🥀🌺🥀FAHIMTA 🥀🌺🥀Part 7

1.8K 106 0
                                    

🥀🌺🥀 *FAHIMTA...* 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed her life...._

*XINNEE SMART*

*this page is for you maman* *gid'ad'o na,* 😍 *inajin dad'in* *yadda kike bibiyar labarin nan* *Allah ybar 'kauna* ❤

*My princess Allah ybaki lafiya* 😢👏🏻

7....... Tafiya ake wanda tun zainabu na marmarinta har ta daina, sai tunane tunane da yacika zuciyarta, gata dai yarinya ce ba wata babba ba amma damuwa da tunani tuni tasaba dasu kamar wata babbar mace,

    Tsawon awanni ne yasada su da jahar ta Niger, wanda Koda suka Kai zainabu tagaji har ta tsige boni, dan dama bata ko karya ba ga uban 'kishi da yacika ma'koshinta, uwani kuwa tsabar rashin tausayi ko pure water bata siya mata ba dama jirgi d'aya yakwaso su dasu Larai duk halinsu daya basada tausayi,

       
     Anasauke su a tasha, uwani tanema musu Napep, sai London Street, kai tsaye bakin gate d'in wani had'ad'en gida aka saukesu uwani tabiya mai Napep din, sanan tanufi bakin gate d'in, yayin da zainabu ke binta kamar zata fad'i tsabar yunwa 'kishin ruwa da gajiya da suka taru mata a lokaci d'aya,

      Bubbuga 'kofar uwani tayi, mai gadin gidanne yale'ko ta wata yar kusurwa ganin uwani yasa yawashe baki, a a dillaliyar dillalai, hajiya uwani ikon Allah, dan ba yau tasaba zuwa gidan ba kasancewar tana yawanzuwa sanadin wata 'kawarta yasa tasan gidan Sai dai dayake uwani akwai shishigi, sai tafi 'kawar tata ma sabawa da gidan,

    Dariya itama tayi malam audu malam audu,... Kenan.. Sukayi dariya dukan su lokacin da yake bud'emata 'kofa, jan hannun Zainabu tayi, suka shiga, nan dai suka gaisa kamar yadda suka saba,

         Cikin gidan suka nufa anan fa zainabu taga ikon Allah dan duk da kasancewarta acikin garin kano to bata ta'ba ganin gida mai kyaun wannan ba, tasandai Zadai ta gifta, amma bata ta'ba ganin cikin ba, todama da gayyarwa? Tunda komai ai dalili yakeyi,

Itadai saibin gidan da kallo take, sunshiga parlourn 'kasa ba kowa aciki Dan haka suka zauna uwani ce taita rangad'a sallama can wata yar dattijuwar mata tafito, suka gaisa da uwani zainabu ma tagaisheta, uwani ce tadubi matar tace Baba hanne, nikam ina hajiya? Ko batanan ne?

Tana nan cewar wacce aka kira da baba hanne tana sama daine mai gidan na nan, bari inkawomuku ruwa da abinci,

     Bayan sunci abinci suna zaune, saiga hajiya tasauko, a a uwani yau kece a gidan namu? dariya uwani tayi... ranki yadad'e wlh nice, Ina yini, Ina gajiya uwani ya hanya?

Lafiya qlu hajiya, munsameku lafiya? Lafiya qlu Alhmdllh,

Hajiya dama yarinyar da mukayi zancen Za akawo kwanakin baya ce nakawomiki yanzun, gatann, hajiya tamaida dubanta ga zainabu da ke raku'be, sannu yanmata, hajiya tafad'a, gaisheta zainabu tayi, ta amsa cike da fara'a, a ranta kuma tana mamakin iyayen yarinyar 'kan'kanuwar yarinya kamar wannan ce Za aturo aikatau tundaga kano har minna? Ikon Allah, tafad'a a ranta,

   To uwani,

Baba Hanne takira tace takai zainabu 'bangaren su, tanuna mata d' akin, to tace, had'i da cewa zainabu ta taso sutafi,

         Nan sukayi zancen nawa Za adinga biyanta, nan hajiya tasallami uwani kasancewar tace mata gidan 'kawarta asabe zata kwana kuma gobe asubanci zatayi,

      Sallama sukayi da hajiya tasa'ba Jakarta tana ta zuba godiya,
.......................................................

Ya sunanki? Hajiya Aisha ta tambayi zainabu dake dur'kushe a gabanta, cike da sanyin murya tace zainabu Abu.... Murmushi hajiya tayi tace.. To mu anan zamuringa kiranki da zainab, kinji? Kai tad'aga alamun taji,

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now