BABI NA GOMA SHA TARA

223 16 1
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

19

Shiru tayi tana kallonsa ya juyar da kansa gefe daya yana magana da momy.

Juyawa tayi tana amsa sallamar sama'ila da yake miko mata kayan gugarsu.

"ila inkai wannan kayan ina? Je can ka ajiye su kan kujera".

Kallonta su mommy sukayi harta k'araso kusa dasu ta zauna, gaishesu tayi Momy ta amsa hisham kuma ya kura mata ido.

"Azzah da zancen wani akanki na aure kike kula samari?"

"wasu irin samari kuma momy? Mutum daya ne ya kirani agabansa kuma wannan yaron ba amsa wayarsa nake ba tun bayan da mama ta yadda da aurenmu dashi".

"kinfi kowa baki ne da kike min wannan rattaben? Meye amfanin rashin daga wayar tasa tunda bai sa yadaina kiranki ba?"

Shiru azzah tayi tana kallon Hisham da yake cin abinci hankalinsa a kwance.

"Ai laifinsa ne momy ba shine ya daina kula niba".

Bugu momy takaiwa bakin azzah, da sauri ta matsa baya.

"idan kaga dama hisham karka bata wayar ma sai bayan biki".

Baiyi magana ba har momy ta fita daga palon, abincin dayake ci ya deba a yakai bakinta,kawar da fuskarta tayi gefe tana ci gaba da fushinta.

"garama kici saboda ba baki wayar nan zanyi ba".

Jakarta da mayafi ta ajiye a kasa ta hau kujera mai zaman mutum uku ta kwanta, jakar ya janyo ya budeta yana fito da kayan ciki.

Kayan kwalliya ne da turare a karamar kwalba sai wata karamar leda da itace ma tafi cika jakar, bude ledar yayi yaga abubuwa kamar maganin gargajiya haka ya tsaya kallonsu, kallonta yayi ta juya masa baya.

"Azzah  meye wannan acikin jakarki?"

Gaba daya ta manta da ajiyarta aciki, kallon hannunsa tayi taga abinda zareena ta batane ya binciko, tsalle daya tayi sai gata agabansa tana zazzare ido.

"wayace ka bude min jaka, innalillahi bani kayan Mutane nan".

Yadda duk ta rikice ya bashi dariya amma ya danne, "kayan mutane dai ko kayanki? ki yi ahankali dai karki zautar dani ranar ashirin da bakwai ga wata".

Bata taba sanin tanada kunya ba sai yanzu, ta kasa magana kawai ta Shiga tattara kayan tana mayarwa a Jakarta.

"wannan turaren yanada kamshi mai dadi zan ajiye miki shi har ranar ashirin da bakwai ga wata".

Bata kula shi ba ta mike da jakar ahannunta da magungunanta data karba a hannun zareena.

Binta yayi da kallo aransa yace, da wani tsukakken jikinta awurin, Zan Gani idan ke jarumar ce dagaske.

Dakin nuwaila ta shiga daya zama nasu ayanzu ta sameta tana danna waya, zama kusa da ita tayi tana ajiyar zuciya.

Da kallo nuwaila ta bita sannan tace, "yaya dai Azzah?"

"nida wannan mutumin ne ya bude min jaka yagane min sirri Wallahi kayan mata fa yagani aciki".

Dariya nuwaila tayi tace "yayi kyau karamar mara kunya, auren saura wata d'aya ne kika fara shaye-shaye".

Turo baki tayi ta kama hanyar fita sbd yunwa takeji.

Gaddafi ta gani yana cin abinci suna hira da hisham.

Ai ajuns la finalul capitolelor publicate.

⏰ Ultima actualizare: Mar 10, 2019 ⏰

Adaugă această povestire la Biblioteca ta pentru a primi notificări despre capitolele noi!

BAYA DA K'URAUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum