Chapter -8

136 17 0
                                    

Daga Yaya har Mama babu wanda ya ce da ni shigo ki zauna ko kuma juya ki koma. Ina tsaye a gurin na kasa kuka na kasa magana har Baba ya shigo.

“Shiga ciki ki zauna mana, ai duk abun da kike ba laifin ki ba ne uwarki ce ta ke goya miki baya, baki da matsala ke”

Cewar Baba sannan ya wuce ni ya shiga cikin gidan. Mama kamar tana jiransa ta ce.

“Daman ai kullum ni ce ice mai dadin hawa, nan gana Noor ko kisan kai ta yi ni zaka dorawa laifi, duk abun da kowa zai aikata kaina zai dawo, shin ni kadai nake da hakkin tarbiyantar da ita? Kai ba Uba ba ne?”

“Saboda ina uba sai aka ce na zauna gida na kula da yara? Tarbiya ai ta uwace no Cewa aka yi na fita na nemo, ke zaki kula da gida dan haka dole duk abun da yara suka yi na ce laifin ki ne”

Mama ta yi shiru na san kuma ba dan ta rasa abun cewa ba sai dan tana gudun fadan yayi nisa.

“Ni na gaji da halin yarinyar nan, tun da aka haife ta cikin wahala nake, kar taje nan gaba ta dauko min abun magana tun da har ta gane bibiyar maza a inda suke, daga bige hannu da kai ban san inda za'a tsaya ba, ko yanzu Allah kadai ya san gaskiyar abun da ya faru, kar taje ta dauko min abun kunya na kasa fita cikin jama'a, zan fadawa yaron idan ya shirya fito ayi auren daman ni dai ba wani abu na aje ba, balle na ce zan dauka na kai masa, ko zane daya Allah ya hore masa ya kawo a hada ya da tabarma ayi musu aure su je can su karata, ke dai ba iya tarbiyarta kike ba tun rana karama balle kuma yanzu da take kara girma”

A fusace Mama ta mike tsaye sai ganin na yi bulalar wayar wuta ta fado a jikinta.

“Wai Malam tunanin kake abun da Noor take dadi yake min? Ko kuma ganin kake ni nake zaunawa na tsara mata shirirtar da zata je ta yi a waje? Daga Islamiya fa ta bar yar'uwarta ta tafi gurin yawon shiririta, a can idan kasheta za'ayi an dade ba'ayi ba, kuma kamar Noor ace ta san ta tsame kafa ta bi wata su tafi restaurant, kanen ubanta ne a can ko na uwarta, babu sanarwa babu neman izinin kowa”

Baba ya rike gemu.

“Toh.... Ai ga irinta nan a gabansu kike fada min magana son ranki kina min tsawa saboda kin isa, ai tarbiyarce suke kallo suna dauka”

“Tarbiyar ce, idan baka Gamsu da ita ba Malam ka auro wata uwar ta zo ta ba su wata tarbiyar, daman ai ka saba aure aure”

Yau kai na ga dabam, Baba ce take fadawa Baba magana cikin bacin rai abun da bata taba ba a gaban idona. Baba kamar yana jira sai ya nufe ta yana nuna kansa.

“Ni kike cewa na saba aure aure...?”

Ya Nabil dake zaune yayi hanzarin mikewa tsaye ya tare Mama ya shiga tsakiyarmu.

“Toh ko dukana zaka yi? Nace dukana zaka yi?”

“Ba dukanka zan yi ba Baba amman ba zan zuba ido ina kallo ka daki Mama ba a gaban idonmu, Baba abun da kake babu dadi wani abun ba laifinta ba ne amman sai ka dora mata laifi komai aka yi a gidan nan cewa kake laifinta ne, ta ina yanzu laifin Noor ya shafe ta? Baba be kamata ace a gaban idonmu ka doke Mama ba wani abun ai ka daga mata kafa ko dan mu”

“Ayyy haka ne, lallai Nabil wuyanka yayi kwari, yanzu ni zaka zauna ka tsarawa magana haka son ranka? Ashe kai ma baka da mutunci toh sai ka doke ni na san ka girma marar mutunci, saboda ina talaka kake raina ni?”

Mama ta ja Nabil gefe ta tura shi.

“Fita can waje idan ya fita sai ka dawo...”

Tana rufe baki Baba ya dauke ta da mari.

“Ya fita sai na fita ya dawo wato ga mahaukaci ko? Ga mahaukaci na hauka”

“Baba...”

Ya Nabil ya zaburo da karfi yana hakki har sai da Mama ta rike shi.

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now