BABI NA GOMA SHA BAKWAI

117 6 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

17

Duka takardun ya had'a ya bawa Hisham.

"wannan photocopy ne, original suna company idan kana so za'a ci gaba da aikin tare da shi abokin nawa idan kuma baka so komai a rubuce yake sai a raba".
Daddy ya fad'a yana turawa Hisham
Jakar daya zubo takardun.

Yaci gaba da magana.."daga k'arshe ina k'ara neman gafara a wurinku ku, ko iya haka ma naga karatun duniya, na d'auki darasi, tunda na taso banji dad'in rayuwa kamar kowa ba haka kuma zan k'are a wahale, ciwo na ba lallai bane ya warke".

Hawayen da suka cika idonsa yayi saurin tarewa kafin ya cigaba da magana,"bayan Gaddafi, Azzah da Nuwaila babu wanda zan tilastawa zama tare dani, suma d'in saboda banida kowa ne sai su".

Mahaifinsu Mommy ne yayi magana." har matarka zaku tafi Abubakar, bazan rik'e ka azuciya na kasa yafe maka ba, kun zama dattijawa ayanzu mutuwar aure a tsakaninmu zubar da kima da mutuncinku ne, rufawa juna asiri da fatan agama lafiya shiyafi dacewa daku, ka godewa Allah daya karkato da kai hanya mai kyau kafin ka kauce masa, Hadiza ce kad'ai zata ci gaba da zama anan wannan umurni ne ba shawara ba".

Babu wanda ya rik'e Daddy aransa kowa ya furta kalmar yafiya amma banda mama Dije hasali ma ta nuna fushinta sosai saboda tunawa da mijinta margayi Aliyu  da kuma rabata da d'anta shekaru masu yawa.

"koda Abba bai fad'a ba bazan biku ba haka kuma bana tunanin kalmar yafiya zata fito daga bakina zuwa gareka, ban kuma amince Hisham ya auri y'arka ba daga yanzu bayan alak'a ta jini na yanke duk wata alak'a dake tsakaninsu".

Azzah ta zuba mata ido cike da mamaki, kuma zancen ya matukar girgizata, shiru tayi tana kallon maman kafin ta maida kallonta wurin Hisham d'in shima mama Dije yake kallo.

Fita mama Dije tayi daga palon tana hawaye, mommy zata bi bayanta mahaifinsu ya dakatar da ita,"ki barta Zainab fushin zuciya ne zata sauko, kawai tana bukatar lokaci ne".

Jamal kam kafarsa kafar Nuwaila duk da bata wani kulashi amma ya nace mata.

Washe gari da sassafe suka kama hanyar kano, sati ya zagayo suka koma makaranta, mommy duk jin gidan take wani iri haka nan dai take daurewa.

Tana kitchen tana girki yaran duk suna makaranta Daddy ya shigo, kallonta ya yi yana murmushi yace, "Nagode Zainab, na zata bazaki dawo gidana ba, na zata daga shekaranjiya farin cikina ya k'are".

Bata kalle shi ba ta fara magana, "idan  kayi duba da abinda alhaji yace mun girma rabuwar aure a tsakaninmu zubar da mutunci ne, ko dan albarkacin su Gaddafi bazanso rayuwar uban y'ay'ana ta wulak'anta ba".

"shiyasa  nake k'ara yi miki godiya, baki tambayeni yadda akayi na gano lafiyar ki lau ba" ya fad'a yana kallonta.

"na zargi Haka bada dad'ewa ba sai dai banga canji atare da kai ba shiyasa ban damu ba".

"haka ne Kuma, keba y'ar fari ba sai wauta, ta ya zaki tunanin bazan gane ba bayan ni mijinki ne".

Murmushi kawai ta yi bata kuma magana ba.

Duk sati Jamal yana zuwa wurin Nuwaila da haka suka samu damar fahimtar juna, ta lura yanada sauk'in Kai da barkwanci.

Kamar wasa zancen aure ya shiga tsakaninsu har ankawo kudin sa rana.

Azzah kuwa shiru babu labarin Hisham dan tunda suka baro sokoto bai k'ara kiranta ba da farko ta damu sosai amma rashin nutsuwarta baya bari agane sbd kullum cikin shirme take.

Ranar auren zareena aka sa tun daga lokacin basuda zama duk inda zasuje da Azzah ake zuwa.

Suna kwance a d'aki nuwaila ta tambayi Azzah ko Hisham yana nemanta.

"bai neme ni ba tunda muka dawo, wata kila ko mama ce tayi masa katanga tsakaninmu".

"Kar ki cire rai dashi Azzah mama dole bazata ji dad'i ba ki kwatanta halin da zaki shiga idan kece abin ya faru dake".

Hawayen idonta ta goge, "na cire rai dashi, Da yana sona da zai neme ni koda sau d'aya ne zai iya zuwa wurina tare da Jamal Amma kinga wata na uku kenan gashi ke har magana ta yi nisa tsakaninki da..." wayarta ta fara ringing sai da ta yi tsaki sannan ta d'auka, banda  um da um-um babu abinda take cewa har suka gama wayar.

"k'anin mijin zareena ne shegen surutu kamar wanda yaci Aku".

Dariya Nuwaila tayi tace," shine daidai ke, amma dai muyita addu'a insha Allah komai zai zama daidai".

Bayan magrib dukansu suna palo Gaddafi yayi gyaran murya Daddy ya kalleshi yace "kanada magana ne? ".

Sosa k'eya yayi sannan yace "Daddy iyayen wannan yarinyar ne sukace na turo za'a  had'a bikin dana yayanta".

Azzah ta tashi daga zaunen da take tace "au dama yaya kana soyayya?"

Hararar ta yayi  ta Kalli Nuwaila tana dariya shidai baice komai ba.

Daddy yace, "insha Allah za'a je, Azzah ce tace akwai bikin zarina idan Sun kammala jarabawa shi nake jira a gama sai muje sokoto gaba d'aya".

"mommy tace Allah ya sanya alkhairi bari ni na kwanta".

Ameen suka amsa babu jimawa Daddy ya bi bayanta, bai ganta a d'akin ba sai motsinta yaji a toilet, shiga yayi yana cewa "amma dai kinsan wannan aiki na ne kike yi ko? "

Batayi magana ba sai da ta daura towel tace,"na hutar dakai".

"Allah dai yasa nazo da wuri kinga sai na k'arasa".

Dariya kawai tayi suka koma d'akin a tare.

A palo Azzah  da Nuwaila ne kad'ai suka rage, Azzah ta kalli Nuwaila tace " Daddy da Mommy Sun iya soyayya fa, Ashe Mommy tana kwalliya dazu tashafa jan baki kuma kayanta skirt ne Daddy yayita kallonta tana burgeshi".

"Allah ya shiryeki da wannan shegen bakin naki kamar cakwaikwaiwa".

Tashi tayi ta koma daki dan lokacin dare ya soma yi.

Su Azzah babu zama saboda biki har saida aka kai amarya d'akinta, saifullahi kuwa k'anin ango ya nacewa Azzah ta d'an fara sakewa dashi amma ba sosai ba.

Bayan kwana biyu da bikin suka wuce sokoto, gidan da Daddy ya yi k'ok'ari ya siya saboda irin ziyara haka acan suka sauka ko kadan baiyi girman gidansu na kano ba kuma bakomai aciki sai katifu kawai.

Tunda suka sauka Azzah ke tsaki dan ta tsani ciro kaya daga akwati sannan saida sukayi shara da mopping sbd k'ura, aranar aka sa labulaye da kujeru a palon wanka sukayi sannan suka fita zuwa gidansu mommy.

Acan suka samu Hisham yazo daga gaisuwa ko kallonsa Azzah bata kuma yi ba,  mamaki yasa shi sakin baki yana binta da kallo.

Follow me on watt pad @safiyyahgaladanchi16

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now