🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 19

1.6K 92 0
                                    

🥀🌺🥀 *FAHIMTA*.... 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed her life......_

   *XINNEE SMART*

~In life nothing will surprise me~ ~any more~ 🤷🏻‍♀

*19* Rukayya, kam agurinta duniya sabuwa dan sossai take she'ke ayarta yadda takeso, a 'bangaren auren Ma"aruf, a cewarta sai ta more kafun takoma gidansa, ko bakomai lokacin, ya gyaru dan so take ya San mahimmancin ta,

   Dan haka ma takashe wayoyinta, daga London, California tabi wani saurayinta, suka wuce, dan haka nema mahaifiyarta batasamun ta dan duk wayoyinta datake amfani dasu layukan waje ne kuma bamai number gashi ita ba wanda takira,

A kwance take kan gado tayi d'ai d'ai da ita sai faman ajiyar numfashi take, dan yauma kamar ko yaushe, bokan nata yazo yagama wujijjigata,

   Saida tad'auki tsawon lokaci tana maida numfashi kafun tami'ke, tashiga bathroom, tayi wanka, normal wankan soso da sabulu, tafito, shiryawa tayi, tazauna wayar ta tad'auko Kai tsaye layin Ma"aruf, na Thailand ta kira, yayi ringing har yagaji ba'adauka ba, ranta ne ya'baci amma bata karayaba tasake kira yana fara ringing cikin sa'a yad'auka sallama yayi, kasa amsawa tayi dan tarasa mai zatace amma dayake batada kunya saitace hello"Ma"aruf, Rukayya ce..... shine tunda natafi ko kanemeni? katse ta yayi tahanyar yin tsaki batare dayace komai ba yayi hanging, shiru tayi tana kallon wayar cikin 'bacin ran katse mata waya da yayi, kawai sai tasake Kira aikuwa tana soma ringing aka katse, busy tagani, aikuwa ranta ya'baci kamar me, take tahau mita,

Tabd'i jam! lallai ma, Ma"aruf, Anya yanacikin hankalinsa kuwa,? lallai nayi sake, aikuwa yazamar mun dole inyi gaggawar komawa, dan bazai yu ba, cikin sauri tafita, shirin tafiya tashiga yi gadan gadan,
 

Yakama yau alhamis "dan haka yau jirginsu Rukayya yalula, zuwa gida Nigeria'  'karfe 8:45jirginsu yasauka, a filin jirgin Aminu kano, dake kanon Dabo,  taxi tad'auka zuwa, hotel, d'aki takama a hotel din,

          Gari nawaye wa, tai Airport, sai Niger state,

Kai tsaye gidan iyayenta tanufa dan sotake taji ko tunda ta tafi Ma"aruf yazo ko bai zo ba?
.......................................................

Rukayya, wannan wani irin shashanci ne? har yaushe zakiyi tafiya, kikasa Kiran Kowwa a gidanku, har Yan uwanki dakuka tafi tare sudawo ke baki dawoba? Uhmm saboda Allah fa?
Tunda mahaifiyarta tafara mata magana komai batace ba, sai faman zun'bura baki take tana guna guni,
   Au ina magana kina wani turo baki gaba ko?
to dan Allah Aunty (kasancewar haka suke Kiran mahaifiyar su) ni mai kikeso ince? Daga dawowa ta kinsakani agaba kinata mun fad'a... Au haka ma zaki ce, to ai shikenan, nayi shiru...., 

toto.... tooo.... nidai kiyi ha'kuri, dama sonake inji ko danatafi Ma"aruf yazo? Kallonta uwar take cike dajin haushin yadda Sam bata ganin girmanta, Koda dai laifin nasu ne itada mahaifinsu sun sagarta yayansu sossai, shiyasa basu da wata tarbiyya,

     Kinji?

maganarta tadawo da ita daga tunanin datake,

Shiru uwar tayi tana nazarin tafad'a matane kokuwa?

Sallamar yayarta Maryam ce tasa dukansu duban 'kofa, kuka take uwa wacce uwarta ta mutu,

     Take hankalinsu yatashi ganin halin datake ciki, lafiya mahaifiyarta ta tambaya, batace komai ba sai kuka datakecigaba dayi, da'kyar dai tasaurara da kukan, cikin sheshe'ka da tashin hankali, tace....

Aunty Umar, yacuce ni, yasake ni..... ta'karasa fad'a da kuka, saki?
Suka had'a baki gun tambaya, Rukayya tace.... Amma dai Umar yacika butulu, duk abunda daddy yaimasa ashe zai iya sakin ki? Ko dayake namiji ne, amma yanaga fuskarki da shacin hannu,
Cikin kuka tace Saida yadakeni kafun yasakeni,.....

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now