Chapter 15

47 3 0
                                    

Ni da Hana kuka muka sha har muka gode Allah, ni dai sai tunanin ya zame min biyu tafiyar Mama da kuma Zafeer, tsammanin da nake Yaya Nabil yayi min fada ko duka ko ya min wata maganar babu ko daya, haka muka kwana cikin bakinciki da kuka. Baba be shigo ba sai da safe, a lokacin ragowar karfin jikin ma ya tafi ya bar ni, zazzabi kuma ya rufe ni har bana iya daga ido da kyau, ina jin lokacin da Baba ya shigo ya bawa Hana kudi wai ta siyo kunu, ta tashi ya fita bata jima ba ta dawo da kofin kokon ta aje a nan dakin ta nemi guri ta zauna ta yi tagumi, duk irin yadda take kaunar makaranta da rashin son wasa da karatun da take a yau ban ga tana shirin tafiya makarantar ba. Ina jin motsin fitowar Ya Nabil amman be cewa Baba uffan ba ya koma ciki, ba kamar yadda yake gaishe shi da safe idan ya ganshi ba, ni ma da na saba lekawa na gaishe shi a yau sai na ji bana bukatar ganin fuskarsa ko yi masa magana. Muna zaune dakin kamar wadanda aka yi ma mutuwa har wajen karfe goma sha daya, sannan Yaya ya sake fitowa yana wanke baki wato brush muka ji an buga kofar gidan, gabana ya fadi wata zuciyar na raya min cewar Zafeer ne ko wasani nasa. Sai da Yaya ya gama wanke bakin sannan leka waje, ya dan dauki lokaci sai dai ba sosai ba ya dawo cikin gidan ina hange lokacin da ya shiga dakin da Baba yake wato dakin Mama, sai na ga hango Baba ya fito da sauri ya fita. Wata zuciyar sai ta raya min cewar wani ne daga familyn Mama wata kila ya biyo sawu ya ji abun da ya faru. Sai dai yadda Baba ya dawo ya shigo dakinmu da kuzarinsa ya katse hanzarina.

“Ina... Nooriyya...”

Na tashi zaune jiki babu karfi.

“Taso ga Alhaji nan ya zo”

Na tashi tsaye ina jin kamar ba zan iya tsayi ba, ba kuma dan na san wane alhajin yake magana a kai ba.

“Saka Hijabinki mana”

Na juya na dauko hijabin na saka na bi bayansa, sai da muka fita waje sannan Baba ya tsayar da ni ya ce.

“Ke saurara kar kije ki yi hauka, kin ga dai mutumen nan mai mutumci ne, kuma yayi mana karamci yadda ya dace, zuwan da yayi yanzu yace min ya zo da magana ne, kuma na fahimci maganarsa ta neman aurenki ne, ban riga na bashi ba, amman dai na fada masa ke ma kina maraba da hakan, karki kunyata ni Noor, Allah ya ba mu wannan damar ya ba mu wannan ikon na zabawa yarinyar mijin da zai dace da ita, kuma ni ubanki ne ba zan zaba miki abin da zai cutar da ke ba, dan haka nake son na baki umarni ba shawara ba, duk abun da ya tambaye ki ki amsa da eh karki karyata mahaifinki karki saka kimata ta zube a idonsa, ki tafi a natse ku yi magana ta hankali idan kika dawo zamu yi magana ta fahimtar juna kin ji ko?”

Na daga masa kai ba dan na fahimci duka yaren da yake karanta min ba, ina mamakin  yadda ya kwantar da murya yana min magana kamar ba shi ba, abun da tun da na zo duniya be taba min ba, na bude ido ne da tsawarsa da duka ta tsana da fargabar fadan yau dabam gobe dabam. Na fara takawa ina ganin hanyar tana rabe min na isa gurin kofar na fita daga kan da zan yi na kalli dama da ni sai na hango Zafeer a tsaye nesa da kofar gidanmu ya rumgume hannayensa yana kallona. Na dauke kaina na nufi gurin da Abokin Kareem yake a zatona Kareem din yana cikin motar ne. Na karasa gurin na tsaya na rumgume hannuna ina jin hawaye na bin fuskata.

“Noor..”

Na ji ya kira sunana, na kasa amsawa kuma na kasa daga kai na kalleshi.

“Noor magana ce na zo da ita kuma na ga baki cikin yanayin da zamu yi maganar, amman zaki iya komawa ciki zan dawo anjima”

Na girgiza masa kai domin na san komawa ta ciki zai iya zama laifi.

“Noor akwai wata matsala ne?”

Na yi shiru, sai ya gyara tsayuwarsa.

“Please ki shiga ciki zan dawo anjima”

Kamar ina jira sai na juya da sauri na dawo cikin gidan ina jin kamar ana turani. Ban karasa dakinmu ba juri ya dibeni na fadi a tsakar gidan sai ga Baba da gudu ya zo ya kamani.

TA ƘI ZAMAN AURE...Место, где живут истории. Откройте их для себя