1

5.6K 334 35
                                    

Amirah  Yarinya ce kyakkyawa. Son kowa kin wanda ya rasa. Yar fillo mai farin jini. Tana zama da iyayen ta da yan uwan ta a garin Maiduguri in da babanta ya samu transfer.

Ta fara zuwa sabuwar makarantar su ita da Yayan ta da kanwar ta guda daya. Sauran kannen ta suna zuwa makarantar primary ne can kusa da gidan su.

Shekarar da su Amirah suka shiga makarantar an kawo wani sabon malamai wadannda suke bautar kasa. Da Mr. Ade, Miss.Fadila da Mr. Aslam.

Mr. Aslam aka bar shi yana kula da yaran aji 6 wato ss3. Ajin yayan Amirah. Miss Fadila kuma aka hadata da mara sa jin maganan makaranta wato aji 4 ss1 ajin su Amirah. Sai Mr Ade na aji 1 wato jss1.
Sannun kuma Mr Ade na taimakawa a labaretori na biology yayinda Mr Aslam da Miss Fadila suke taimakawa labaretory na Physics.

Kun san dai yanda yan mata ke yi idan sun ga saurayi kyakkyawa. Toh haka yan matan makaranta suka fara bibiyar Mr Aslam. Shi kuma ba wanda yake so sama da Amirah!!! ..




4.3.2017


Labarin Amirah. Where stories live. Discover now