🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 2

2K 101 0
                                    

🥀🌺🥀FAHIMTA 🥀🌺🥀

Xinnee smart

2.............Filin jirgin mallam Aminu kano jirgin da yataso daga minna Niger yasauka wanda MA"ARUF MUHAMMAD, ne direban da yatu'ko jirgin izuwa birnin na kano,

Jirgin na gama sauka, yafito bayan ya saita komai, abokinsa kabir ne ya hangosa dasauri ya'karasa yana ganinsa shima yasaki murmushi, the mr m m,dan yawanci abokansa haka suke kiransa, dariya yayi, kb kb,mota suka nufa cike da nishad'i, gidansu kb suka nufa, yayi wanka yaci abinci yayi sallah, nanfa suka soma zuba fira,

       Kb ne yadubeshi yace Mr yau Sai kwanan club ko? Ya'karasa yana dariya, tsaki Ma"aruf yayi, Kb Nika San fa bancika son yaran hausawa ba dan sam basu iya komai ba dan ba wata ma'kurar wayewa a tattare da su nikuwa kasan inason komai mai aji, ya'karasa fad'a yana mi'kewa bara ind'an kwanta,
    Yashige bedroom din Kb yai kwanciyarsa take bacci yai awon gaba da shi,

...................................................................................
Malam sahabi asalin bafulatanin sokoto ne  yawon biggali ne yakawoshi wani 'kauye a kusa da garin kano har yafara sana' ar Saida Leda, cikin ikon Allah yakoma zama a cikin garin kano kasancewar sa tun asali maraya ne shiyasa bashida wasu yan uwa duk da yanadasu sai dai tun asali basu da wani amfani hakan yasa yasabawa Kansa dayin Rayuwa shi d'aya, a haka yahad'u da Baba Larai wacce itama haifaffiyar kano ce Baba Larai macece mai tsananin kaifin harshe wanda ko mijinta bata ragawa mo'kota kuwa tsakaninta dasu saidai sannu a hanya amma ba wata kyakyawar mu'amala a tsakani,

Shekarar su 10da Malam sahabi amma ko'batan wata bata ta'bayiba, abun yadami Malam hakan yasa yafara neman aure gadan gadan, wanda duk inda yaje sai abata lamarin, wanda Larai ce take 'batawa ta hanyar yin barazana, Malam yagaji,yayita addu' a,

Wata rana yaje gurin malaminsa yace Malam ataya mu addu'a Nan yakwashe komai game da haihuwa da aure yafadamasa, cike da karaya Akan fuskarsa shidai Allah yayi shi da son haihuwa shiyasa duk yashiga damuwa,

      Malam yace nabaka mata sahabi kafara Shiri kawai cike da farinciki yace Malam.... Dakatar dashi Malam Abu yayi, karkace komai kaidai kafara Shiri daga yau,

Tunda yasamu wannan albishir d'in farinciki yacikashi, amma duk da haka baifad'awa Larai ba wanda shima baisan daliliba yadai tsinci kansa yakasa fad'amata,

Sai ranar d'aurin aure yafad'amata aikuwa kamar tayi hauka tayi masifa a ranar harta gode Allah,

Saidai bayyada zatayi domin Allah yahad'a auren sahabi da hansai, ba'kinciki daikam tashashi kamar ta had'i yi zuciya,

A haka suke zaune da hansai cinmutumcin yau daban na gobe daban, har tsawon wata shida inda d'an 'Karamin cikin hansai yafito d'an wata ukku, wayoooo ina wuta Larai tajefa hansai Kai hatta da Malam sahabin tsanar sa takeji kamar shiyabawa hansai cikin yahanata, baiwar Allah hansai kam bata damu da itaba duk cin mutumcin da zatai a gidan sam bata kulata, kocan ita ba mai hayaniya bace,

A haka Allah yasauketa lafiya tahaifi d'anta Namiji, kyakyawa kasancewar iyayensa duk fulani ne, wayoooo Larai kamar tamutu tsabar ba'kinciki da hassada, musamman yadda taga Malam sahabi nason yaron,

A haka wata 'kawarta takawomata ziyara, nan takwashe komai tafad'a mata, shawarar zuwa gun boka tabata da farko ta' ki Dan hansai akwai tsoro kamar me, daga baya da shed'an yaimata hud'ubar da tasaka ta amincewa, basu bata lokaciba suka je inda tanemi akashe hansai Malam yadaina yin komai Saida izininta a take boka ya amince, kwanabiyu hansai takwanta ciwo bata dad'eba tace ga garinku, mutuwar tagirgiza Malam sahabi kamar me yayin da Larai kamar ta takarawa tsabar farin cikin.........................................



Xinnee smart

Vote and comment

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now