🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part.. 1

6.7K 276 6
                                    

🥀🌺🥀FAHIMTA 🥀🌺🥀

Xinnee smart

@zinnira Muhammad whatppad
a user
1.......... Sad'ad'e takeyi tamkar wata 'barauniya Saida ta tabbatar bawanda yaganta ta fyalla a guje, bata zame ko inaba Sai bayan layin su gidan Amina Amarya tanufa, tanashiga tayi sallama,

Amina dake tsakar gidan ta amsa had'i da washe baki dantasancewa yanzunnan za aimata wanke wanken da takasa yi tun safe,

Dan zainabu yarinyace da bata da ganda kokad'an, shiyasa suke Shiri sossai dan Amina akwai son banza,

A a, zainabu kece tafe da yammannan? yau bazaki islamiya bane? duk Aminace taimata wad'annan tambayoyin, itakuwa bata bata amsa ba Sai da takwankwad'i ruwan randar Aminan Mai sanyi, tayi ajiyar zuciya,

Ina yini? Tafad'a lafiya 'kalau Amina tafad' a cike da fara'a akan fuskarta, Dan Amina macece Mai fara'a sossai, hakan yasa yara keson zuwa gidanta yin wasa,

Zainabu ince dai ko lafiya yau bakije makaranta ba?

Lafiya 'kalau yau yini nayi baba bata bani abinci ba shiyasa nikuwa nace bazani makaranta ba shiyasa tana shiga d'aki nagudo, ta'karasa idonta taf da hawaye,
tausayin tane yakamata, tace Ina zuwa, madafi tanufa ta d'ebo abinci a plate takawomata, aikuwa kamar jira take tasoma ci hannu baka hannu akushi, ko d'agowa Batasonyi dan ganintakeyi kamar za'a kwace, Saida tacinye tas tasud'e hannu sannan tad'ago ruwa Amina tami'kamata ta kar'ba tashanye tas tayi hamdala, mi'kewa tayi tanufi kwanukan wanke wanken tafara wankewa bayan tad'ebo ruwa a rijiya, Amina kam madafi tanufa tafara 'ko' karin d'aura girkin dare dan yamma yafarayi, cike da tausayin rayuwar zainab takeyin komai

Itakam tanajin tausayin yarinyar, a ranta Sai dad'a tsinewa halin wasu mata take,

Zainabu nagamawa tayi kwanciyarta Kan sumintin 'kofar d'akin Amina take bacci yai awon gaba da ita,

Kiran sallar gariba da akene yasa Amina tashinta,zainabu... Zainabu, tad'an bibbigi' kafarta, 'ko' karin cigaba da baccin take Amina tace tashi kiyi sallah Jin ta ambaci sallah yasa tabud'e idonta duhun magribar da taganine yasa tami'kewa ba Shiri,

Kuka tasa yaukam nashiga ukku dan nasan baba kasheni zatayi, cike da tausayawa Amina tashiga rarrashin ta Kan ta tsaya tayi sallah taci abinci, amma Ina hankalinta yayi gida, da'kyarma ta tsaya tayi sallah,

Amina nafad'in ci abinci sai inrakaki, batama tsaya saurarenta ba tafice dasauri kamar zata tashi sama,

A d'arare tayi sallama tashiga gidan, kamar yadda ta zata baba nazaune Akan tabarma tana sauraren radio muryar amurika,

Cike da fargaba ta 'karasa kusa da ita,
Baba sannu da gida, ko d'agowa batayiba bare tasaka ran zata amsa, tana Nan a dur' kushe yayin da gabanta ke tsananta bugawa,

Har aka Kira sallar isha 'I. Kanzil ba tace mata ba saima tashi da tayi tashige d'aki tabarta,
Itama tashi tayi tashiga ru' ba'b'ben d'akin ta a d'arare ta kwanta Kan lamushashiyar tabarmarta, zuciyarta cike da fargabar shirun baba dan tasan ba alkhairee bane, a haka bacci 'barawo yasace ta............................................................................
Janda yakewa tabar shi zai tabbatar maka da ransa a' bace yake,shifa takurar nan ta ishe shi why why??? Dolene he is not interested in marriage, why mom da Dad zasu takura lalli sai yayi aure,

Ina.... Bazai yuba aure at this age dayake morewa 'kuruciyarsa? Bazai yarda yalalata rayuwarsa dalilin wani aure ba, haka kawai yakawo yar sa ido a gidansa? Nooo tafad'a da' karfi kamar wani zararre, ai kozanyi aurenma bada wannan banzar yarinyar ba, itakuwa mommy ta matsa da Sai na auri wannan mara kamun kan, mtssss yaja wani dogon tsaki cike da damuwa,wani wawan zu'ka yaiwa tabar wanda baisan ta'kare ba Sai Jin zafin wutar yayi a la'b'bansa uchhhhh yasaki yar 'kara had'i da shafa gurin, farin hankie d'insa yasa yagoge bakinsa,

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now