🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 14

1.4K 88 2
                                    

🥀🌺🥀 *FAHIMTA*.... 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed her life_...........................

*XINNEE SMART*

14....Rukayya, direct gidansu ta tafi, tana zuwa tasamu su Maryam na shirin zuwa London, take taji tanason zuwa dan ta kwana biyu bata fita abroad ba, acewarta,

Nan suka shiga Shiri, sati na zagayowa Suka tafi, dan haka Koda Ma"aruf yaje gidansu saita'ki fitowa haka yaringa zarya, har yasamu labarin bama ta 'kasar, sossai hankalinshi yatashi ransa ya'baci,

Mum kam ci kanka bata cemasa ba saima idanu datasa masa, tunbai fahimci mum fishi take dashi ba har ya FAHIMTA,

Anyi sa'a yaje yabata ha'kuri, inda bata 'bata lokaci ba tadubeshi,

Ma"aruf!

Na"am mum, kasan me nakeso dakai? Girgiza kai yayi kamar wani yaro alamun baisani ba, to yanzun zan sanar dakai, aure nakeso kasake yi, cike da razana da kalamanta yace haba mum aure fa? Yanzun fa dudu du auren kwana nawa Zaki ce kuma inyi wani?

To shikenan tunda ban isaba tashi kaje, tafad'a Fuskarta na nuna fusata, Allah ya huci zuciyar ki mum ba haka nake nufi ba,mekake nufi to inba haka ba,? Ma"aruf wlh ka kiyayeni kasani ni mahaifiyar kace, yakamata kadinga tuna wannan,

ha'kuri yashiga bata sossai sannan tasauko,

Mum to ba Wai auren ba banida yarinyar da nakeso, wannan kuma kabarshi a hannuna ni zan nema maka matar..... Again mum!

Haba kibari mana insamu za'bina, Rukayya kece kika nema mun please mum once nima kibari insamu wacce nakeso sai inyi auren.... Mtss maganarka batada wani amfani abunda zan sanar maka kawai kafara Shiri wannan umarni ne a matsayina na mahaifiyarka kuma bance kasanar da Kowwa ba Koda kuwa matarka ce..... tana gama fad'in haka ta tashi ta tafi,

hankalin Ma"aruf, ne yatashi ganin mum, tanason tawargaza masa shirinsa, lallai akwai matsala to ko fitowa zaiyyi yace mata yanada wacce yake so? to ai shikuma a ganinsa zainab bata isa aure ba,

A Yan kwanakin har fad'awa yayi tsabar tunanin dayasa wa zuciyarsa, daga 'karshe dai ya yanke cewa zai bari bayan mum tayimasa auren, lokacin zainab takammala karatun ta sai yafito da Maganar a haka yabarwa zuciyarsa zancen,
.......................................................
Mum ce zaune a bakin gadon zainab, yayinda zainab, d'in ke zaune a'kasa, kusa da 'kafar mum,

Sunanta mum takira,
d'agowa zainab tayi tadubeta had'i da amsawa, yayin da'kirjinta ke bugawa, hakannan batasan mai yasa mum tace tanaso zasuyi magana ba, koma dai manene tasan Maganar dole tana da muhimmanci tunda har mum tasameta har d'aki,... Maganar mum ce takatseta......

Zainab, alfarma nake nema a gurin ki, kuma nasan insha'Allah zakiyi mun, musamman idan naduba yawan biyayyarki a gareni to nasan tabbas bazaki bani kunya ba, sai dai kuma banaso ya kasance Zaki amince ne saboda kisakamun ri'kon da nai miki, ko d'aya.. So nake ki amince da kanki saboda bazan aiwatar babu yardar ki ba,
Inafata kin Fahim ce ni?

Cike da fargaba zainab tadaga kai had'i dacewa, insha'Allah mum Zaki sameni mai biyayya a gareki,kinji fad'a mun komai kike so nikuma yanzun in aiwatar da izinin Allah,

Shiru mum tayi bayan ta jinjina kai, zainab so nake ki amince ki auri d'ana Ma"aruf,....

Cike da razana tace mum shine yace yana son aure na?

girgiza kai tayi, ko d'aya, nice dai nake nema masa macce ta gari wacce tadace da rayuwarsa, bawai ballagaza irin Rukayya ba, Allah yasani ina nadamar had'a auren Ma"aruf da Rukayya dan sam bata dace dashi ba, bata da tarbiyar zama uwar yayansa, narasa mai yasa amincin da ke tsakanina da hajiya Bilkisu, yarufe min ido har nakasa ganin rashin dacewar aurensu, mtss hmm ta'karasa fad'a cike da jin ciwo a ranta,

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now