BABI NA UKU

91 4 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BAYA DA K'URA...

Daga alk'alamin Sophie galadanchi.

3
Sati d'aya da kammala registration d'inta ta soma shirin zuwa makaranta wata ranar litinin Nuwaila ta zuba mata ido tana kallon hauka zalla a zuciyarta tace,"to me wannan yarinyar zata je yi makaranta yau?".

Azzah kuwa riga tasa doguwa ta wani yadi mai laushi ja da karamin gyale bak'i,rigar abud'e take tundaga sama har k'asa tasa skirt bak'i aciki da riga k'arama bak'a tasa red lipstick da powder sai kwalli.

Nuwaila ta kalleta tace,"ni kuwa yarinyar nan zanso naji me zaki je yi makaranta yanzu bayan ko time table ba'a kafe ba".

Jikin bags hanger d'inta taje ta janyo wata k'aramar jaka mai dogon hannu ta sa wayarta aciki sannan ta samu damar amsa Nuwaila,"nayi k'ok'ari ma yau da kika ganni zanje MTN office na siya Sim card nayi register daga nan zan wuce makaranta saboda ina so nasan yanayinta da kyau zan je kuma naga kalar abincin da suke siyarwa idan bazan iya ci ba to zan san me zanyi tunda wuri".

"Sim card a wayarki?,waye ya baki dama", Nuwaila ta tambayeta tana zare idanu.

Tab'e baki tayi tasa k'aramin hanky bayan ta dauko takalmi daga sheo rack d'inta tana gogesu sannan tayi magana,"jami'a ce ta bani dama mana Dady ya tura ni makaranta dole yasan zan saka sim a wayata".

"Kafin nan yakamata kiyi informing dinsa akan siyan sim card din da zaki yi",Nuwaila ta fad'a tana yafa mayafin data d'auko daga wardrobe d'inta.

"Dole zan fad'a masa amma bayan na siya, yawwa zaki bani dubu biyar kafin Dady ya turomin kud'ina".ta kai k'arshen zancen tana washe k'ananan hak'oranta.

"Sai kije wurin Gaddafi dubu uku suka rage min zan sa mai kuma zanci abinci dan bazan dawo ba sai yamma",daga haka tasa takalminta tana shirin barin d'akin.

"O'o yayata kalleni fa AZZAH SUNUSI MAIKANO gudar k'anwarki,ke yanzu ba abin bugun k'irjinki bane ace nice k'anwarki,ko abinda ya faru lokacin da nake registration ya isa yasa kisani a k'asan zuciyarki yadda na siya miki girma a wurin y'an department d'inku",tana jujjuya jikinta yadda Nuwaila zata kalleta dakyau,"ki taimakeni da dubu daya nasa mai wallahi motar fa a reserve take jacking ma take Allah".

Dariya Nuwaila tayi tukunna ta jefa mata dubu d'aya sannan tayi gaba.

Azzah na k'ok'arin shiga inda momynsu Nuwaila ta fito take fad'a mata,"ashe jiya momy jikinta baiyi dad'i ba mama Dije tace bata jima da samun bacci ba ki tafi kawai karki tasheta".

"Allah sarki momy Allah ya baki lafiya ya tashi kafad'unki acikin iyalinki,inama ace Dady yana zama nasan zaki fi samun kulawa, amma dukda haka mama Dije na k'ok'ari Allah ya biyata itama", Azzah ta fad'a tana goge d'an guntun hawayen da ya zubo mata.

Ameen Nuwaila ta amsa tukunna suka fita.

"Sama'ila!", Azzah ta kira mai gadinsu ya fito da sauri.

"Ka tabbatar motar nan ta wanku in and out?",ta fad'a tana yamutsa fuska.

"Sosai ma auta ga Alhaji da hajiya".

"Ok to saita min ita da gate sannan ka bud'e mana gate d'in da sauri lokaci na tafiya".

Jikinsa na rawa yayi yadda tace, har ya rufe gate d'in bayan fitar su yana d'aga musu hannu yana washe baki kamar wanda akayiwa bushara da gidan aljanna.

BAYA DA K'URAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant