BABI NA HUDU

80 4 0
                                    

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

BAYA DA K'URA...

Daga alk'alamin Sophie galadanchi.

4
K'arfe takwas da rabi ta isa wani reshe na kamfanin sadarwa na MTN,da shigarta ta shak'i wani sanyi da kamshin turaren da a rayuwarta bata tab'a jin turare mai tafiya da hankali irinsa ba, kallon ma'aikatan wurin tayi kowanne da mazauninsa da komfuta a gabansa sai faman aiki suke.

Wani security ya tambayeta,"y'an mata mai kike so?".

"Layi zan siya in kuma yi register".

"Ok kije gun wancen da yake zaune shikadai", godiya tayi masa ta k'arasa wurin,kujera ya nuna mata ta zauna,bayan minti talatin tagama siyan layin har register wannan yasa tayi shirin fita.

"Wannan numbern ka duba location din?",wani saurayi dayake ji da aji ya fad'a yana bin Azzah da kallo kafin ya dawo da idonsa kan wani ma'aikaci dake wurin.

"Hisham number din bata cika aiki ba, yanzu zancen da ake kusan fiye da wata biyu layin yana k'asa kuma bazamu iya tracing location ba sai layin yana kan wayar kuma a kunne, karka damu zan cigaba da dubawa".

Shiru ya d'an yi na wani lokaci sannan yace,"to shikenan yau zan koma Kaduna amma zan ringa nemanka a waya",daga haka yai masa sallama yana sauri ya fita dan baya so yarinyar daya gani yanzu tai masa nisa.

Azzah kuwa tana fita da hanzari ta tafi gidan mai dake kusa da wurin dakyar ma motar ta shiga gidan mai kasancewar babu mai.

Hisham kuwa yana biye da ita a baya yanaso yaga gidansu amma bayan ta fita daga gidan mai sai yaga ta kama hanyar BUK binta yayi yaga tayi parking mota a department dinsu tunani ya d'an yi kad'an sai ya dauko wayarsa ya dauki motarta hoto.

Yayi haka ne saboda ya ajiye lambar motar.sauri yake dan haka yana fita daga BUK ya kama hanyar Kaduna.

Azzah kuwa ranar yawo tasha a cikin BUK sai kusan azahar ta hadu da Nuwaila ta fito daga lectures.

"Wai baki tafi gida ba?", Nuwaila ta tambayeta tana karasawa kusada motar.

"Yanzu zan wuce na gaji har zan wuce na hango kuna fitowa shine na k'araso nan in d'an huta".

"Ok ga wannan text books din ki wuce min dasu ki bawa Gaddafi idan yana gida". Nuwaila ta fad'a tana bud'e kofar baya ta zuba mata su,"kuma Dan Allah kimin mutunci ga mai sunan momy tana ciwon mara unguwar mu d'aya ki sauke ta gida".

"Kuyi aure kunk'i ai dole ciwon mara ya addabe ku",Azzah ta fad'a tana kallon agogon hannunta.

Tsaki kawai Nuwaila tayi ta kalle mara lafiya,"momy kyaleta ki shiga kinji Allah ya baki lafiya".

Ameen yarinyar ta amsa tashiga batayiwa Azzah magana ba har sai da suka kai layinsu ta nuna mata, abin mamaki Azzah taga yarinyar ta ciro key tana bud'e d'an madaidaicin gate d'in gidansu amma batayi magana ba ta kama hanyar gida.

Aikinyi ya samu layi tasa a wayar bayan tayi wanka da sallah ta ci abinci, Gaddafi ta bawa ya mata downloading WhatsApp da Instagram.

Ta kira Dady bata sameshi ba tace zata jira da dare ta k'ara gwadawa.

Hisham kuwa da tunaninta ya isa Kaduna ji yake kamar ya dawo amma dole zai je ya tsaya kan kwangilar da suka samu kodan  cigaban kamfaninsu.

BAYA DA K'URATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang