17.

1.4K 148 3
                                    


Rayuwar Amirah

Part 17

"Hauwa ya ibada? Munyi missing naki" 

"Maman Nabil. Alhamdulillah. Ya kike ya raino?"

"Wallahi lafiya lau. Ai hajiya Kaka is doing most of the job."

"Gaskiya kam. Tana kokari. Kai ta bani wahala ai. Thank God na gudo Saudi. Nabil ya daina kukan dare koh?"

"Ea da sauki dai. Idan na koma gida zanyi miki sending pics nashi"

"Ibrahim ya turo min hotun da suka sa kayan I love daddy ai. Nabil da Nawfal. "

"Haba? Ga ni nan da shi ma in bashi kuyi magana ne ?"

"A'a ki bari. Munyi magana dazu" taji Ibrahim ya amsa ta. Tayi mai murmushi tace toh

"Toh Hauwa sai anjima. Ayi ibada da kyau. Ayi mana addua. Ban da waya da babe dayawa. Ibada kika je yi ba love ba " Amirah ta dan kalli Ibrahim yayin da ta ganshi ya na murmushi sai ita ma tayi dariya

"Kin ji ki koh. Toh zan muku addua. A shafa min kan Nabil na. " tayi dariya

"Insha Allah. Toh sai anjima." Suka gama waya ta kashe.

Ibrahim ya kai ta gida ya shiga ya gaishe da kowa ya basu dan abun da ya shiyan musu da special abu na Hajiya kaka sanna yaga baby Nawfal da Nabil kafin ya tafi.

Amirah na kwance a gado tana dariya tana chatting. Nafisa tazo ta kwanta kusa da ita.
"Da wa kike chatting?" Ta leka wayanta. "Ohh Tahir ne. Kwana biyu banji labarinshi ba."

"Haha. Ea walahi mun kwana biyu bamuyi hira bane. I've been busy with work and the baby."

"So how are things going?" Nafisa ta tambaya

"Not bad. Yace zai zo Yola ma soon. Kullun sai yace na tura mishi hoton Nabil da Nawfal ai."

"Ayya. Idan ya zo zaku hudu? Zai zo gida?"

"May.....be..." Amirah ta amsa.

"Wani irin maybe? Ni ina so na ganshi fa tohm. "

"Zan ce wa Ayman ya zo ya dauke ki ku koma gidan ku ai kafin nan. Dama ai kin riga kin gama jego." Amirah ta mari hannun kanwar ta.

"Na kara haduwa da Mr. Aslam da matarshi yau. Da na fita da Ibrahim." Amirah said sadly. .

"And.. ? "

"And I let him believe what he saw."

"It's for the best ai. In sha Allah."

"I guess"

"Now. Back to Tahir...." Nafisa changed the topic.

****

Nafisa da Amirah suka shiga motan Ibrahim tare da yaran su. Za suje gaishe da Yayan baban su da ya dan tsofa kadan. Allah yayi wa matarsa rasuwa shekarun baya. Yanxu shi da yaran sa ke zama a gidan. Baban dan sa yayi aure ya gina gida dab jikin bango kusa da gidan baban sa yana zama. Saboda yana samu yana kula da baban sa da kannen sa.
Hauwa wacce ta amsa kiran Allah bana 'yar yayan baban su Amirah ce. Ta haihu amma likitoci sun hana ta breastfeeding. Da tayi zaman jegon ta a gidan su Amirah na wurin kwana 25 sai lokacin tafiyan ta saudi yayi ta bar jaririn wurin Amirah da Hajiya Kaka su kula da shi. Dama kuma Maman Nawfal wato Nafisa ita ke shayar da shi tun da aka haife shi kwana uku 3 bayan ta haifi Nawfal. A haka Nabil yayi mamani da dama. Hauwa ce maman da ta haife shi, Nafisa ce maman da ke shayar dashi sai kuma wanda take rikonshi ita ce Amirah. Yanxu mutane da dama sun san ta as maman Nabil.

Suka isa gidan Baban Hauwa. Sun zo su gaishe shi kuma su nana mai yadda jikokin sa ke girma masha Allah. Mijin Hauwa wato Ibrahim ya durgusa har kasa ya gaishe shi cikin mutun ci. Baban Hauwa mutun ne mai saukin kai. Ya na da son hira haka ya saba da su Amirah. Duk da Ibrahim na da kama kai da rashin so sake jiki sai da Baban Hauwa ya sa shi ya fara sake jiki a gaban sa.

Har sanda ya tsokani Nafisa a kan Ayman yasa Ibrahim ya kira yayan shi, Ayman a waya suka gaisa. Ya ringa damun Amirah kuma akan sai ta bashi labarin saurayinta wai yaushe zata fito da miji. Amma bai takura mata ba dan yasan komai nufin Allah ne.
Suka koma gida cikin farinciki da albarka da Baban Hauwa yata sa musu.

Nura ya sha kona ya gansu sun fito diga gidan.

****

Amirah na zaune gurin desk nata a wurin aiki sai wayanta yayi ringing. Bata gane number ba amma kawai ta yi picking sai ta fita diga office in domin ta amsa wayan.

"Salamu alaikum."

"Wa'alaika salam" ta amsa mai magana. Muryan shi kaman ta dan gane.

"Sorry please da Amirah nake magana koh?" Nan take Amirah ta gane muryan mai magana.
Bakinta ya rufe gam. Ta kasa magana.

"Hello. Amirah? Kina ji na? Hellooo"

Ta yi kokarin amsawa amma muryanta yaki fitowa.
"He...hello" da kyar maganan nan ya fito kuma bata ji dadin yanda muryanta yayi ba 

"Uhm Amirah. Nura Aslam ne."

Shiru bata kara cewa komai ba sai yayi deciding ya cigaba da maganan shi.

"Nasan you can hear me so i will just keep talking. Uhmm.  It was really nice seeing you again. You didn't really change much though it looks like you lost some weight. Is the work hectic? I prayed for you alot that Allah makes everything easy for you and protect you and... if there is a chance for us I prayed that we meet again. You saw Aisha the other day right. She really is heavy. We are having our first child together.... well make that the 3rd child. Hamid and Hamida have really grown up even though they are still cry babies haha... I thought you might be curious about them. Ranan na fito zan ga abokina sai naga kun fito diga gidan baban abokin nawa. Ina ta so na miki magana. Na ganki tare da Ibrahim and your sister da babies in ku a hannu. Masha Allah. Allah ya raya. So I just wanted to call dama.  I had your number saved in my heart. When i dailled i just prayed zai shiga I was hoping baki chanza number ba. Na cika ki da surutu koh?" Nura yayi dariya sanda yasa Amirah ma ta danyi dariya amma da bakinta a rufe saboda kar yaji. Amma inaa too late ya dan ji kadan amma. And he smiled in satisfaction.

"I have one question I would like to ask you. Just one. Because my instincts are telling me something else from what I've seen so far. Amirah are you married?" Yayi tambayan shi.

Zuciyan Amirah na bugun uku uku. Bata dan mai zata ce mai ba. No tasan mai zata ce mai amma koma ta rasa dalilin da yasa ta kasa mai magana.

"Ehn ? Amirah can u atleast answer me. Yes or no kawai will do."

Nura ya jira bata amsa ba har ya gaji.

"Toh naji Amirah. I will call again when you feel like talking. I simply asked u for a simple yes or no. My instincts tell me that you aren't married that he's not your birth son though Aisha told me you aid you had a son. You could just answer me Yes or No. I believe my instincts are correct until you prove them otherwise."

Ya jira ta amsa bata amsa ba. Har zai kashe wayan sai yaji tace mai
"Yes"






18.3.2017

Labarin Amirah. Where stories live. Discover now