BABI NA GOMA

83 2 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

10
Yadda ta kafe idonta akansa yasa shi fahimtar cewa tana buk'atar k'arin bayani, gyara zamansa ya yi shima yana kallonta.

"K'addara ce take ta afkawa kaina Zainab, daga wannan sai wancen, matsalar yau daban ta gobe daban".

Shiru ya yi ya had'e kai da gwiwa a hankali ya ci gaba da magana.

"Kamfaninmu ya fara samun rauni, na yi bincike sosai akan ma'aikatanmu bansame su da wani laifi na cewa matsalar daga wurinsu take ba, kafin ma na yi haka saida na tattaro su duka muka zauna, amma babu wani bayani dake nuna cewa mun gaza ne ta wani b'angaren, mun tashi ne kan cewa ko an samu wani kamfanin da ya fi namu ne ko kuma yake mana zagon k'asa".

Fuskarta ta yi alamar tausayi har ruwan hawaye ya kwanta cikin idonta.

Huci ya fitar mai zafi sannan ya kwanta gefenta.

"Yarinyar nan Azzah tana so ta zama wata kalar daban, Sam bata da nutsuwa".

Ya gaji da surutu baya samun amsa sai kawai ya rufe idonsa ya yi bacci.

Washe gari da sassafe motar Azzah ta iso, bai fad'a mata ba dan baya son hayaniya, fita yai ya dubo ta da kyau bazama ka gane ba sabuwa bace, abubuwa sun masa yawa bazai iya siya mata sabuwa dal ba, kuma ya tabbatar tunda ta kafe sai irin motar Azzah komai tsadar motocin gidan baza ta so su ba.

Tana zaune a palo tana shan tea ya mik'a mata key d'in motar, ihu ta yi ta rungume shi har da su masa blowing kisses a kumatu.

Murmushi kawai ya yi yana shafa kanta.

Waje ta fita dan ganin motar, ba k'aramin dad'i ta ji ba, motar bak'a ce sab'anin ta Nuwaila ja sai k'yalli take, daga waje data dawo d'akin momy ta shige ta same ta a kwance kamar yadda ta saba ganinta.

"Momy Daddy ya siya min irin motar Nuwaila amma tawa bak'a ce, wata rana zamu fita yawo dake a motar, kinji momy?".

Murmushi momy ta yi tana lumshe idonta, Azzah bata damu ba tunda tasan ba magana zata yi mata ba, fita ta yi daga d'akin ta koma d'akinta, teddies d'in ta duka ta kwasa ta zuba gaba da bayan motar, Air freshener ta sa a motar ta kunna AC ta bar ta a slow.

"Dole ma Zarina ta ga motar nan yau", ta fada tana murmushi.

Sama'ila ta kira ya rugo yana mata kirari.

"Inga yatsunka in kana tara farce baza ka tab'a min mota ba, Kar ka kankare min fenti".

"Ranki shi dad'e auta ai bana ma tara farce da baki ma nake cirewa".

"Mtsww k'azami ne kai Sama'ila, ni zo ka goge min motar daga waje kawai fita zanyi".

Shi gaba d'aya Azzah mamaki take bashi, juyawa kawai ya yi ya dauko bucket.

Kitchen ta samu Mama Dije tana aiki, rungume ta tayi ta baya tana fad'a mata sabuwar motar da Dady ya siya mata, da kuma fitar da take son yi yanzu.

"To Azzah Allah ya sanya Alkhairi, ki yi ahankali kinji? Kuma kar ki Kai dare".

"K'arfe shida insha Allah zan dawo".

"Ki gaishe su".

D'akin Nuwaila ta lek'a ta ga bacci take tun d'azu sai kawai ta fita.

Slow take tafiya da motar ta jona wayar da Aux cable, wak'ar Ali Jita mai taken Indo ta kunna.

Direct gidansu Zarina ta wuce, sosai Zarina ta taya ta murna.

"Amma babe ki rage sanyin AC yasin har na soma jin fitsari".

Dariya Azzah take da hawaye, "bar ni ke dai na fi son abina a haka".

Har maman Zarina ta fito taga motar, addu'a ta yi mata had'i da jan kunne kan su ringa tuk'i cikin nutsuwa.

Pictures d'in motar kuwa sun cika wayar Hisham, babu inda bata dauka hoto ta tura masa ba, yana kwance a d'aki sai dariya yake dan ta fad'a masa next time idan ya zo ajiye motarsa zai yi ita zata Kai shi duk inda zashi da sabuwar motarta, shi dai ya amsa mata da to kawai.

Washe gari da safe Alhaji mukhtar wato mahaifi ga Jamal marik'i ga Hisham ya kira Hisham d'in domin jin inda maganarsu ta kwana.

BAYA DA K'URAWhere stories live. Discover now