BABI NA SHIDA

80 3 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BAYA DA K'URA...

Daga alk'alamin Sophie galadanchi.

6
D'aga wayar Azzah ta yi amma ba ta yi magana ba, "munafuka to ni ce ki ke wani jan aji".

Dariya Azzah ta yi ta ce, "Anya zarina kina da gaskiya kuwa?, Kullum cikin chanza number to bari ki ji sai na fad'awa mama a bincike ki da kyau".

"Ka ji mazuga to layinta ne, ki shirya gobe k'arfe takwas akwai lecture da Dr ya yi fixing kuma kin san zai iya yin test".

D'an tsaki ta yi sannan tace, "goben ki zo ki d'auke ni dan ni na daina hawa kucakar motar can".

Nuwaila data fito d'aukar pad taji abin da Azzah ke fad'a ta yi murmushi, ita ba ta san wace irin rayuwace Azzah ta d'orawa kan ta ba.

Dariya sosai zarina ta yi, "kar ki wani damu zan zo".

Daga haka suka yi sallama.

Kwanan zaune Dady ya yi yana tunanin wata gagarumar matsala da ke shirin tunkaro kamfaninsa.

Ya fi shekaru goma sha biyar yana wannan aikin basu tab'a samun matsala mai kama da wannan ba.

Idan zai iya tunawa sun gina makarantu na gwamnati fiye da guda arba'in haka kuma private schools ma bai San adadinsu ba, haka da hotel sun karb'i kwangilar ak'alla sun kai guda goma sha shida balle aje maganar estate a abuja sune k'wararri ta b'angaren zana gidaje na estate da kuma k'era su.

Dak'yar ya ga wayewar gari dan haka momy na bacci ma ya fita office dinsu yayiwa tsinke ya had'a meeting d'in gaggawa.

Hisham kuwa aiki ya kacame masa wannan karon Allah ya sa musu hannu kamfanin su na yiwa motoci k'ayataccen fenti shi ke haskawa ga motocin ma ana zuwa siya ba laifi dan haka ba shida zama da zai samu damar kiran gwanar tasa, ta wani gefen kuma ga y'ar uwarsa kafsha da ta dame shi da zancen soyayya bayan shi kuma ba shida ra'ayin ta zama matarsa gaba d'aya ba ta burgeshi idan kuwa ta gan shi fi'ili kala-kala ta ke k'irk'ira.

Har sun kusa fara exam suna zaune karatu su ke babu kama hannun yaro kira ya shigo wayarta sai da ta yi tsaki sannan ta d'auka.

"Da farko zan fara bawa gimbiya ta hak'uri akan jina shiru da ta yi, wallahi aiki ne ya matuk'ar siye min lokaci", abin da Hisham ya fad'a kenan bayan Azzah ta d'aga wayar.

Tsuke fuska ta yi sannan ta ce, " Dan Allah zan iya sanin dawa nake magana".

"Hisham",ya ce yana murmushi.

Ba wai dan ba ta gane ba ta kuma cewa, "Hisham daga ina?, Ka sake duba lambar daka kira kila ka yi kuskure".

"4matic silver dake hannunki na hagu ki zo ina jiranki amma wannan karon kar ki ce baza ki shiga mota ba dan Allah", kashe wayar ya yi yana kallon yadda ta had'a fuska.

Yi ta yi kamar ba zata je ba sai kuma ta mik'e zarina ta bi bayanta da kallo a hankali ta ke tafiya harta k'arasa kusa da motar staye ta yi tana kallon gefe sai da ya sauke glass ta gefenta ya yi magana sannan ta shiga ta zauna.

Murmushi ya yi sannan yace, "Surprise na ke son baki shiyasa ban fad'a miki zan shigo ba".

"Ina yini, ya hanya?".

"Lafiya lau Azzah my sweetheart".

"Uhm muna karatu ne wani satin za mu fara jarabawa tunda mun gaisa zan koma mu ci gaba da karatu".

Hannu ya sa bayan motar ya d'auko leda ya mik'a mata har zata karb'a ta tuna maganar mama Dije.

"Ku kama mutuncin ku kada ku yadda wani abu na daga hannun saurayi ya rufe muku ido har ya gano ko kuma ya yi tunanin saboda abin hannunsa ku ke tare da shi, idan da hali ma duk yadda ya kai ga son ku karb'i kyautar da ya yi muku to kada ku karb'a sai idan maganar aure ta shiga tsakanin ku, ku yi hak'uri na d'auke ku tamkar y'ay'an dana haifa shiyasa nake muku nasiha banaso tarbiyarku ya samu tangard'a saboda Allah da kuma mahaifiyarku da ke kwance babu lafiya".

Hawaye ya gani a idonta ji ya yi kamar ya rungume ta amma bashida damar yin haka hasali ma baisan abinda yake damunta ba da ya sa hawaye zuba daga idonta.

Bata karb'i ledar ba bata kuma yi masa sallama ba ta fita daga motar tana kuka.

Yana kallo ta koma wurin sauran kawayenta da suke karatu tare.

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now