🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 5

3K 124 3
                                    

🥀🌺🥀 *FAHIMTA* .... 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed_ her _life....._

*XINNEE SMART*

5..........MA'ARUF MUHAMMAD, shine cikakken sunansa mahaifinsa Alhaji Muhammad haifaffen garin katsina ne,

Alhaji Muhammad yanada yan uwa da suke uba d'aya kasancewar shi d'aya mahaifiyarsa ta haifa, har tabar duniya, sauran yan uwansa duk mata ne kuma yayinsa ukku sai kuma 'kannensa biyu, duk mata, wanda a yanzun duk sunyi aure kuma suna zumunci sossai kasancewar lokacin da mahaifinsu usmanu yana raye ya koyardasu kula da juna dakuma Jin' Kan juna, dan haka kobayan da ba ransa basu yar ba, Allah yayiwa Alhaji Muhammad dukiya mai tarin yawa, kasancewar sa d'an kasuwa, domin 'bangaren business, yakaranta, sai Allah ytaimakeshi kasancewar sa mai kiyaye dokokin Allah da bada zakka aduk lokacin da yakamata, a yawon kasuwancinsa ne yahad'u da hajiya Aisha a garin Sudan wacce takasance basudaniya ce, inda suka' kula soyayya har magana tayi nisa inda ba'adau lokaci ba aka d'aura musu aure yataho da ita Nigeria kasancewar Alhaji Muhammad yana yawan kasuwanci a jahar Niger kuma amininsa d'an can ne yasa yake sha'awar zama a garin dan sossai garin yai masa inda bai 'bata lokaci ba yasamu fili yad'an d' asa gidansa a London street, tunda yagama gininsa yakoma can da iyalansa dan tsakaninsu da Bauchi sai ziyara ko lokacin bikin sallah dan acan yakeyi yin sallah duk shekara tsakaninsa da yan uwansa kuwa kullum yana cikin kyautata musu,

Shekarar su biyu da aure Allah ya azurta su da samun d'a namiji kyakyawa suka d'auki son duniya suka d'ora masa, ranar suna yasanya masa sunan mahaifinsa wato MA'ARUF, inda suka maidashi Baba, kowwa a family haka yake kiransa, inda yana shekaru, goma aduniya Allah yasake azurta su da wata yar inda aka samata sunan mahaifiyar mommyn su, wato Amina suke kiranta Nina,

MA'ARUF tunda yatashi sangarta ce ne Sam shi bayason yane ma abu ace babu to ranar za'a yi rigima dashi kuwa, so tari yafi Shiri da Daddyn sa dan acewarsa yafi son shi,

A garin minna yayi primary yayi secondary school d'insa, yana gamawa daddy yanema masa admition a US Oxford University, inda yakaranta mass com, saidai me yana gamawa yace bai san zancen wani aiki ba, kuma ma shi wata makarantar zai shiga, mommy ce taso hanashi amma yakafe ga Daddy kuma yad'aure masa gindi dan haka ba yadda ta iya dole tazuba musu ido, take akayi masa komai nashiga makarantar koyon tu'kin jirgi a Thailand, acan nefa ya'karasa lalacewa dan dama a US Sam basaji yan gang d'insu ga karatu ga rashin ji sune club sune neman mata, sam ya'bata tarbiyar iyayensa a Thailand kam abun ba acewa komai dan acan ne ya iya shan taba, saidai bayan taba baya shan komai, amma duk da wayannan 'kazaman halayyar tasa hakan bai hanashi ri' ke addininsa ba dankuwa sallah kowacce a lokacin ta yake dan yayi karatun islamiyya kafun barinsa 'kasar, har kuma lokacin idan yazo Nigeria hutu to akwai malamin dake masa littafai da hadda,

Tunda ya' kare karatunsa na koyon tu'ki, wani kamfani suka d'aukeshi aiki a 'kasar inda nanma da' kyar iyayensa suka amince,

Tunda yafara aiki mommy kullum cikin binsa yayi aure take amma abun yaci tura, dan shi sam aure baya gabansa acewarsa har yanzun ba wacce taimasa.......... To yanzun dai da alama Anka........ 🤭🤣Yanmata nasonsa saidaishi tsakaninsa dasu hutawa ce kawai ba zancen soyayya, sam a tare dashi, a danginsu ma haka abun yake dayawa yanmatan family su suna 'ko' Karin Kai masa hari amma shi basa gabansa Sam,

Rukayya da mom keson ya aura yar wata 'kawarta ce hajiya sa' a, yarinyar tadad'e tana tallan kanta a gareshi ya'ki saurararta dan acewarsa sam bata da kamun Kai dan rawar kanta yayi yawa,........................

_Cigaban labari_

Kb yanakomawa gida yayi wanka yayi breakfast, sanan yafita bai zame ko inaba sai wani boutique dogayen riguna yasiya mata guda hud'u da takalma Plat guda biyu sai brush da toothpaste lotion da turare, yabiya wani restaurant yayi mata take away d'in chips da farfesun 'Koda wanda yaji had'i, provision store yaje yasiya mata kayan tea, sanan yanufi asibitin da Kaya ni' ki ni'ki kai tsaye d'akin yaje a zaune yasameta tayi tagumi da alama ta Lula duniyar tunani ne,

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now