BABI NA GOMA SHA SHIDA

126 7 2
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

BAYA DA K'URA...

DAGA ALK'ALAMIN SOPHIE GALADANCHI.

MAKARANTA WANNAN NOVEL KU SHAIDA WANNAN SHAFIN NA DOTAR MEELA ADEEL NE (AISHA). WWW.KYAUTARDOLE .COM

16

Keb'abb'en d'aki aka ware musu domin yin wannan maganar har yaran babu wanda aka ware.

Hisham, Jamal, Gaddafi, Nuwaila, Azzah da Aisha, sai su momy da iyayen su.

Kan Dady a k'asa ya soma bayani yana jin kunyar yaran shi da yake matuk'ar so.

"Azzah, Nuwaila da Gaddafi, ina rok'on Allah kada ya dada tsana ta acikin zuciyoyinku bayan jin wannan lamarin da ya faru".

"Ni da mahaifin Hisham mijin Hadiza (mama Dije) mun kasance a shekarun baya shak'ik'an abokai, Wanda a family na da nashi kowa ya sanmu atare, mahaifin Aliyu ya kasance babban d'an kasuwa, lokacin da tsufa ya kama shi a lokacin Aliyu ya yi aure sanadin haka ya kasa dukiyarsa kashi biyu ya raba musu kaso d'aya duka yayansa da wayanda yake rik'o, acikin wannan kyauta daya musu Aliyu mahaifi ga Hisham ya samu kud'i da kuma wani babban fili dake hanyar fita gari".

"Ni lawyer ne yayinda shi kuma ya kasance likita, sannan ni maraya ne koda na taso banida uwa banida uba a raye kasancewar gidanmu gidan taro ne yasa ban rasa masu kula dani ta fannin abinci da sutura ba sai dai nakan sha wahala b'angaren makaranta, babu wani takaimammen mutum d'aya da yake kula da harkar karatuna, duk Wanda na samu da hali shi nake rok'a akan ya taimaka min tun bayan dana gama primary, a wannan lokacin mahaifin Aliyu shine ya kasance mai kula da harkar karatuna harna kammala degree na nayi bautar k'asa na da duk abinda ya dace a lokacin da nake fafutukar neman aiki a lokacin ne Aliyu ya kammala nasa karatun kuma a take ya samu aiki kasancewar karatun mu yasha bamban, bikin kammala karatunsa aka had'a dana aurensa, awurin bikin naga mahaifiyarku naji Ina sonta sai dai ni a lokacin banida kud'in da zanyi aure ko gidan da zan saka matar banda, bayan aurensu ne mahaifin Aliyu ya raba musu dukiyar sa dan haka idona yana kan filin da aliyu ya samu, a wannan lokacin ne kuma Hadiza ta samu juna biyu Wanda hakan ya k'ara masa sonta sosai a zuciyarsa har takai ga ya d'auki kyautar wannan filin ya bata ita da d'a ko y'ar da zata haifa musu".

"Babu wanda ya zuga ni, babu Wanda ya bani shawara sharrin Zuciya ne".

"Ya bani labari akan kyautar da yayiwa matarsa sai zuciyata ta k'ara karkata akan wannan filin, da haka na ringa nuna masa cewa bai kamata a ajiye kadara haka ba sakaka saboda gidansa ana yawan shige da fice, Allah ne kawai ya karkato da zuciyarsa kaina yasa ya bani ajiyar takardun filin, ya tabbatar min da bai fad'awa kowa ba hakan ya k'ara bani k'warin gwiwar aiwatar da abinda zuciyata take kitsa min".

"Haihuwar Hisham ya k'ara tabbatar da son da Aliyu yakewa Hadiza ni kuma alokacin na samu aiki a kano ban fad'awa kowa ba saboda na gama yanke shawara ni da zuciyata cewa idan na gudu bazan dawo ba domin ana shirin aurena da k'anwar Hadiza, babu dad'ewa da auren na gama shirya komai sai kuma wani mummunan abu ya faru Allah ya yiwa Aliyu rasuwa, na girgiza kuma nayi bak'in cikin mutuwar abokinsa shak'ik'i, sai dai zuciya ba tada k'ashi domin ban sauya k'uduri na ba, a ganina babu Wanda ya san da zancen filin, a haka akayi aurena da Zainab bayan wata biyu da rasuwar Aliyu a gidan haya muka fara zama da matata, tun daga ranar da akayi auren idan Muna zaune sai zainab ta sani a gaba taba kukan tausayin Hadiza da jaririnta, idan Allah ya tashi kwancema bawa dubara babu yadda zaiyi shine dalilin daya sa nayi tunanin dauko Hadiza na tafi da ita".

"Na samu nasara wajen d'auko Hadiza sai dai aka samu mummunan akasi ashe aliyu ya sanarwa babban yayansu cewa filin Hadiza yana hannuna, ganin na kaurace musu yasa suka shiga nema na, ban fad'awa Zainab komai ba naje na siyar da filin cike da nasara na d'auke Hadiza da Zainab na tafi dasu batareda na lura cewa Hisham baya tare dasu ba, na tafka babban kuskure na raba d'a da uwa, kwana biyu da isarmu kano komai ya samu dan nayi nasarar samu gida acikin gidajen gomnati anan muka fara zama, bansan dalilin daya hana Zainab da Hadiza nuna min wani abu game da d'auko su da nayi ba, amma nafi tunanin cewa tsorata suka yi da yanayi na".

"Wallahi tallahi saida nasa k'afa na bar garin nan ban tab'a kwana hankali kwance ba nayi nadama sosai hakan yasa a kud'in filin banci koda k'wandala ba".

"A haka Zainab ta samu ciki har ta haifi Gaddafi babu wani taron suna daga mu sai y'an unguwa, ashe duk haukar da nake su Zainab basusan mai yake faruwa ba, Gaddafi bai wuce shekara uku Zainab ta samu wani cikin daya kwana arba'in kawai ya zuba zube, bayan wata uku da yin b'ari ta kuma samun wani cikin Wanda naga ya dace su san dalilin d'auko su da nayi, zuciyar Zainab bata da k'warin da zata d'auki irin labari na tashin hankalin dana zo mata dashi, ashe tanada high BP awurin ta zube min, nayi gaggawar kaita asibiti akace ta samu ciwon b'arin jiki babu abinda yake iya yiwa kanta, cikin jikinta a wannan halin ta rene shi sai dai Allah ya kawo sauk'i kafin haihuwa kasancewar nacewa da nayi akan nema mata lafiya Hadiza itace shaida ta, amma na d'auki Karan tsana na dorawa Hadiza koda Zainab ta haifi Nuwaila bata sake daukar ciki ba sai cikin Azzah a wannan lokacin ne kuma ta sake faduwa babu abinda take iya yiwa kanta nida Hadiza mune a tsaye wajen kula da ita, Hadiza ta zama tamkar y'ar aiki a gidan, yaran ita take kula dasu, a wannan halin aka haifi Azzah yarinya mai masifaffiyar gagara,  Zainab bata san nasan cewa lafiyarta lau ba kallonta kawai nake, akwai ranar da naji tana fad'awa Hadiza dalilin yin haka kan cewa zasu samu dalilin guduwa zata ci gaba da kwanciyar har su samu damar guduwa saboda Kar na kashe su da yayansu, naji zafi a ranar banyi bacci ba saboda ni na jawa kaina duk abinda ya same ni".

"Na fara da bud'e chamber, sannan nasa kud'in filin su Hadiza wurin yi musu kasuwanci wannan abin Allah ya d'aukaka shi na samu had'in gwiwa da wani construction company muka had'a hannu nake juya musu kud'in yayinda nikuma na kara samun budi saina koma b'angaren kasuwanci na bud'e manyan provision store, daganan na bud'e boutique inda nake fita waje d'auko kaya ganin na samu alkhairi sosai yasa nayi resigning daga aiki a lokacin su Gaddafi sun girma, inaso nayi aike gida amma iyayena basa raye kuma nakan lek'a Sokoto sai dai naji labarin a gidanmu babu Wanda ya damu da sanin ina nake tunda na zab'i na barsu babu ruwansu dani".

Numfasawa ya yi ya maida kallonsa ga Zainab kafin yaci gaba da magana, " Zainab nasan lafiyarki qlw tun kafin naji zancen da kuke keda Hadiza idan kinaso kiji ta wace hanya na sani ki bari sai mun samu keb'ancewa daga ni Sai ke zan fad'a miki".

"Hisham kuwa na gano yana hannun Alhaji Ahmad shiyasa hankalina ya kara kwantawa a lokacin ne kuma na daina takurawa Hadiza, idan zata tuna komai tare nake musu ita da Zainab kuma nace zan samo mai aiki amma ta hana, Hisham idan zaka tuna ranar da ka fito daga gidana kazo wajen Azzah ni kuma na dawo daga office a lokacin ne na had'u  dakai kuma na gane ko kai wanene, sai dai ban nunawa kowa nasan da zuwanka ba, nasan da had'in gwiwarka kai da mai gadin gidana Sama'ila, nasan cewa Kaine kake turawa ayimin sata a store nasan Kaine kake dak'ile mana ayyukan company dan haka nayi niyyar zuwa Dubai a kwana bakwai a yimin aikin da zasu yi min kasancewar ina fama da ciwon hanta, idan an gama aikin zan dawo na mik'a maka komai na rok'i gafararka, yawon Dubai da nake ina haduwa da wani likita ne d'an India nasha kwanciya a asibiti daga sunan naje saro kaya amma ban fad'awa iyalina inada wannan ciwon ba".

Kuka Hisham yake babu k'akk'autawa yana magana, " Dady babu abinda na rasa Abu d'aya ne yake k'ona min rai shine rabani da mahaifiyata, bansan dad'in uwa ba, lokacin da Abba ya fad'a min abinda ya faru na k'uduri niyyar kassara rayuwarka domin ina ganin dukiyata ce da mahaifiyata kake tak'ama da ita sannan kuma kamaida ita y'ar aiki a gidanka, a lokacin dana had'u da Azzah bansan y'ar ka bace sai a lokacin dana bita har gida na gano itace y'ar ka, sonta nake da gaske da aure kuma amma lokacin dana d'auke ta naso na b'oye ta ka d'andcana raba d'a da mahaifi kaji yadda naji nida mahaifiyata".

Kuka Azzah ta fashe da shi ganin yadda Hisham yake kuka yana fad'ar son aure yake mata duk da abinda mahaifinta ya masa.....

Nayi k'ok'ari...
Sai mun had'u a shafi na gaba.

Your comments pls.

Follow me on wattpad at safiyyahgaladanchi16.

BAYA DA K'URAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن