🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺Part8

1.5K 102 0
                                    

🥀🌺🥀 *FAHIMTA...* 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed her_ _life_

*This page is for you my friend* *Asma'u Adili domin jin* *dad'in* 😍😘😍

*XINNEE SMART*

8.... Shiru yayi bayan sungama waya da mum wacce tabashi umarnin lallai yau koman dare yataho gida hankalinsa ne yatashi yayin da damuwa taimasa illa,

       Kb ne yashigo had'i da masa sallama a kasalance Ma'aruf ya amsa, dubansa kb yayi, kayi ha'kuri nasan insha'Allah wannan son dana gani a idonka bazai tafi a banza ba, nayi maka al'kawarin binciken duk inda take,

murmushin ya'ke yayi nagode kb, yakamata intafi yanzun domin mum tayi fushi kuma tace lallai intafi yau,

      Dan haka inaga ni zantafi please kb kasake zuwa ka bincikar min, kuma nima bazan jimaba zandawo,... Nan kb yaimasa al'kawarin binciken duk inda zainab take,

  'karfe goma shabiyu ya isa garin minna danhaka koda yaje gidan shiru kowwa yakwanta, kai tsaye sashensa yanufa, wanka yayi yakwanta zuciyarsa cike da damuwar rashin ganin zainab, picx d'inta yabud'e a phone dinsa yana kallo...... Mai yasa baki jirani ba zainaba ta,?

dana san idan nadawo bazan sameki ba da bantafi ba dana jira harzuwa lokacin da zaki warke aimana aure, inason ki zainaba ta, I'm madly in love with you, surutansa yake had'i da shafa Fuskarta a jikin phone din,...... Haka yakwana yanafaman mafarkanta yayin da sonta ke dad'a hudashi,

Washegari a makare yatashi  dayake yasake kwanciya bayan yayi sallah  dan haka a gurguje yayi wanka, yashiga cikin gidan su, sallama yayi yashiga ba kowwa a parlour sai Baba Hanne dake goge dining d'in da akagama break fast,

     Jin sallamarsa yasakata waigawa, a a maigidana sannu da zuwa, murmushi yayi yace amaryas ykk lafiya?

Lafiya Lau Alhmdllh, ya aikin Naka?  Alhmdllh,
Nan suka gaisa sossai dan sunsaba da Ma'aruf sossai danshi sam bashi da girmankai ko wula'kanci,

      Baba ina mum, hajiya tana Saman Alhaji, OK ya fad'a had'i da nufar upstairs d'in,

Sallama yayi a parlourn mahaifinsa,iyayen nasa ne suka amsa cike da farincikin ganin d'an nasu,zama yayi y agaishesu cike ladabi wanda wannan kesa suke dad'a 'kaunar d'an nasu, amsawa sukayi yayinda suke tambayarsa aikinsa cike da kulawa, amsawa yayi,

nan d' akin yayi shiru, mum ce tayi 'karfun halin cewa Baba.....d'ago kai yayi yadubeta yayin da gabansa ke tsananta fad'uwa, fuskar mum d'in ya kalla yaga alamar ba wasa nan yasakejin gabansa na sake fad'uwa,

      Baba kayarda cewa mu iyayenkane? cike da mamakin maganarta yace banganeba mum, kaban amsata, ba tambaya ba,

Eh"

to tunda kayarda damu iyayenkane to kasandai bazamu za'bama ka abunda zaicuceka ba, munyanke shawarar aura maka Rukayya a matsayinmu na iyayenka tunda tafara magana gabansa ke fad'uwa amma dayaji abunda tafad'a sai yaji har wani zazza'bi zazza"bine yakamashi, take yafara magana, haba mum banace kibari tukuna indawo ba Sai muyi Maganar? Yafada kamar zaiyi kuka, a gskiya mum idan akace saina auri Rukayya ba aimun adalci ba dan sam banasonta, Kuma ma mum...

Baba ya isheka, mum takatse shi cike da fushi,

kuma wlh sai ka auri Rukayya waton dan kaga ina lalla'bakane shiyasa kake son 'batamun rai to baka isaba kaji dan ni nahaifeka bakai ka haifeni ba.. Tana gama fad'in haka ta fita... Gurin Dad yajuya, Dad please.. Wlh ni banason Rukayya dan batada tarbiya sam, numfashi Dad yaja to a gaskiya babana mum din ku nada gaskiya idan ba haka akai maka ba bazakayi auren ba naga alama, saidai zancen rashin so da kake magana idan bakasonta to kanada wacce kake so ne? Shiru yayi yana tunanin yafad'a masa yana da wacce yakeso kokuwa? To amma ai dole yanemi Jin wacece kuma? Mai zaice masa?

       Muryar Dad dayaji ne yasa shi dawowa daga tunanin dayake, nace kanada wacce kake so ne? Dad yasake maimaita masa tambayar a Karo na biyu...... Eh.... gaskiya a a, yasamu kansa dacewa cike da daburcewa,

Numfashi Dad yaja yace Baba kayi ha'kuri kawai ayi auren nan, wata rana zaka fara sonta ne, kaji,?

       Never, yafad'a bazan ta'ba son Wata ba nariga da nasoma son wacce nake so kuma bazan sauya ba,.... Ya fad'a a zuciyarsa,

ganin ba wata mafita kawai yafita ransa na tsananin 'Kuna, shikam dai zainab ce taimasa kuma itace za'bin sa, sossai yakejin son yarinyar na dad'a huda shi, tabar da yadad'e baisha ba ce tafad'o masa a rai, take yashiga nemanta a d'akin, aikuwa cikin sa' a yasamu a bedside drower dinsa, nan yashiga ja yayin da damuwarsa ke dad'a ruruwa tsananin sonta ne ke dad'a hudashi,

..... Zainab..... Zainab, mum ce ke Kiran zainab wacce ke kwance a d'aki duk jinta take tamkar mara lafiya,Sam yau takasa gane kanta,

      Kiran mum ne yadawo da ita daga tunanin meke damunta da take, dasauri ta nufi kitchen inda taji Muryar mum din nasake kiranta,

Mum gani tafad'a bayan ta isa inda mum din take, Baby mai kikeyi haka nake ta kiranki baki ji ba?

            Mum bakomai bandai ji bane yi ha'kuri mum..... Oh.... no u don't have to apologize,

Dama abinci Zaki kaiwa brother dinki dan yadawo jiya daganan sai ku gaisa, gabanta ne yafad'i badai d'an rainin hankalinnan zata kaiwa abinci ba tab.... Saidai kuma ba yadda zatayi dole taje dan bazata iyayiwa mum musu ba, a sanyaye tad'au basket dinda food flaks din keciki,a sanyaye tanufi part dinda akace nasane,

        Sallama tayi a 'kofar shiga parlourn shiru taji ba a amsa ba dan haka tabud'e labulen, dan'kofar a bud'e take, yana kishingid'e akan three seter, hannunsa ri'ke da tabarsa yana zu'ka yayin da daya hannunsan ke ri'ke da cup din lemon champagne, ga kuma bottle d'in a gabansa,

       Gaban zainab ne yayi mummunar fad'uwa cike da tsoro, tace.. a a abincin ka ne akace inkawo mak.......a....jikinta sai rawa yakeyi, dan tunda take ita bata ta'ba ganin giya a fili ba gwara ma taba tasha ganin mutane na shanta amma giya 'kiri' kiri haka..........dan a ganinta kwalbar champagne din da tagani giya ce,

      Shikuwa tunda tashigo yagama sandare wa a gurin dan tabbas yau kam ba gizo take masa ba..... cikin 'karfin hali ya isa gareta, batare da yace komai ba yatsura wa fuskarta ido tabbas itace....... Zainab kam tuni tsoro yarufeta dan tunda take bata taba tsayawa da namiji irin haka ba..... Zaunawa yayi a gabanta had'i da lankwash 'kafafunsa yad' aura duka hannayensa a Kan kuma tunsa, murmushi kawai yake batare da ya lura da halin da zainab d'in take ciki ba,

     Hannunsa yasa zai zaunar da ita, da gudu tafita tabar d'akin,

Direct d'akin ta tawuce, Kan gado tafad'a tana haki, a zabure kuma tami'ke wardrobe din kayanta tanufa, 'kullin kayan da tazo dasu gidan wanda mum tahanata sakawa ta janyo, warwareshi tashiga yi, nan taciro rigar pillown da tad' auko daga asibiti, shin shinawa tayi tabbas babu banbanci Dan still har yanzun 'kamshin na nan daram, kuka tafara....... Wayoo bawan Allah ina zanganka ingode maka, inyimaka kyautar da bazaka manta ba?

       Insha"Allah wannan ba Bawan Allah na bane mai kirki mai mutumci, tayama wannan mashayin zaizama bawan Allah na, kawai dai'kamshin ne daya,

      Wlh bansanka ba Bawan Allah amma insonka zuciyata batasan so ba dan bata ta'ba yiba amma tun lokacin da kataimakeni nkejin 'kaunarka nakejin sonka kamar bazan rayu baka ba'kamshin ka kawai zafafa wutar sonka yake a zuciyata bare kuma ganinka duk ranar dana ganka zan soka zan 'kaunace ka har sai kace ya isa....... ta' karasa zancen tana murmushi ita d'aya..........

Tundaga ranar zainab take avoiding d'insa har aka fara shirin biki yayin da yarasa natsuwar hankalinsa Sam duk yadda yaso haduwa da yarinyar tadauke masa wuta mum kuma yanason tambayarta ita yana Jin shakka,

Saidai yau yayi al'kawarin ganinta ko ta halin Yaya, dan haka yatashi yanufi d'akinta.......










_Xinnee smart_

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now