🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 12

1.5K 92 0
                                    

🥀🌺🥀 *FAHIMTA*.... 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed her life..._

*XINNEE SMART*

12.....'karfe 8pm jirgunsu yatashi sai gida Nigeria, Koda suka isa ba wanda yaje tarbarsu dan ba wanda yasan da zuwansu kasancewar ba wanda ya fad'a wa haka itama, a'bangarenta bata fad'a wa Kowwa ba,

     Dan haka sai taxi suka nema,
.......................................................

Mum sossai tayi farincikin ganin d'an nata, inda farincikin nata yakasa 'boyuwa, sai fara' a takeyi, Shima kansa baisan yayi kewar mahaifiyar tasa ba Saida yaganta, inda Shima farincikin sa bai 'boyu ba sai washe baki yake,

  itakam yar mulkin sai yatsina take kamar tagakashi, mum kam tunda talura da taketakenta, tad'auke kanta tai kamar batasan tanayi ba, a ranta tace nagode wa Allah tunda nasamu d'ana yazo lafiya, duk abunda zakiyi kiyi tayi ke kikasani,

mum ce ke raya hakan a ranta, yayin da take jera musu abinci,

     Bayan sunci sun'koshi ne suka nufi part d'in shi, suna zuwa yayi wankan shi yabi lafiyar gado, itama wankan tayi ta kwanta haka suka kasance ba wanda yakula wani dan haushin jarabarta ma'aruf keji had'i da fargabar Kar yakulata, tanemi lalurar,

dan a yadda yagajinnan ba abunda zaiyi mata, yayinda Rukayya kejin haushinsa dan abunda yayimata jiya..... gashi haryanzun abun nadamunta saidai kuma ba fuska, dole tashafawa kanta lafiya ta kwanta, cike da alwashin zuwa gurin boka kuma bazata bari amasa da sau'ki ba wannan karon, saidai ayi wacce Za ayi,,

    Dasafe yaje yagaida iyayensa, akan hanyarsa tazuwa dinning inda zaiyi break fast, ne suka, had'u da zainab wacce ke sauri ta tafi tahafiz saboda yau Saturday ne ba school, sanye take da riga da wando na makaranta, kalar purple dan haka sossai kalar taimata kyau kasancewarta fara, daga kitchen tafito batama lura da mutum ba 'ko'karin shige shi take yari'ko hannunta wanda hakan yatilasta mata waigowa, gabanta ne yayi wata irin fad'uwa, a razane take dubansa cike da tsoro dan itakam harga Allah tama manta shi,

      Zainab"yafad'a cikin wata kasalalliyar muryar da tasake fad'arwa zainab da gaba,

Babu gaisuwa? cike da tsoron sa tace inakwana? kintashi lafiya? lafiya qlu tafad'a cike da gundura da zancen nasa,zaisake magana takatseshi, dan Allah kasakar mun hannuna kaga kar wani yaganmu a haka,

murmushi yayi batare da yasaki hannun nata ba, cike da rashin damuwa yace saime dan anganmu, narai narai tayi da ido kamar zatayi kuka.. dan Allah kasakeni intafi zan makara kuma idan namakar bulala za aimun, ido yazaro dan kin makara shine za adake ki?

    Aikuwa duk wanda yayi gangancin dukanki wlh bazaiji da dad'i ba, matu'kar nasani,

Jan hannunta yayi suka fita, yayin da take binsa jitake uwa tasha'keshi tsabar haushinsa datakeji dan dai bataso yaga tamasa rashin kunya ne data fisge hannunta ta tafi kuma ma batason mum tasan meke tsakaninsu, so take surabu lafiya,

Abakin 'kofar fita parlour sukayi kicibis da Rukayya wacce sai lokacin ta tashi yunwa ce takorota shiyasa ta zuwa part d'in badan haka ba bata yi niyyar zuwa wani gaida masu gidan ba,

    Wani irin kallo ta watso musu musamman, hannun zainab dake cikin na Ma"aruf, zainab tuni Jikinta yafara rawa dan take taji tana tsoron matar,

     A bangaren Rukayya kam tsanar zainab ce takamata kallo d'ayan dataimata take taji muguwar tsanar yarinyar dan sam jitayi bata mata ba,ko kad'an,
   Ma"aruf kam ko kallonta baiyiba, yara'bata yawuce zainab tazo itama zata ra'ba tawuce, tafincikota ke dan ubanki ina tsaye zaki ra'beni ki wuce? Kallon ta zainab tayi batare da tace komaiba,

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now