Chapter 18

51 2 0
                                    

Ni dai tsoro ya kamani zuciyata na raya min ko dai cewa aka yi a samo mai irin soffofina. Sam zuciyata bata natsu da wannan ba. Saboda haka na yi amfani da Hana na saka ta ari wayar Ya Nabil da sunan wata yi ma kawarta flashing ta kawo min.

“Noor Allah yasa ba wani abun zaki yi ba”

Na karbi wayar ina dan turo baki.

“Ni me zan yi ba Hafix ne yace na ari wayar na kira shi ba, kuma kin san idan ni ce ba zai bani ba”

“To kina da numbershi a kai ne”

“Ina da shi a littafi dai”

“Kin san halin Yaya dai dan ana bikinki ba zai hana yayi miki dukan tsiya ba, kuma dan Allah karki kira Zafeer”

Na mata banza na tashi na dauko littafin na zauna a gafe daya kamar ina saka number alhalin number Kareem dake cikin wayar Yaya nake dauka. Sai da na gama na mika mata wayar

“Gashi na ma fasa kiran”

Ta karba ta duba sashen kiran ta ga ban kira ba ta sake miko min.

“Ni ban hana ko kira ba amman karki kira Zafeer da wayar Yaya kin san abu mai sauki ya hada mu yayi mana duka, kuma kowa ya ji ya san baki yi daidai ba”

“Ni fa ba Zafeer zan kira ba, ai Baba yace be yafe min ba idan na yi magana da shi Wallahi ba shi zan kira ba, kuma ki bar shi zan ari wayar Gwaggo na kira da ita”

Duk yadda ta so na karbi wayar sai na ki saboda sanin halin Yaya da na yi kamar yadda ta fada. Sai da ta fita azuwan mayar masa da wayar sannan na fito na tsaya daga jikin kofa na ari wayar Anty Larai domin ita ce mai lafiya a cikin yan'uwan mahaifina. Har ta ba ni na juya sai kuma ta kira na juyo bata ce min komai ba sai da na matsa kusa da ita.

“Noor Allah yasa dai ba tsohon saurayinki zaki kira ba?”

“Wallahi ba shi zan kira ba Anty Larai ai Baba yace be yafe min ba idan na sake magana da shi”

“Toh, na san ai kina da hankali ba kamar yadda suke fada ba tafi ciki ki yi wayar”

Na shiga dakin na nufi littafin da na rubuta number Kareem jiki na kwashi number na saka a wayar Anty Larai sannan na fito daga dakin na faki idon mutane na shige bandaki na rufe sannan na aika masa da kira.

KAREEM POV.

Jikin Momy ne babu dadi kwana biyu, ciwon da take yawan fadar rayuwarta yake nema ya sake sallamo mata sai dai wannan zuwan be tsanannta kamar yadda yake tsanani idan aka bude file dinta ba. Tun daga ranar da take jin fever din yana zagoyo mata Yusura take ta zirga-zirga na zuwa dubata, idan ta gama abun da take Kareem zai wuce da ita ya sauke ta gidan Momy sai dare zai dauko ta. Kasancewar yau Jumma'a babu makarantar Allo da Yamma washe gari kuma Weekend ne babu boko sai ya kwasa har da yaransa suka tafi duba Momy, ba sabon abu ne ba a gurin yaran kusan ko wane yana kai su su wuni sai dare ya dawo da su domin Momy mace ce mai son yara kuma gidansa ma yana cike da yara a duk ranaku hutu na yayan da ta raina ta aurar ko na Abokiyar zamanta ko kuma na yan'uwana.

Kamar kullum yau ma sun tarar da jikokin dangi da kuma na kanwar Kareem dake aure a garin. Hakan kuma ba karamin dadi yayi ma yaransa ba domin suna fama da kadaici a gidansu da babu kowa sai kayan kallo. Yusura ta shiga dakin Momy da lullubinta da far'a tana yi mata ya jiki. Kareem ya zauna kusa da mahaifiyarsa yana sauraren yadda take amsawa Yusura tana shi mata albarka.
Yusura ta kalli Mijinta fuska a sake kamar ba ita ba, ta ce.

“Abban Tine ba zaka matsa Momy ta koma asibitin nan ba? Yau kwana biyu jiki ya ki dadi fa”

“Akwai wasu magani da muka dora ta akai, kin san ciwon ya kan taso wani lokacin kwana biyu sai ya tafi, to daga yau zuwa gobe dai idan ba a samu sauyi ba dole asibiti zamu koma”

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now