Chapter -10

277 22 4
                                    

Follow the KHADEEJA CANDY channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

*Duk mai son ya rika samun Littafin TA KI ZAMAN AURE yayi following wannan Channel din mai suna KHADEEJA CANDY a nan zaku rika samu duka littafaina in Sha Allah*

✧✦ 𝗧𝗔 Ƙ𝗜 𝗭𝗔𝗠𝗔𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 ✦✧

𝗕𝘆 𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮 𝗖𝗮𝗻𝗱𝘆

*Talla👇👇👇*

KINADA DAYA DAGA CIKIN WADANNAN MATSALOLIN ❓👇👇👇
To kiyi saving numba ta ki danna wannan link👇 https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1 Idan kinyi saving ki fadamun zanyi SAVING TAKI😍ko Baki Siya yanzu ba WATARANA zatayi maki AMFANI👇👇
1.INFECTION CIWON SANYI 👉LALACEWAR BREAST👉RASHIN HIPS & BUTT👉KIBA TAYI MAKI YAWA KINASO KIYI SLIMMING👉TUMBI YAYI MIKI YAWA KINASO KI RAGE ?👉 AKWAI KUMA INGANTATTUN KAYAN MATA APHRODISIACS MASU KYAU DA INGANCI GA kUMA SABAYA ASALIN MAI KYAU 3500 only 👌

KIZO KI GWADA KAYAN AMNOOR INA TABBATAR MAKI BAZAKIYI NADAMA BA 👉 KIYI SAVING NUMBER TA  DM ME https://wa.me/message/N2S6DQEPETKQO1

*Chapter - 10*

“Dan nan? Kai kam uwar da ta haifo ka ta iya haihuwa, Allah mai iko na gode na gode Allah ya saka da alheri”

Baba ya kai kasa yana masa godiya har da kuka, ni kam mamaki ya hana ni rufe bakin sai kallon ikon Allah nake. Muna hada ido da Kareem na sauke kai kasa na bata fuska, domin abun da Baba yayi be min dadi ba, ina jin yin haka ba daidai ba ne. Sai dai ba babu bakin yin magana baba ya dafa ni danya ya cinye. Kareem ya sauke hannunsa a hankali kasa yayi yana motsa agogonsa har sai da na dago na kalleshi sai ya daga min gira daya irin na wadda ke tambaya a boye. Ban ce komai ba daman ni me zance a gaban Baba ko ba a gabansa ba ne na riga na daina duk wani abu da be shafe ni ba.

“Baba anjima Nabill zai kawo Noor asibiti a sake daure hannu saboda ba son a kwance har sai ta ji sauki, kuma kar ayi wasa da maganin da na kawo”

Na ji Kareem yana fada, sai na lake kafada daya bacin ran nawa ya kara bayyana na saka kuka a take.

“Aa Wallahi ni bana so, akwai zafi sosai”

“Aa ba sake taba hannun za'ayi ba, daurewa kawai za'ayi”

Ya amsa min hakan be canja kudurina ba na girgiza masa kai.

“Ni dai bana so a bar shi a haka”

Baba ya juyo kaina kamar mai jirana.

“Aiko sai kin so, ka ga sakaryar yarinya ko? Haka ta da sakarci, ba da zafi ake cire zafi ba, shashashar yarinya kawai”

Kareem ya kira sunan Baba a hankali sannan ya ce.

“Baba dan Allah ku daina kiranta da sunaye marasa kyau, kamar yanzu kace mata sakarya, su iyeye kamar wani bakin tabo ne a jikin farin tufafi duk yadda ya diga sai ya bayyana, shiyasa ake son a rika taka tsantsan da kalami, yara basa jin magana mun sani dukanmu muna da su, amman a haka muke kai zuciya nesa idan ba haka ba, sai mu yi barna kuma a karshe dai mu din ne za mu wahala, misali yanxu kana kiranta mahaukaciya to ba zata taba yin hankali ba, ko da kai mutanen unguwa ne suke mata wannan ikirarin balle mahaifi. Amman fa ka yi hakuri na shiga tsabgar da ba tawa ba”

“Aa ai gaskiya ka fada, haka ne Wallahi ai bakin ne ya saba kuma ita wannan Noor din idan ka zauna da ita na wuni daya, In Shaa Allahu sai ka ji ta gundureka saboda bata jin magana sam, shiyasa ma nake so na aurar da ita na huta”

Na kalli Kareem sai na rufe idona ina jin kunya ta rufe ni, ta dayan bangaren kuma ina jindadi, ni kaina ai na fi son ayi min auren ma na huta domin na san Zafeer ba zai min abun da ake min a gida ba, shi ba zai taba gajiya da ni ba.

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now