bin umarnin Momy ya auri Macen da ba ita zuciyarsa take ba, ya cutar da kansa kuma ya cutar da Safeena, gashi yanzu shi da ita sun fada cikin halaka. Ya shafa kansa sannan ya juyo ya nufo kofar falon ya tura ya shiga arba da yayi da Yusura tana mopping ya dada bacin ransa, domin ita ce macen da ta ruguza masa komai a rayuwarsa. Me yasa bata amsawa Mahaifiyarsa cewar ba zata iya zama da shi ba tana da wanda take so? Shi ba zai iya musawa Momy ba, amman ita zata iya fada mata bata sonsa da yanzu duk haka be faru ba, gashi suna da yara har biyu amman wani abu mai suna so be fara shiga tsakaninsu ba.

“Breakfast dinka is ready”

Ta fada masa ganin yadda ya tsaya a gurin yana kallonta fuska babu Annuri, ita kanta ba son take ya kalleta ba, yadda yake jin tsanarta haka take jin tsanarsa a zuciyarsa har ma ta fi shi. Ya dauke kai ya bar kofar a bude ya nufi stairs. Yana shiga dakinsa ya aje mug din ya aje wayarsa a saman gado ya cire tufafin jikinsa ya dauki bathrobe ya saka ya nufi bathroom kamin ya shiga wayarsa ta yi ringing. Juyowa yayi ya dawo ya dauki wayar ganin number mahaifin Hafiz ya saka shi zaunawa sannan ya amsa wayar cike da ladabi.

“Hello Abbah”

“Naam Kareem kana lafiya?”

“Lafiya Kalau Abbah ya gida?”

“Lafiya Kalau”

Daga haka Abbah yayi shiru be sake cewa komai ba har sai da Kareem ya tambaya.

“Abbah lafiya?”

“Lafiya Amman ni ma ita na kira na ji, na ga duk hidimar auren nan da ake ba ka zo ba Kareem ko last week da aka kai lefen abokinka na yi zaton zan ga domin maza suka kai lefe amman ban ganka ba, ko da yake dai ya ba da izuri cewar aiki ya maka yawa amman ina fatan dai ba matsala kuka samu ba”

Kareem yayi murmushi.

“Haba dai Abbah ni da Hafiz ai mun zama yan'uwa dangantakarmu ta wuce abota ina kallon Hafiz a matsayin dan'uwa ne na jini ba aboki ba, babu wani abun da ya shiga tsakaninmu kuma babu abun da zai taba shiga tsakaninmu har abada”

“Toh haka nake fatan ji, shi ma kuma haka ya fada min amman zuciya bata natsu ba sai shiyasa na kira da kaina”

“Abbah kullum muna tare da Hafiz ma, kasan gurin zamanmu daya, indai ba ina aiki ba kullum muna tare da juna, babu wani abu da ikon Allah”

“Tohm Allah ya muku albarka”

“Ameen Abbah Sai anjima”

Ya aje wayar sannan ya mike tsaye ya shiga bandakin. Ya dauke shi awa daya daga fitowa wanka zuwa shiryawa cikin manyan kaya kasancewar yau Jumma'a. Sai da ya dauki abubuwan bukatarsa sannan ya fito daga dakin ya sauko kasa ya fice daga falon yana zuba kamshi kamar shi ne angon. Motarsa ya nufa ya bude ya shiga ya murza key yayi warming din motar sannan ya kwanta ciki yayi relaxing yana murmushin da shi kadai ya san ko na minene. Can kuma ya dago ya ja motar yana danna horn Mai gadin ya bude masa Gate. A minti goma shabiyar ya isa kofar gidan mahaifinsa ya faka a harabar gidan da karin minti uku, ba yabo ba fallasa ya fito motar ya nufi kofar falon da zata sada shi da bangaren mahaifiyarsa. Gidanta gidane dake cike da jikokinta da na dangi domin kuwa ita mace ce mai tsananin son yara da yan'uwa, sai dai kasancewar safiya ce babu ko daya duk sun tafi makaranta. A falo ya sameta tana zaune ta dora kafafuwanta a karamin Center Table hannunta kuma rike da plate din dafaffen nama tana ci. Kusa da ita ya zauna yana fadin.

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now