BABI NA TAKWAS

73 2 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

8
A yanzu babu wani shiri tsakanin Azzah da Nuwaila, tun daga ranar da Azzah ta fad'awa Nuwaila maganganu marasa dad'i.

A hankali ta fara tattara kayanta tana barin d'akin dan a ranar bata kwana d'akinsu ba, washe gari ma ba'a d'akin ta yi wanka ba.

Azzah na kwance kan gadonta Nuwaila ta yi sallama ta shiga d'akin ba tare da ta yadda sun had'a ido da Azzah ba.

Wardrobe d'inta ta bud'e ta d'auko kayanta ak'alla zasu kai kala goma ta fita daga d'akin bayan mintuna biyar ta dawo toilet ta shiga ta d'auko brush d'inta da sauran kayanta dake band'akin.

Azzah ta bita da kallo baki a sake, jikinta yayi matuk'ar sanyi.

A zuciyarta take magana bayan fitar Nuwaila daga d'akin.
"Nuwaila gaba take da ni saboda d'an wannan maganar da na yi mata? To ai Gaddafi ya rama mata".

Tsaki ta yi a fili wani b'angaren na zuciyarta yace, "k'yale ta kawai zata dawo, fushi ne na d'an lokaci".

Dama idan anji muryar Nuwaila to ita da Azzah ne suke rigimar da suka saba ko kuma hira suke, wannan karon Nuwaila ta zama shiru sosai.

Babu wanda ya lura da Nuwaila ta bar d'akinsu d'akin dake kusa da na Gaddafi ta koma.

Da d'ad'd'aya Nuwaila ta kwashe kayanta daga d'akin sai da ya zamana babu komai nata a d'akin sai wanda ta mance da shi kawai.

Soyayya ta jini da jiki ta shiga tsakanin Hisham da Azzah.

A yau Hisham ya fad'a mata yana nan zuwa gidansu, tunani Azzah ta shiga yi ya zata yi da Hisham, sau biyu ya tab'a zuwa gidansu amma wannan karon da zai zo sai taji ta diririce bata san dalili ba.

Har ranar da zai zo ta kasa sanarwa kowa da zuwan Hisham.

Wanka ta yi tasa riga da skirt na atamfa ja, ko hoda bata shafa ba haka kawai ta ji bata murnar zuwansa yau.

Shabiyu na rana ya kirata cewa ya iso ga shinan a unguwar su ta fito ta shiga dashi.

Bayan ta amsa masa ta nufi kitchen wurin Mama Dije.

Shiru ta yi tana wasa da zuben hannunta.

"Lafiya dai autar momy?" Mama Dije ta tambaye ta.

"Hisham ne ya zo yau daga Kaduna" ta fad'a tana murmushi.

"Wannan sakacin naki yana bani mamaki Azzah, yanzu ya kike so ayi?".

Shiru ta yi dan bata san mai za ta ce ba kuma.

"Tuwo muka yi yau na shinkafa da miyar alayyahu da agushi idan zai iya ci ko ki dafa masa indomie" Mama Dije ta fad'a tana rufe freezer.

Zaro Ido Azzah ta yi ta ce,"zai ma ci tuwon bazan iya dafa indomie ba bana jin dad'i yau".

Allah ya sauwak'e ki je ki shigo dashi.

"Sama'ila!"

Daga bayanta ya fito yana washe baki.

"Gani nan autar hajiya".

"Ka bud'e gate zan yi bak'o".

Tana gama fad'ar haka ta bud'e k'aramar k'ofar ta fita.

Daga nesa ya hangota, tada motar ya yi ya fara tafiya, tana ganin motar ta gane sai kawai ta juya zata koma cikin gida.

Gidan ya shiga ganin gate a bud'e, ya jinjina girma da kyau na gidan tun daga waje, ga motoci masu kyau da tsada.

K'arasowa ta yi shi kuma ya bud'e motar ya fito.

"Kai baby ka yi kyau sosai kamar a gudu da kai".

Murmushi ya yi ya ce, "Nagode, tare da babban yaya nazo fa", ya fad'a yana nuna mata motar.

Kunya taji tana murmushi tace, "to ku zo mu shiga cikin gidan".

Gaba ta yi suna binta a baya.

Mama Dije ta shirya abincin akan teburin dake tsakiyar palon mai d'an fad'i sauri kawai take kar su zo su same ta.

Sallamar su ya yi dai-dai da shigewarta korido d'in da d'akin momy yake.

Zama suka yi har ita ta gaida su sannan ta gabatar musu da abinci.

Nuwaila ce ta fito daga d'akinta doguwar rigar bacci ce a jikinta mai kauri da hula fara sai da ta zo tsakiyar palon sannan ta lura da mutane a wurin.

Ganin Azzah a zaune ta tabbatar bak'inta ne a take ta d'aure fuska ta ce, "Ina wuni" kawai bata jira sun amsa ba ta yi gaba.

Binta da kallo suka yi, Hisham na mata kallon meyasa zata yi haka bayan suna gaisawa a waya tana da fara'a, yayansa kuma yana mata kallon Wannan black beauty d'in fa.

Ta shi Azzah ta yi ta koma d'akinta dan kamar ba zasu iya cin abincin a gabanta ba.

Koda ta dawo sun gama, Hisham ya kalleta ya ce, "idan da hali zamu gaishe da momy".

Shiru ta d'an yi sannan ta ce "barin duba idan ba bacci take ba".

Babu dad'ewa ta dawo zata musu iso d'akin momyn.

Nuwaila na shirin fita suka sako kai d'akin dan haka ta koma ta zauna badan ta so ba.

Har k'asa suka durk'usa suna gaisheta murmushi kawai take tana lumshe ido, ta k'urawa Hisham ido har sai da ya tsargu.

Sallama suka mata suka fita, amma yayan Hisham har waiwayen Nuwaila yake tana danna waya ta tsare gida fuskar nan babu alamar annuri.

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now