BABI NA GOMA SHA UKU

67 4 0
                                    


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

13

"Dama akan wannan mai samfurin y'an China ne kake wulakanta soyayya ta".

Kansa ya d'aga yana kallonta sai kuma ya yi murmushi ya ce.

"Na barta a hannunki eesha, ki tabbatar ta ci abinci idan kina sona da gaske to ki taya ni son matata".

Yana gama fad'ar haka ya fita.

Dogon tsaki ta yi sannan ta koma d'akin. Sallah ta samu Azzah na yi dan haka ta zauna gefen gado tana danna wayarta.

"Anty ki taimaka ki bani abinci tunfa da kuka d'auko ni baku bani abinci ba".

Kallonta eesha ta yi tana murmushi ta ce, "Kar ki damu barin karb'o miki, idan zaki wanka ga sabon kaya nan ki chanza akwai kayan bacci ma a ciki inji mijinki".

Baki Azzah ta sake tana kallonta har ta fita.

"Hmm wallahi sai Hisham ya yi dana sanin sato ni". Abinda Azzah ta fad'a kenan, abincin da eesha ta kawo mata ta tsakura kad'an saboda ta kasa ci sai tunanin gida take har bacci ya sace ta.

Wasa-wasa an kwana uku babu wani labari akan Azzah, hankalin y'an gidan ya yi matuk'ar tashi.

Tun suna kuka har hawayen ya k'afe, babu Wanda zasu kaiwa kukansu.

Tun ranar da aka kawo ta gidan da Hisham ya shigo sai yau ya sake dawowa bayan kwana hud'u kenan, bai tab'a tunanin akwai wani abu ajikin Azzah da zai iya ramewa ba sai yau, ta rame ta k'ara haske.

Da sallama ya shiga d'akin ya sameta a kwance kan gado, bata amsa ba ta zuba masa idanuwanta da suka kod'e saboda kuka kwana biyu.

"Ki yi hak'uri ba'a son raina na raba ki da su momy ba Azzah kawai ya zama dole ne saboda ya kamata hakan ya faru".

Juya masa baya ta yi saboda ko ganin fuskarsa bata son yi.

"Ranar Monday an fara lectures ka d'auko ni, yaushe zaka maida ni gida karka lalata min karatuna", tana kuka take maganar.

Ba zai juri kukanta ba dan haka ya mik'e ya bar d'akin, jin fitar sa yasa kukanta k'aruwa.

Dirar bazata Dady ya yi wannan karon, ba Wanda ya san da zuwan sa amma abin mamaki babu kowa a gidan har Sama'ila.

Dama fad'uwar gaba ta dame shi yau, duk gidan har d'akin mama dije ba inda bai sa kafarsa ba, a gigice ya fito ya ci karo da Gaddafi ya dawo daga aikin dare da ya yi. 

"Kai Gaddafi ina mutanen gidan babu kowa aciki".

Gaddafi daya k'araso da sauri yana mamakin ganin Dady  ya ce. "Dady na barsu duka a gida jiya yanzu na dawo daga wurin aiki".

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" abinda Dady ke ta maimaitawa kenan.

Eesha ta shigo d'akin da Azzah take ta sameta zaune tana kuka.

"Daddy's girl tashi za'a maidake gida wurin Dadynki".

Da sauri Azzah ta mik'e ta fito daga d'akin ko mayafi bata nema ba, a wajen gidan ta samu su Hisham, Jamal, Wanda ya sato ta daga kano da wata babbar mata da wani Alhaji duk a waje n gidan, ga motar ta a gefe ta sha wanki sosai, lek'a motar ta yi ta hango wayarta da jakarta da mayafinta, sanda suka k'araso ta gaisheda mutanen dake wurin sannan tace.

"Hisham na shirya, ka maida ni gida, su momy hankalinsu ya tashi nasan suna can suna kuka".

Mota suka shiga,kusan mota uku suka kama hanya, suna tafiya har suka shiga kano murmushi ta yi.

Gani ta yi basu bi hanyar gidansu ba, abu kamar wasa taga sun tsaya wani wurin sun karb'i abu suka kuma d'aukar hanya, tafiya ta yi ta fiya sai gasu a sokoto.

Vote me on wattpad at safiyyahgaladanchi.

Kuyi hak'uri da wannan idan Allah ya kaimu gobe na samu lokaci zan k'ara wani page d'in.

School things...

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now