Chapter -7

102 9 0
                                    

KAREEM POV.

Kareem yayi kanta da sauri ya rike Safeena yana kokarin kwatar hannun Noor da ihunta ya cika dakinta tana fadin hannunta.

“Safeena karki karya mata hannu”

Daker ya kwaci hannun Noor a hannunta ta murgude hannun har yayi yaushi, gaba daya Noor ta rude kamar wadda ta fita hayyacinta ta fadi kasa ido a zare tana haki.

“Kin fita daga hayyacinki ne? Me ke damunki?”

Kareem ya tambaya cikin tsawa kamin ya juya ya rika ya kai hannu zai taba hannun Noor sai ta juyar da shi dayan gefe.

“Ya karye Azzaluma yar masan wuta ta karyashi”

Noor ta fada cikin kuka. Kareem ya shiga mata magana a hankali cikin rarrashi yana kokarin rika hannun ya duba.

“Be karye ba, kawo na gani”

Wani hawaye mai zafi ya saukowa Safeena, zafin da take ji a zuciyarta ya fi wadda Noor take ji a hannunta. Duk abun da ake Hafiz na zaune yana kallo be ce kuma be yi yunkurin yin wani abu ba, sai a lokacin da ya ga hawaye ya sauko a idon Safeena.

“Tirr da ke, tirr da uwa irinki... Tir da mata irinki... Tir da haihuwar ya irinki, tir da auren mace irinki, indai har sabon Allah ya kai ya rufe miki ido ki kama hannun wata ki murde saboda kishi, A gaban idona to kin yi hasara kuma kin cika tantiriyar yar iska, kuma haka da kika yi ba zai hana Kareem auren yarinyar nan, albashi sai ki hade zuciya ki mutu”

Ta dauke idonta daga barin kallon Noor ta kalli Hafiz, kamin ta kai hannu ta taba hawayen da bata san da saukarsu ba sai a lokacin, ta yi murmushi ta dubi Kareem dake fadin.

“Babu komai tsakanina da Noor, wace magana kake haka? And ka cire bakinka daga magana da ita, babu ruwanka idan zaka yi magana ka yi da ni ba da ita ba, ba ka da wannan hurumin”

Dauke kai Safeena ta yi ta juya ta fice daga office din. Kareem ya kalleshi cikin damuwa ya ce.

“Akan me zaka fadi wannan maganar? Zata dauka da gaske ne, Safeena tana da mugu mugun kishi, baka san abun da zai je ya dawo ba”

Hafiz ya wulga masa wani wulakantaccen kallo. Har zai yi magana sai kuma ya juya ya kalli Noor da ta cire hijabi saboda wani azabar zafi da take jin ya game jikinta gaba daya sai kuka, Kareem ya ci albakarcin Noor tana gurin ba dan haka ba, Hafiz zai fada masa magana ne marar dadi, sai dai baya son Noor ta san komai dan haka yayi shiru. Kareem ya juya ya kalli Noor sannan ya nufi gurin da keys dinsa suke ya dauka, ya nufi inda take.

“Taso mu tafi asibiti zan duba miki a can”

Noor ta girgiza kai tana jin wani irin azaba a hannu.

“Aa a barshi haka, gyaran akwai zafi ni taimakonta kawai na yi, me yasa zata min haka? Miye laifina ni?”

Kareem din take tambaya tana kuka sai gumi take. Kareem yayi shiru yana kallonta cike da tausayawa ya rasa me zai ce.

“Mamana bata san na zo nan ba, jiya sai da ta yi min duka sai da kaina ya fashe saboda kai, bata bar ni na ci komai da na tafi da shi ba, yau kuma wata ta karya min hannu saboda kai, kuma na san Mama sai ta min duka ko Baba, na san haka zata min ba zan biyota na zo ba”

Tausayinta ya kama shi. Ya sake mika hannu ya rika hannun ta kauce tana kokarin mikewa tsaye.

“Be karye ba Noor, duba kawai zan yi sai na baki magani, idan akwai zafi ba zan taba ba na miki alkwari”

Ta kalleshi.

“Rantse”

Ya daga hannunsa.

“Na rantse”

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now