BABI NA GOMA SHA BIYU

61 2 0
                                    


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

12

B'ata rai momy ta yi tana kallon Gaddafi, a hankali ya girgiza mata kai amma bata daina masa kallon tuhuma ba.

Idonsa ya mayar kan Nuwaila yana mata alama da, ki yi mata bayani.

Nuwaila ta kalli gefen momy tace, "mafita zaki bamu momy, bamu san halin da Azzah take ciki ba, dare ya soma yi".

Zaune ta tashi tana kallon su hawaye ya cika idonta.
"Nuwaila mai zance? Azzah zata iya b'ata a garinnan kuma za'a iya sace ta, akwai kidnappers amma bana tunanin Azzah zata je unguwar da bata sani ba har ta b'ata bata kira kowa ba domin neman mafita, kuje kuyi reporting police station da sassafe ku bada hotonta gidajen radio da television a yad'a cigiya, Ina jin tsoro".

"Allah ka tak'aitawa wannan baiwa taka wahala, Allah ka sa bata shiga mugun hannu ba", addu'ar da mama dije ke yi kenan.

Ameen suka amsa duka.

Nuwaila hijab d'inta ta saka suka fita ita da Gaddafi.

Suna tafiya a mota kowa ya kasa magana sai can Nuwaila ta katse shirun da cewa,"duk laifi na ne, da ban d'auke mata wuta ba da zansan kaso hamsin cikin d'ari na daga rayuwar da take yi yanzu, saboda wasu kalamai na banza da baza su lak'e min ajiki ba na daina kula k'anwata, idan wani abu mummuna ya faru da Azzah bazan daina ganin laifin kaina ba".

"Kiyi hak'uri insha Allah babu abinda zai sameta".

A hanyarsu ta dawowa Gaddafi yace, "ba zamu samu wani gidan radio da suke aiki har k'arfe goma na dare ba".

"Allah ya kaimu gobe sai mu fito da wuri". inji Nuwaila.

Har zasu shiga gida Gaddafi ya tambayi Nuwaila, "ko kinada lambar saurayin Azzah wannan Hisham d'in?".

Sai da ta yi murmushi kafin ta soma magana, "haba Gaddafi, Hisham da ba a garin nan yake ba, mai zai had'a shi da b'atar Azzah?".

"Ba haka nake nufi ba, I just want to hear from him if zamu samu wani information akanta".

"Well.. banda lambarsa gaskiya, amma if i check through my call log zan iya ganin numbern wannan brother d'in nashi ya kirani day before yesterday".

Palo suka k'arasa ta shiga suka tarar da Momy da Mama Dije jugum kowa da tunanin da yake a zuciyarsa.

Momy ta katse shirun da cewa, "banida matsala kamar Babanku ya dawo ba'a sameta ba, bana tunanin rayukanmu duka zasu yi dad'i".

Shiru suka yi kowanne ya kasa magana.

A b'angaren Azzah kuwa lokacin da ta fita bata yi nisa ba ta tsaya siyan lemu a wani shago sai kawai taga mutum a motarta ya shigo, ta tsorata sosai ganinsa da sharb'eb'iyar wuk'a.

Umurni yai mata da ta koma baya ba tareda ta fita daga motar ba sai dai ta tsallaka daga cikin motar, tsoro ya hanata musa masa tana ji tana gani yaja motar suka bar unguwar, a lokacin ta kallon kiran da zarina ke mata amma ta kasa d'agawa, batasan iya adadin tafiyar da suka yi ba sai ganin ta yi sun shigo Kaduna, sai a lokacin wani irin kuka ya zo mata, labarin kidnapping da take ji yau shine yazo kanta.

Ta shiga uku bata yi sallama da kowa ba, bata roki kowa gafara ba gashi zata mutu, Allah sarki Hisham d'inta shikenan bazasu kuma ganin juna ba sai a lahira, auren da taci buri akai zata yi gashi wa'adinta ya kusa cika ba tare da ta yi auren ba.

Tunowa ta yi da Hisham fa a nan garin yake dan haka ta ringa kallon waje ta window ko Allah zaisa ya ganta amma sai ji tayi an bud'e gate d'in wani gida motar ta shiga.

Janta wannan mutumin yake tana turjewa har suka shiga gidan wani d'aki ya wullata ya rufe, to a mota mayafinta ya cire, garin dukan k'ofar d'akin d'ankwalinta ya zame ihu take da iya k'arfinta amma bata ji alamar akwai wata halitta akusa ba.

Fad'uwa ta yi zaune ta jingina da k'ofar d'akin tana kuka.

"Me na yi maka dan Allah, bansan ka ba, idan kud'i kake so ka bani wayata na kira Dady na ko nawa kake so zai baka amma karka cutar dani ban maka laifin komai ba".

Abinda take ta maimaitawa kenan har bacci ya d'auketa a wurin.

Kusan magrib ta farka ta shiga toilet alwala ta yi ta fito babu hijab d'ankwalinta kuma baida girman da zai rufe mata jiki, gefen gadon ta zauna tana tunanin wannan rayuwa.

Turo k'ofar akayi da sauri ta d'aga kai tana kallon wanda zai shigo.

Kusan shabiyun dare suna zaune ba wanda yake tunanin kwanciya.

Dak'yar Nuwaila ta gano numbern Jamal ta bawa Gaddafi amma dare ya yi yanzu ba lallai ma ya d'aga ba sai yace zasu bari har da safe.

A ranar bacci b'arawo ne kawai ya sace su shima ba cikin dad'in rai ba.

Ko wanka Gaddafi da Nuwaila basu yi ba k'arfe bakwai suka fita a hanya ne Gaddafi ya samu damar kiran Jamal.

Gaisawa suka yi ya fad'a masa dalilin kiran ko Hisham yanada wani labari akan Azzah saboda yau bata kwana gida ba kuma wayarta ko an kira bata d'agawa.

"Ni d'an uwana ba mazinaci bane, da zuciya d'aya yake son k'anwarka, zan dai fad'a masa kuma na basa numbernka koda wani taimako da zai iya yi muku wajen nemanta". Abinda Jamal ya fad'awa Gaddafi kenan.

Shiru Gaddafi ya yi saboda sosai maganar ta sosa zuciyarsa, su suke nema dan haka komai aka musu dole su yi hak'uri.

"Ba abinda nake nufi kenan ba Jamal taimakon nake nema kuma daga information d'inda zamu samu daga wajensa zai iya zama silar ganinta, bana shaidar Azzah amma inaji a jikina ba yawon banza ta tafi ba, da motar ta ta fita, ka yi hak'uri kada ka d'au zafin zuciya ka kwantata hakan ace k'anwarka ce haka ta faru akanta ka yi tunanin yadda zaka ji a zuciyarka".

Jikinsa ya yi sanyi sosai kuma ya tausaya musu dan haka yace su bari ya yi magana da Hisham d'in.

Wata kyakkyawar yarinya ce zata Kai shekaru ashirin da uku kaya ne d'auke a hannunta, kallon Azzah ta yi sosai amma kafin ta yi magana Azzah ta riga ta.

"Innalillahi! kema satoki suka yi? Mun shiga uku ya zamuyi mu gudu daga gidannan".

Kallonta kawai yarinyar ke yi baki a sake tana mamaki.

Azzah zata kuma magana idonta ya sauka kan Hisham dake bayan wannan yarinyar data kawo mata kaya.

Da gudu ta ruga sai bayansa ta b'oye.

"Alhamdulillahi baby boo nasan baza ka tab'a bari acutar dani ba".

Hannunta wannan yarinyar ta janyo ta dawo da ita cikin d'akin had'i da bata kayan dake hannunta suka fita tare da Hisham d'in daya sha mur kamar tsohon dan ta'adda.

Zama Azzah ta yi gefen gado tana kuka iya k'arfinta, acikin kukan take fad'in, "na shiga uku shine ya sace ni, Hisham Kaci amanata, idan na fita daga gidannan wallahi sai na nuna maka nice AZZAH SUNUSI MAI KANO..".

Surutan ta ci gaba dayi yana jiyota a palo ya dafe kansa bashida wani zab'i daya wuce haka, kukanta yana tab'a zuciyarsa.

Follow me on wattpad at safiyyahgaladanchi.

Comments d'inku sune zasu fi k'aramin k'arfin gwiwar typing, shirunku shi yake sa jikina yayi sanyi kamar labarin baya muku dad'i shiyasa nake kasa typing wani lokacin.

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now