2

3.8K 267 31
                                    

Rayuwar Amirah
Part 2

Nura Aslam, dan saurayi da bai dade da gama Jami'a ba ya samu aiki a Jane group of schools.
Ya zo ne ya koyar da yara amma bai san yanda akayi ya fara son wata yarinya ba. Amma he was careful. Bai bari kowa ya gane ba. Nura mutun ne mai fara'a da yawan wasa. Sabida haka mutane da yawa suna son sa harta malamai suna son yi mu'amala da shi.

Lokacin assembly da safe sai ya samu kan shi yana kallon layin yen Ss1 bayan yan SS3 ne daliban sa. Wata rana Miss Fadila ta tambaye sa mai yasa yana son kula da yan ajin ta kawai yayi mata murmushi yace ya san su ne da rashin ji kawai baya so su na bata wahala ne. Fadila sai taji sanyi a ranta.

Rayuwa ta ci gaba kwanar Amirah Julde ya kara yawa a zuciyar sa. Ita kuma Amirah bata da damuwa a rayuwar ta. Ko wa ya riga ya san ta .. bata jin magana. Duk malamin da ya shigo aji zai yi duka sai ya duke ta koh tana cikin masu laifi koh bata ciki. Abun har ya zama mata jiki. Da anzo duka a ajin tashi take yi ta bada annun ta kawai ayi a gama. Ita bazata iya musun ba sabida bata lokaci ne. Harta mazan ajin sun safa mata lafiya. Ita ce new student amma kuma ta fi su iya shege.

Wata rana yan aji 4 suna jin yin rashin mutunci. Suka tashi suka samu motan principal suka painter ta, suka wasa gutter a kan machine in malamin su na mathematics. Suka kyarya mirror na bike in Mr. Aslam saboda shi abokin Ms Fadila ne kuma ms Fadila ta basu haushi amma ba abun da zasu iya mata.

Washa gari a assembly aka tsayar da yan ss1 za'a musu duka. Dama an riga an kama mace daya da maza biyu. Aka ce su fito da sauran da suka taya su yin aikin nan da wanda suka bada sha waran yi.
Akayi nuna kowa banda mutun 4. Amirah included.
Principal yace bai yarda ba dole Amirah na ciki. Yan aji suka ce bata ciki kuma ma ta tafi gida da wuri jiya. Aka ce toh ai tana cikin yan shawara kenan, yan aji suka ce a'a ita ce wa tayi ba ruwan ta kar suyi haka.
Ms Fadila ta karyata su tace suna so su kare mata ne kawai.
Amirah ta ce ba komai ita zatayi punishment in.

Principal ya bawa Mr Aslam bulala yace ya zane su. Nan take mr Aslam yace wa Amirah ta tafi aji shi ya ga wanda sukayi aikin kuma bai ganta a ciki ba. Miss Fadila zata musa yace mata ai yan ajin su suka ce bata ciki , ita ma Amirah tace bata cikin su amma mai yasa baza'a yar da da ita ba sai ata duka kaman jaka.
Yace wa Amirah ta tafi aji. Nan take Amirah ta fara kuka.

Ita kan ta bata san mai yasa take kuka ba. Duk dukan duniyan nan idan za'a mata bata taba kuka amma yanzu da taji wani ya yarda da ita kuma baza'a duke ta ba kawai sai ta fara kuka. Kowa ya ji mama ki a wurin.
Yau ga Amirah na kuka.
Bata ce masa komai ba kawai ta tafi ajin ta. Ta sha ruwa ta sha re hawayen ta.

For the 1st time ba'a duke ta ba idan ana dukan yan ajin su tunda ta shiga makaranta Jane group of schools.
Dama ko a makarantan ta na da ma dukan ta ake kamar Jaka.


4.3.2017

Labarin Amirah. Where stories live. Discover now