BABI NA GOMA SHA HUD'U

73 4 0
                                    


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

14

"Hisham wai me kake nufi da ni ne?"

Azzah ta tambaye shi cike da jin haushin sa.

Ko kallonta bai yi ba balle tasa ran zai amsa mata, Aisha ce ta yi magana.

"Calm down mana Azzah, tunda kika ga munzo tare ki kwantar da hankalinki".

"Kamar ya in kwantar da hankalina? mutum ya raba ni da iyayena, ya gaya min inda zai kai ni, na fara tsanar sa bana son ganin fuskarsa, kuma wallahi sai Allah ya saka min".

Runtse ido Hisham ya yi dan yaji zafin kalamanta amma dai baya son yin magana a yanzu.

Kuka Azzah take yi har suka iso k'ofar wani gida mai d'an girma, da motoci ak'alla zasu kai biyar bayan wad'anda suka zo dasu daga Kaduna.

Fitowa suka yi zasu shiga gidan Azzah ta kafe bazata shiga ba.

"Ku shiga ku fito, babu inda zani, banida kowa a garinnan dan haka a yau d'innan bazan kwana ba Kaduna zan koma".

Hisham ya matso kusa da ita yace, "idan baki zo mun shiga ba Allah a kafad'a zan dora ki na shiga dake, kinsan ban miki kala da d'an yankan kai ba".

Saida ta harare shi sannan ta yi magana.
"Banga alama ba".

Gaba ya yi ta bi bayansa ita da Aisha.

Suna shiga ta hango mama Dije da Momy a zaune kan kujera saida gabanta ya yi mummunar faduwa har saida mararta ta murd'a, da gudu ta fad'a kansu tana kuka.

"Momy, Mama Dije kuma sato ku suka yi ko? Ku yi hak'uri laifina ne dana yi soyayya da Hisham ashe mugune ban sani ba, Mama Dije ina yayata Nuwaila?".

Shiru suka mata sai ji ta yi su Hisham na gaisawa da mutanen dake palon, cike da mamaki ta juyo tana kallon su d'aya bayan d'aya.

Duk inda hankalin Dady yake saida ya bi ya tashi.

"Gaddafi Sokoto zamu duk inda wani abu yake na wuta a gidannan ka kashe shi, ayi sadaka da kayan abincin da zasu lalace, kayi sauri".

Gigicewar da Gaddafi ya yi yasa bai damu da Jin dalilin zuwa Sokoto ba, cikin sauri ya yi yadda Dady yace.

Bayan ya gama Dady ya jashi d'akinsa suka shiga fito da duk wasu takardu da suka shafi dukiya da kadararsa, sai a lokacin hankalin Gaddafi ya kawo wuta.

"Dady meya shafi neman su Momy kuma da document d'innan da zaka kwasa?".

"Idan mun isa can zaka ji komai yanzu banida nutsuwar yi maka bayani, Muradi na kada su rabani da matata".

Shiru Gaddafi ya yi har suka kama hanya basu bar koda Sama'ila bane dashi suka tafi, koda suka iso Sokoto karfe biyar ta yi.

Dady ya yiwa Gaddafi nuni da hanyoyin har suka iso gidan, tun daga ganin motocin awurin ya tabbatar da suna gidan.

Kafin isowar su Dady. Awurin Momy ta yiwa Azzah bayanin komai, duk rawar kai irin na Azzah sai da ta girgiza dajin lamarin, shiru ta yi tana kallon Hisham.

Gidan suka shigo ganin k'ofar palon a bud'e yasa suka danna kai ciki, numfashin da Dady ya sauke ya dawo da hankalin mutanen palon garesu, Dady kuwa Momy daya hango a zaune yasa shi sauke numfashi.

"Bana buk'atar sake ganin fuskarka a gidana, ka gaggauta sake min y'a ta ka k'ara gaba kuma ka kwashi yaranka ko d'aya kada ka barmin".

Sosai jikin Dady ya yi sanyi, a hankali ya k'araso kusa da tsohon dake zaune kan kujera ya durk'usa gabansa.

"Baba kayi hak'uri ka bani damar kare kaina dan Allah, na yadda da kowane irin hukunci amma rabani da Zainab tamkar zare ruhina ne daga gangar jikina".

"Kalamanka tamkar gwarancin yara haka na d'auke su dan haka bana buk'atar naji dalilinka macuci kawai".

"A'a Malam kayi hak'uri abi komai a sannu kuma wannan zancen bai kamata ba agaban yara".

Shiru d'akin ya yi babu mai magana sai wannan matar da nake sa ran itace matar tsohon dake zaune.

"Kaga maikano tashi ka tafi idan hankali ya kwanta zuciyata ta rage zafi sai kazo a yi magana ta fahimta".

Mik'ewa ya yi yana kallon Momy ta yi saurin kawar da kanta.

Sun dad'e basu yi bacci mai dad'i irin wannan ba, Dady kuwa bacci k'aura yaiwa idonsa, washe gari da sassafe suka juya kd shida Gaddafi saboda wasu dalilai.

Kuyi hak'uri Ina dad'a jefaku a cikin duhu.
Akwai wata sark'ak'iyane idan kun cigaba dabi zamu warwareta insha Allah.

Ku k'ara hak'uri dani akan gajerun shafuka hakan yana faruwa ne saboda rashin samun isashshen lokaci.

Kada ku manta Ina buk'atar comments d'inku mussaman my wattpad people.

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now